ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai tsaye tace “Ta k’warank’watah…!
Da sauri suka kalleta ta kwashe da dariya tace “papa wannan Maitafasan take fad’in haka fa.”
Da yake yasan da sun bar gurin zata manta sae yace “Huh…” kawae ya cigaba da driving d’in shi…
Har suka hau titi sannan K’arama tace “Uncle ina Aunty Sumayya?
Hararanta yayi ta gefen ido sannan yace “Gata nan a bayan mu.”
Dafe kirji tayi had’i da waro ido ta juya baya da sauri don har ga Allah ta d’auka da gaske yake, ganin ba kowa ya sata sakin ajiyar zuciya tare da hararan shi…Kallonta yayi ya tab’e baki had’i da jujjuyar da kai…
Cikin shagwab’a tace “Bunkul ko?Toh Sorry Good Morning…”
Banza ya mata yana hararanta ta gefen ido wadda ta kasa fassara ta ko mai cece… Babu wanda ya kuma magana a ciki har suka yi tafiya mai nisa da yake a kauyen ba wani bacci suke samu ba don haka daga Udutti har K’arama suka ciga ba da bacci a cikin motar…
Madre ce ta kirashi suka gaskisa tare da tambayar shi hanya a lokacin sun kusa isowa gari sae ya fad’a mata sun kusa, cewa tayi mai ya wuce gidan shi domin Sumayya ta koma bai tambayi dalilin komawar Sumayyan ba don yasan Madre baza ta yi son zuciya ba koma menene toh da dalili.
Sae ana gab da Magrib sannan ya shigo cikin gari direct gidan shi ya nufa har lokacin Bacci suke sae da maigadi ya bud’e masu gate sannan K’arama ta farka gabanta yayi mummunar fad’uwa a wahale ta kalleshi tare da dafe kanta da hannu d’aya Sumayya kadae ke fad’o mata!Ya lura da canjinta don haka bai kalleta ba sae da ya gama parking sannan ya dube ta ya sake mata murmushi yace “Sleeping belle…”
Mayar mashi da murmushin tayi tare da bud’e kofar ta sab’i Udutti da kyar sabida tayi mata nauyi yanzu suka yi gaba. karar bud’e gate ya fito da Sumayya daga wanka d’aure da towel a jikinta duk kumfa tazo ta tsaya bakin kofa tana tsalle Su K’arama suka fara shigowa ta basu hanyan suka shige falon ta kwantar da Udutti tana fad’in “Aunty Sumayya mun dawo.”
Ma’aruf na shigowa ta daka tsalle tare da bashi hot hug kamar zata koma jikin shi shima hugging nata yayi yana fad’in “Oyoyo Mamin boy…”
Rashin dace ya saka K’arama d’agowa tana kallonsu wani abu ya soki zuciyarta kamar taci mad’aci, karo na farko kenan a rayuwarta da ta tab’ajin hakan, saurin zub’ewa tayi k’asan rug idanunta suka kawo ruwa a hankali tace “Na shiga uku me kenan?Kishi nake da Aunty Sumayya ne?kai no yunwa nake ji shi yasa…”
Da sauri ta mike ta shige kitchen ba tare da ta kallesu ba ta fara bud’e warmers ta samu jallop rice da taji koda da kwae sae kamshi take ko ba’a fad’a ba tasan daga gidan Madre aka zo dashi cikin sauri ta cika plate ta zauna cikin kitchen in tana turawa hawaye na bin kumatunta wanda ta rasa dalilin zubuwarsu…
Ma’aruf kam yana ganin K’arama ta shiga kitchen ya janye Sumayya daga jikin shi yana fad’in “Ina boy?
Fari tayi tace “Yayi bacci dear!ya hanya?
“Alhamdulillah.” ya fad’a ta k’ara hugging nashi tare da mashi peck a kumatu ta ja hannunshi ta zaunar dashi saman kujera tana fad’in “K’arama kawo mashi juice da abinci na nan a kitchen bara naje na shirya ni kuma…”
Hannunta ya janyo yace “Ke baza ki iya kawo man ba?
Fari ta kuma yi tace “Dear ban fa k’arashe wankan ba naji ka shigo kasan bazan iya hakura ba banganka ba…”
Kafin yayi magana ta shige ciki tana maimatawa K’arama abunda ta sata… K’arama kam na jinta amma a zabar dake yawo a zuciyarta ta hanata mikewa bare ta kawo mashi abunda ta sata…
Shirun da yaji ne ya sashi mikewa ya nufi kitchen d’in, ya dad’e tsaye a bakin kofa ya hard’e hannayen shi a kirji yana kallonta kamar an mata dole take tura abincin tana kuka motsin da yayi ya sata mikewa da sauri ta juya mashi baya tayi saurin goge hawayenta… a hankali ya matso kusa da ita jikinshi na gogar nata hannunta ya kamo cikin nashi ya d’aura kanshi saman wuyanta kwantar da murya yayi yace “Me nene Hafsah?
