ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A Razane ta dankara mashi cizo tare da tureshi da iya karfin da Allah ya bata!wani kallo take jefa mashi cikin kyarma tace “Gidan ubanwa ta zama Matarka?

Lumshe ido yayi bayya so ya nuna fushinshi akanta murmushin takaici ya saki ya k’ara rungumota yana fad’in “Ki natsu na maki bayani Sumayya…

“Wallahi bazan Natsu ba Ma’aruf…!Ta fad’a kai tsaye tana turo duk abunda ke saman gadon ganin zata fita yasa shi saurin maidota d’akin ya rufeta ta waje ya kira Madre a waya ya fad’a mata abunda ke faruwa ce mashi tayi ya jira gasu nan zuwa har da Abban yanzu…

Kitchen ya lek’a ganin ba K’arama ya sashi lek’awa d’akinta amma babu ita a hankali ya kira sunanta tare da lekawa toilet a mak’ure ya tarad da rungume da Amir da bai san inda ta daukoshi ba, k’arasawa yayi cikin toilet ya d’agota a hankali ya had’eta da jikinshi yana bubbuga bayanta a tare suka furtawa juna “Sorry…”Sannan sukayi shiru kamar ruwa ya cinyesu sae da yaji tsayuwar motar Abba sannan ya janyota ya zaunar da ita kan gado ya fita!yana fita ta rungume Amir ta saki kuka mai cin rai da tasan shigarta kitchen zai janyo wannan bala’in da ta tsaya ko da zuciyarta zata daina aiki……

Su duka aka tarasu a falo a take Abba ya warware mata komae kuka ta fara da yake tana masifar tsoron Abban tana fad’in “An cuceta…

“Waya cuceki A cikinmu Sumayya?Abba ya fad’a tare da kafeta da ido

Cikin kuka ta nuna K’arama tace “An dae cuceni Abba…

Gyad’a kai yayi tare da masu nasiha sosae su duka ya bata hakuri sosae har ta natsu a gabansu…

Madre tace “Ya kamata ka rabasu komae kafin mu tafi ta yarda za’a bawa ita Hafsa din hakkinta a matsayin matarshi bawae a matsayin YAR RIKO ba…”

Harara Sumayya ta watsa mata tare da sakin kuka
Abba yace “Kamar me kenan Hafsat?

“Ina Nufin ka raba masu zaman gidan…!ta fad’a kai tsaye

A Hankali yace “Wannan ai hakkin mijinsu ne…”

Girgiza kai Tayi tana kallon K’arama Ma’aruf yace “Abba ka raba masu komae zata fi dauka da mutunci…”

Mikewa yayi yana fad’in “Kwana biyu biyu kamar yarda shari’ar islama ta raba……

Kukan kura Sumayya tayi tace “Wallahi ban yarda ba…

A Natse Abba ya juyo yace “To ya kike so ayi?

Ba kunya tace “K’wana bakwae bakwae…

Madre zatayi magana Abba ya tsayar da ita yace “Maganar ta ce da mijinta Hafsat mu je kar na kuma jin wata magana ta taso…”

Suna tafiya sabon bala’i ya sake tashi sae dae iyakarta fad’a a baki tare da zagi amma ta dauki maganar Madre bata tab’a K’arama ba,sae dae ta dage akan sae dae ayi kwana bakwae bakwae!Ma’aruf yace “Bata yiyuwa Sumayya kwana biyu biyu na tsara maku…”

Tsaki ta saki tare da wurgawa K’arama harara tace “Wallahi indae ba kwana bakwae ba sae dae ka dinga kwana gidan Madre…

Dariya ta bashi amma yayi k’ok’arin danneta zaiyi magana K’arama tace “Dan Allah Uncle ka barshi a yarda tace …

Duka ta kaiwa bakin tace “Wane shege ya tsoma bakin ki a ciki banza munafuka…Ko ku yarda ko karku yarda abunda na tsara kenan!

“A matsayinki nawa? Ma’aruf ya tambaya kai tsaye

“Na bala’in gidanka… ” ta fad’a kai tsaye

Ranshi ya fara b’aci ya nunata da hannu yace “Mind your laguage and even extra cure of your tongue Sumayya karki ga kamar a kyaleki ne ki kawo man raini wallahi zan sab’a maki sannan ki bar man gidana kuma ki sani babu wanda ya isa ya man dole a cikin zama dake…”

Harara ta balla mashi tana girgiza jiki K’arama kam mikewa tayi ta dauki Amir zata shige d’aki Amma Sumayya tayi kukan kura ta cafko yaron tana fad’in “Aje shi dan ubanki tunda bake kika haifa man shi ba…”

