ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana idar da sallar Sumayya ta farka, gadon Amir ta fara dubawa taga yana nan sannan ta harari Yaya Ma’aruf dake zaune kan sallaya yana lazimi be kulata ba dan yasan dole idan ta farka sai ta ci gaba da tijararta, mamakin shi d’aya yadda yaga ta iya bacci suna tare amma bata rungume shi ko kuma duk cikin kishin ne oho ya tab’e baki.

Sumayya na fitowa ta zari hijjb ta kuma d’aukar extra sallaya sannan tayi hanyar parlor, anan tayi sallah kasan cewar tasan idan a d’aki zata yi toh Ma’aruf zai iya fitowa yaje d’akin K’arama. Shima kamar yasan target d’inta dan haka yana kammalawa yayi bathroom ya kunna heater sannan ya koma kan gado, laptop d’in shi ya bud’e ya fara aiki sai dai duk kusan rabin hankalin shi yana ga K’arama, ko tayi bacci, ko kukan ta cigaba dayi duk babu wanda ya sani dan haka zuciyar shi ta fad’a cikin zullumi.

Ihun daya jiyo shiya sashi fita da gudu, a d’akin K’arama ya jiyo dan haka ya karasa ciki me zai gani! Sumayya ce zaune a ruwan cikin K’arama sai jibgarta takeyi sannan ta shak’i wuyanta, shima iya karfinsa yasa tare da yin ball da ita nan tayi gefe har kanta ya bugu da katakwan gadon d’akin.

Da sauri ya d’aga K’arama wadda ke ta faman rik’e wuya tana tarin wahala, Ma’aruf na niyar yin fad’a ya hango Udutti makure a karshen gado sai kuka take yi, saurin sakin K’arama yayi ya k’arasa wajanta tare da d’aukarta duk da tana da girma jan hannun K’arama yayi suka fito, ganin haka da Sumayya tayi yasa ta kuma yo kukan kura tasa hannu biyu tare da tura K’arama tayi gaba tare da buguwa da k’ofar d’akin kafin kace me goshinta da hannun hagonta sun bugu.

Wani wawan juyi yayi tare da kai idanunshi k’asa inda K’arama ke zube goshinta na fitar da jini, da sauri ya kalli Sumayya lokaci guda idamuwan shi sunyi jawur kamar taruwar jini ita kuma ta rik’e kugu sai girgiza take jira kawai take ya kawo mata duka itama ta zage ta rama amma sai taga sab’anin haka, d’ago da K’arama yayi tana mik’ewa tsaye ta saki wani uban ihu tare da komawa k’asa ta sulale sabida ji tayi tamkar zai cire mata kafad’a.

“Uncle hannuna ya cire.”

K’arama ta fad’a tana kuka, cicib’ar ta yayi suka fita ganin ya d’auke ta yasa zuciyar Sumayya tunzura da gudu tayi hanyar kitchen ta d’akko muciya, Udutti na zaune sai kuka takeyi a haka Sumayya ta tsallaketa, sai da ya shigar da K’arama cikin mota sannan yayi saurin komawa drive seat yana zama kawai yaji taratsatsa! Kallon gurin yayi a tsora ce nan yaga Sumayya r’ike da muciya ta fasa mai glass na setin da K’arama ke kwance.

“Wallahi yau sai naga karshen cin amana, sai naga karshen wulakanci a gi..”

Bata k’arasa taji wani gigitaccen mari a duk gefen fuskarta wanda yayi sanadiyar sa hakorinta yin girgid’i, damkar ta yayi yana janta zuwa waje mai gadi da maiyi musu wanki da goga suka fito suna bashi hakuri, ko sauraran su beyi ba ya bud’e karamar kofar gidan tare da tunkud’a Sumayya waje, ihu ta dinga kurmawa shi kuma ya koma ciki tare da figar motar afusace yayi hanyar get har yana neman latsewa me gadi yatsun kafar shi.

Wani pravite hospital ya nufa zuciyar shi a jagole, yana zuwa nurses suka d’auki K’arama aka shiga emergency room da ita sai faman kuka take tana jin ta tamkar ba ita ba, yana tsaye yaji ringing d’in wayar shi zarowa yayi nan yaga sunan my everything wato Madre, wani zazzafan yawu ya had’iya kafin yayi peaking tare da karawa a kunne yayi shiru ba tare dayayi magana ba dan zuciyar shi wani zafi take yi mai.

Cikin kakkausar murya yaji Madre na tambayar shi,

“Ma’aruf kana ina?!”

“Hospital.”

Ya fad’a a hankali yana kallon kofar room d’in da yake jiyo ihun K’arama, cike da mamaki Madre ta kuma cewa,

“For doing what?!”

K’irjin shi ya dafe tare da rufe idanuwan shi sannan yace,

“Madre na kawo Lil Hafsat ne za’ayi treatment d’inta.”

