ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Har kusan La’asar sannan result d’in ya fito wanda ya tabbatar da tana d’auke da Vaginal cancer saukinta ma d’aya bata yi Spreading to other areas ba iyakar ta a Vagina d’in kuma bata da wani karfi a jikin sosai, gaba ta sakata tana tambayarta ko tana shiga toilet d’in dake da mutane masu yawan amfani dashi?!” Nan ma tace “a’a.”

Tambayarta ta kuma “Toh ko kina wanke Vagina d’inki da sabulu kamar give ko olive ko honey haka?

Cewa Sumayya tayi “Tana wank’ewa amma bada sabulun give ko olive ko honey ba a’a da irin wanda ake had’awa na mata…!”

Jingina kai tayi ta kuma tambayarta “ko kina cushe-cushen kayan mata a jikinta Sumayya?

Babu kunya tace “Eh amma ‘yan bauchi ne suna da kyau sosai.”

Ita kanta doctor Safiyya sae da ta jinjina amsar Sumayya sannan tayi mata fad’a sosae tare da ganar da ita illar duk abunda za’a baka ace kayi matsi dashi.

Magunguna sosae doctor in ta rubuta masu don cewa tayi inda tayi k’arfi da sae an mata Radiation therapy sannan tace ta dinga yawan shan kankana (water melon) don ita ce zata koro mata sauran cutar dake makale a cikinta sannan ta daina tsarki da ruwan sanyi kwata-kwata ta dinga shiga ruwan dumi da aka zuba gishiri a ciki…

Suna komawa gida takaici yasa Madre tace maza-maza Yaya Maryam ta tattara Sumayya ta mayar da ita gidanta tun da bata isa ta sumayya fad’a mata matsalarta ba bare ta ji maganarta, Duk yadda yaya Maryam ta so Madre tayi hakuri ta bar Sumayyan ta k’ara samun sauk’i amma ta k’iya karshe ma ita da kanta ta tattaro kayan Amir dake part d’inta ta kawo masu tace kafin dare har Maryam d’in ta tabbatar ta bar mata gida!Ganin abun bana wasa bane yasa suka fara shirin kowama muhallin su…

Wajen Magrib Yaya Maryam ta d’auki Sumayya dake ta faman turo baki tana kuka ta mayar da ita gidanta. Ta mata fad’a sosae ta k’ara jaddada mata illar abunda take sha tare da wanda take cusawa da mata misali da Amir dake da matsalar ido tare da Udutti da jikinta yake dabbare-dabbare wanda duk sanadiyar maganin matan da take amfani dashi ga kuma CS d’in da take sha sannan Uwa uba cutar da take d’auke da ita yanzu…!

Sosae jikinta yayi sanyi tana kuka tace wa yaya Maryam “Sister insha Allahu bazan sake ba!amma kuma to zan iya saka white miski saboda warin ya rage…?!”

Cikin natsuwa Yaya Maryam tace “No Sumy Duk abunda zaki yi inserting a steath d’inki Sumayya to akwae matsala ko menene hatta miski da hulba da lalle da muke d’auka mu saka don kwae muna ganin maganin natural ne to wallahi duk suna da side effect d’insu ke dae ki rike ruwan zafin da doctor ta ce maki da kankana da tab’s d’in da muka saya, Idan kina ganin ma zaki jaraba da na hausa to zan kawo maki ZAITUN ORIGINAL, GARIN SHAMAR DA KUMA GARIN FUREN LALLE sae ki kwab’a da ZUMA Ki dinga sha yana magani cancer sosae ko wace iri ce…”

Sumayya tace “toh.” Ita dai kawai idan za’a mata abun da zai sa mijinta yaji dad’i to zata sha ko menene. Da haka Yaya Maryam tabar gidan tana mamakin Sumayya kowa ya gaya mata haka ake mallake miji oho…

《》《》

KATSINA

Zamansu cikin jin dad’i da kwanciyar hankali suke yi a jauyan, tsaraba kam ba gidan da ba’a kai ba yayin da mutanen kauyen baki d’aya suke haba-haba dasu bare ma Udutti da ta ware tana shiga gidajen mutane kowa ya santa su Maitafasa kam kullum sae an kawo masu tafasa da curin fura!Kundum ma ba’a barta a baya ba da yake shiri take nema da Maitafasa ta ciwo bashin gero rabin tiya ta daka masu fura ranan da akace Ma’aruf zai zo d’aukar su zata kai masu.

Kafin ta kai masu ne Maitafasa ta lura da ita ta kuwa watsa hannu tace, “Kundum wa zaki kaiwa hurar nan ne?