Kokarin janye jikinta tayi amma ya zagaye hannunshi a shafaffen cikinta cikin rad’a yace “Me aka maki kike kuka?
A Hankali tace “Ka sakeni please…”
K’ara matseta yayi yana kissing wuyanta yace “Fad’a min kukan me kike?wani abu aka maki daga shigowarki zaki dawo kitchen ki zauna kina kuka kina cin abinci… ?
A Hankali ta tsayar da wuyanta tare da lumshe ido tace “Yunwa nake ji kawai.”
Gira d’aya ya d’age yace “Kawai?
Juye-juye ta fara da k’arfi ta janye jikinta ta juyo suna kallon juna lokaci guda ta sadda kai k’asa tace “Ai harda Headache.”
Ido ya waro yace “Yaushe ya fara maki ban sani ba?
Banza ta mashi ya saka hannu ya janyota jikin shi ya matse yace “Karya bata maki kyau Hafsat… Fad’a min me kikewa kuka?
Muryar Sumayya suka ji a tsaye bakin kitchen tana fad’in “Kut! Na shiga Uku !Ya Ma’aruf me nake gani haka?K’arama a jikinka….???!”
Ku taimakawa K’arama a hannun Sumayya????……HajjaFeedohm kam mun sab’e ta k’warankwatsa ba damu za’a jibgi K’arama ba!Team Maitafasa ku kawo wa jikarku d’auki????????♀
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????
*SADAUKARWA……*
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *85*
*ZIB Gaisuwa da babbar murya Wannan page din nakune kuyi yarda kuke so dashi #Much love????*
Muryar Sumayya suka ji tsaye bakin kitchen tana fad'in "Na shiga Uku !Ya Ma'aruf me nake gani haka?K'arama a jikinka?
K’ara ta saki tare da tureshi daga jikinta…a rud’e take kallon Sumayya tare da Ma’aruf da ya nuna halin ko in kula yana kallonta kuka K’arama ta saki ta nufi gurin Sumayya tana fad’in “Wallahi Aunty…
Wani gigitaccen Mari ta sakar mata tare da angazata da karfi tana fitar da numfashi kamar zaki!a jikin Ma’aruf ta fad’a ya saka hannunshi duka biyun ya zagayeta yana kallon Sumayya…Da sauri K’arama ta tureshi tana girgiza kai tana kuka
Kukan kura Sumayya tayi tana fad’in “Wallahi sae na kasheki sae na rabaki da numfashi yau, ni zaki cuta?Ashe dama cutata kake Ya Ma’aruf sonta kake shi yasa tun tana mayyarta ka daukota ka nema mata magana ashe Kaunace?Plate din dake kusa da ita ta janyo ta jefa mata tana kuka…kaucewa yayi plate din ya fad’a kasa ya saki K’arama ya matsa tare da rungume Sumayyan a jikinshi kwace kanta ta fara kokarin yi tana d’urawa K’arama ashar ya dauketa cak ya nufi d’aki da ita ya kwantar da ita saman bed tare da rungumeta jikinshi…
Dukanshi take tana fad’in “Ka cuceni kaci amanata Allah ya isa!Wallahi ban yafe maka ba mugu, azzulumi, dan iska kawae…Ka aureta mana daka tsaya kitchen kana rungumeta…”
A Hankali yace “Dan Allah kiyi hakuri ki tsaya muyi magana sossae Sumayya…”
Duka ta kuma kai mashi kamar Mahaukaciya tace “Nak’i na tsaya d’in…Uban me zaka fad’a man bayan da idona naga kana rungume da waccen shegiyar mayyar munafukar yar kauyen wallahi sae na kasheta ka sakeni banza azzalumi macuci,uban me yaja hankalinka a jikinta Ma’aruf yarinyar da kama wanka?wannan banzar k’azamar yar kauyen fa ce Ma’aruf?Diyar cikinka amma ita kake runguma a kitchen?
Kwalarshi ta shaka tana fad’in “Ka fad’a man uban me ta mallaka da ya ja hankalinka Ma’aruf?
Runtse Ido yayi yace “Dan girman Allah ki natsu!
“Wallahi baran natsu ba!Da idona na ganka Ma’aruf rungume da yarinyar da ba matarka ba!ka fad’a man yaushe ka lalace har ka fara Zina…?
Sam maganganunta basu b’ata mashi rai ba saboda yasan duk macen da taga mijinta a haka dole ta ji ba dadi a hankali ya rungumota yace “Matata ce Sumayya…