“Treatment kuma Ma’aruf me yasa meta sannan kuma meya had’aka da Sumayya harka fasa mata baki tare da yi mata d’ankaran duka kuma ka koreta?!”

Shiru yayi dan yasan yanzu idan yace zai yi magana toh zuciyar shi na gab da kumbura dan haka sai daya dad’e kafin yace,

“Madre ki taho Haske pravite hospital zaki ga komai sannan zaki ji komai da idanki a kuma zahira ba labari ba.”

“Ok I am coming soon..!”

Ko miniti 10 ba’ayi ba sai gata, number d’in room d’in ya gaya mata taje. Madre na shiga taga K’arama a kwance an nad’e goshinta da bandege hannan kuma nannad’e an sargafe mata shi da wani zare ya biyo ta wuyanta, salati Madre ta saki tana tafa hannuwa har takai kusa dasu tana kallon K’arama wadda Ma’aruf ke zaune akan kujera yana kallonta.

“Hafsatu meya faru haka yau na shiga uku ni Hafsat me zanji mezan gani.”

Zama Madre tayi bayan Ma’aruf ya tashi yabar mata kujerar, cikin alhini ta kuma tambayar abunda ya faru nan ya sanar da ita iya abinda ya sani sannan ya d’ora da cewa,

“Wallahi Madre bansan yadda zanyi da Sumayya ba, duk iya yadda zanyi daga jiya zuwa yau na ganin ba’ayi abinda zai tada rigimaba sai da nayi Madre, amma yarinyar nan sai da ta yi tasan abinda zai janyo tashin hankali a tsakanin mu na kasa gane meke damunta dan wannan ba kishi bane…”

“Hmmm Sumayyatu kenan, ai ni dataje babu ko d’an kwali tana kuka tace min kana tashi daga bacci gurin Hafsat katafi dama da dare saidaka ci mata mutunci bayan mun tafi, toh shine bayan ta fito ta ganka da Hafsat kana shan bakinta oh ni Nana hafsatu, toh shine dan tayi maka magana ka rufeta da duka sannan ka korata gida kaji abinda ta ce min.”

Ma’aruf kuwa yana jin Madre tace Sumayya tace wai yana shan bakin K’arama yayi saurin rintsa idanuwa, shin wannan yarinyar wace irin mata ce da batada kunyar furta ko wace irin kalma a gaban ko waye ciki kuwa harda mahaifan shi. Allah ya shiryeta ya ganar da ita yasa ta gane illar furucin ta a bainar jama’a da kuma karyar data koya. Ya fad’a a cikin ranshi, yana rik’e da goshin shi yaji muryar K’arama cikin kuka tana yiwa Madre magana,

“Madre wallahi Allah ba haka bane, ita aunty Sumayyan ce ina kwance nida baby Udut kawai ta shigo d’akin ta na duka na wai..wai…wai karna lalata mata ‘y…”

Ta kasa k’arasawa sai kuka take zabga, a kid’ime Ma’aruf da Madre suka zaro idanuwa jin furucin K’arama na karshe dan ko bata k’arasa ba sun fahimci abinda take nufi.

Hakuri Madre tayi ta bawa K’arama suna nan harta fara bacci, gado aka basu har na tsawan kwanani uku kasan cewar gocewar k’ashi K’arama ta samu a hannunta, Madre ce ta kalli Ma’aruf yayi shiru harya d’an fad’a sabida shiga tashin hankalin da beyi tunanin zai shiga ba.

“Ma’aruf tashi kaje gida inyaso sai ka d’ebo yaran dan duk a gida kuka barsu itama bata d’akko kowa ba.”

Zambir Ma’aruf ya mik’e dan sam ya manta da Udutti da Amir a gida, car key d’inshi ya d’auka da azama yayi saurin barin d’akin yana cewa,

“Ok ina zuwa Madre.”

“Toh sai ka dawo Ma’aruf.”


Ma’aruf na shiga gidan tun daga compound yake jin kukan Aminr yayi saurin fita a cikin motar ko kasheta beyi ba ya nufi cikin parlor, mamaki ne ya kusa kasheshi dan ganin Sumayya da yayi a zaune kan kujera tana kad’a kafa yayinda Udutti ke makure jikin kujera ta matse Amir a jikinta suna faman kuka.

Kutakan Sumayyar bebiba yayi saurin zama tare da d’ora su akan cinyar shi gabaki d’ayan su, lallashin su ya fara yi cikin sa’a ya samu Udutti tayi shiru sai ajiyar zuciya da take yi jefi-jefi ya zamana Amir ne kad’ai keta faman kuka yana janyo gaban rigar Ma’aruf alamar yana neman abincin shi, ganin haka yasa Ma’aruf tausasa murya ba tare da ya kalli Sumayyar ba yace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button