A Hankali tace “Hafsatu K’arama zan bawa tayi tsaraba.”
Tsaki ta saki tana watsa hannu tace “Bana san munahurci Kundum…! aka ce maki bani da kud’in daka masu ne?

“Ta k’warank’watsa Maitafasa ba haka nake nuhi ba kiyi hakuri ki yahe min komae ya wuce.”

Kundum ta fad’a tana matse hawayen karya.

Sosae Maitafasa ta matsa tana leken fuskarta sannan ta kwashe da dariya tace “Kundum idan munahurci ya ganki har wata runguma yake maki aradun Allah!banda kina bakar munahuka meye na matse hawayen karya a huskarki?ko kiyi kuka ko kar kiyi kin sani Maitafasa na kamnarki Kundum matsalar bana son munahurcinki amma komae ya wuce, sai dai amma aradun Allah kika kuma shiga harkata sae na balli dawon battar ubaki…!

Shiru tayi ba tace komae ba a haka suka jera suka fita a bakin k’ofa suka ga mai unguwa Kundum ce ta tsaya ta gaidashi sab’anin maitafasa da ta hura hanci tayi gaba tana wakar habaici “Da Mai-uguwar kauyen mu k’ara bak’ar jaka a hayyeee…!”

Girgiza kai yayi yana kallon Kundum cike da gulma amma tak’i kallon shi tayi gaba tana kallon k’asa… Suna tafiya tana jan Maitafasa da labari amma tak’i kulata sae da tace “Ke ni ruhe min baki, ko kuma Allah tsine uban munahuki.” amma sam kundum tak’i zuciya sae dae lallab’a Maitafasa take har suka isa kauyen… a d’akin Inno suka yada zango suka mimmike kafafu ko wace ta ja baki gefe…

Lauratu ta shigo d’auke da Udutti tayo mata wanka sabida karta b’ata jikinta da k’asar gidan suka tsallakesu ta aje ta, Kusa dasu Udutti ta koma ta kurawa jajjayen hakoran Kundum ido tare da kwashewa da dariya tace “Bakya brush ko? yarinya ki dinga yi gashinan hakoranki sunyi daty.”

Maitafasa ta amshe da fad’in “Ina fa ta keyi yarinya!matar da bata aje komae ba sae munahurci itace za tayi brum (brush)? ta samu tayi assalatu ma kadae…”

Yarinyar ta girgiza kai ta fita da gudu K’arama ta maidota… ta duk’a har k’asa ta gaidar da Su, Kundum ta kad’a baki zata amsa amma Maitafasa ta make bakin da bayan hannunta tana fad’in.” Ruhen baki ke ta gaida da shegen shishshigi zaki amasa?, Lahiya lau Hafsatu K’arama ya d’ari d’ari da kauyan namu?

Dariya K’arama ta danne ta mik’e ta tabbata Maitafasa baza ta tab’a canza hali ba sae dae ta rage to meye laifin kundum don ta amsa gaisuwarta?

Yaran da suka fad’o d’akin suna fad’in “Ga mota ga mota.!” Shi yasa gaban K’arama mummunar fad’uwa yayin da Maitafasa ta mike ta fita kamar ita aka kira!Ma’aruf kam yana zuwa suka shige bukkar Ard’o suka gaisa sannan Ard’on ya kira mashi Hafsuwalle itama suka gaisa ya aje masu kud’i masu yawa yace sauri yake su K’arama su fito zasu wuce…

Sosai Umma tayi wa K’arama gargad’i akan k’inbin Umarnin mijinta haka ma Lauratu ji take kamar karta tafi sati d’ayan ji take kamar yanzu suka zo zasu koma harda hawaye tayi.

Har bakin mota mutanen gidan suka rakosu suka shiga sannan Ma’aruf d’in ya bawa sallau kud’i yace ya raba masu bayan ya bawa Maitafasa ya ja mota suka d’auki hanya komawa gida…

Har suka kusa fita kauyen K’arama bata kalleshi ba sae Udutti dake ta faman zuba kamar b’arkakken fanfo…

Murya k’asa k’asa yace “Ba magana ko lil Mommah?

A Hankali ta kalleshi sae taga ya mata kyau na musamman!ji take dama ya tsaya a haka tayi ta kallonshi ba tare da ta d’auke ido ba, da yake hanya yake kallo sae ta saki jiki tana kallon shi har da su murmushi kafin Udutti tace,

“Papa tana kallonka…” Udutti ta fad’a tana kallon K’arama. Da sauri ta mayar da kanta k’asa cike da kunya ta sa tafin hannunta tana rufe fuskarta.

Murmushi yayi yana jefawa K’arama harara sannan ya kalli Udutti yace “Ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button