Tana hawaye tace “Aunty dan Allah kiyi hakuri…

A Fusace tace “Na rantse maki da Allah kika kuma kirana da Aunty sae na maki shegen duka a gidannan…

A Hankali Ma’aruf ya tako ya ja hannun K’arama ya turata daki sannan ya kama hannun Sumayya ya shigar da ita daki!Cikin lallashi da dadin baki ya lalaba Sumayya har ta sauko…Sam kin barinshi tayi a fita daga dakin sannan ta kafe dole sae dae ayi kwana bakwae bakwae kuma gurinta zai fara kwana “To” kawae yace mata yana bata hot kiss amma sae tureshi take…

Shi kansh mamaki yake kamar ba Sumayya ba ganin rikicinta ba mai karewa bane ya sashi gyara kwanciya ya juya mata baya tashi tayi zata sauka daga gadon ya maidota da hannu yana fad’in “Kika fita daga d’akin nan sae na bata maki rai wallahi…

Tsaki ta ja tace “Udutti zan dauko ko sae na barta a falo”

Zaune ya mike yana kallonta sannan yace “Dama a gurinki take kwana Sumayya?

Hararanshi tayi tace “Yau nake so ta kwana gurina…”

“To bara ki daukota ba…”Ya fad’a kai tsaye

Cikin daga murya tace “Wallahi sae na daukota”

“Bismillah…”Ya fad’a fuska a daure

Hararanshi tayi tana kokarin sauka daga kan gado ya sa hannu ya fizgota tare da kifa mata mari sannan ya turata saman gadon yana fad’in “Ki sake jaraba sauka sai na baki wanda ya fi wannan wallahi…!

Kuka ta saki tana fad’in “Wallahi ka daki aurenka mugu kawae…!

Dariya yayi mai ciwo yana yace “Bara na sake dukan auren nawa ta yarda bara ya sake gigin dawowa gurina ba…”

Da sauri ta mirgina karshen gadon tana hararanshi …shi kam juya mata baya yayi ya kwanta …da yake muguwar matsoracoya ce kasa fita tayi ta sulale ta kwanta gefe tana kuka…

Da asuba kafin ya tadata sae da ya leka dakin K’arama ya isketa rungume da Udutii suna bacci !leka fuskarta yayi yana kallon,busassun hawayenta sannan ya shafi kanta tare da kiran sunanta…

A Hankali ta bud’e idonta ta mike zumbur tana kalle kalle kafin ta saki kuka tace “Uncle Aunty Sumayya fushi take dani !dan Allah ka bata hakuri matsayin uwa na dauketa bana son fushinta “

Rungumota yayi tayi saurin tureshi tana girgiza kai……

_Mutane wallahi ba kuyi ba, Kamar jiran mutum kuke yayi wani abu ku tasan masa da kanannan maganganu OH!????????‍♀ MUN CE ALMISKI na da side effect kuma baza mu canza ba..!Yeah munsan NANA AISHA (R.D)tana amfani da Almiski duk bayan d’aukewar al’adarta, ke duk bayan al’ada kike amfani dashi koko duk lokacin da kika bushi iska zaki zuba a gabanki…? Sannan irin,Almiskin da Nana Aisha tayi amfani dashi kike amfani dashi kema?karyane Almiskin da ake sayar muku dashi 200 500 karshe 2k shine pure miski a gurinku?Idan haka kuke tunani to tabbas karamar kwalwa gareku.????Saboda masifar iskanci saei a biyoka pc a dinga maka maganganun da mutum bashi da ilimi akansu,kafin kuyi magana ku tabbatar kuna da ilmin abunda zaku fad’a…KAUYAWA KAWAI????

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

 Page *86*

Uncle please dan Allah ka dena janyo min fitina ka fita kaje wajanta kafin yanzuma tazo har ta hanamu yin sallah.”

K’arama ta fad’a tana kokarin kwatar kanta a wajan Ma’aruf, ganin duk ta rud’ene yasa ya saketa tare da mikewa tsaye dai-dai kunnanta ya rad’a mata yace,

“Matsoraci kawai.”

Kasa tayi da kanta zuciyar ta cike da tsoro, juyawa yayi ya fita yana murmushi cikin sa’a kuwa haryaje cikin bathroom Sumayya bata farka ba. K’arama ma tana ganin ya fita ta shiga bayi alwala tayi tazo tayi sallah sannan ta tashi Udutti itama tayi sannan suka kuma komawa suka kwanta sai dai K’arama ta gagara yin bacci tunani kawai take yi na yadda zata samu su dai-daita zaman su ita da Sumayya dan bata so ace sunyi zaman kishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button