ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kizo kibashi ya sha dan shi bashida laifi nine kuma ni zaki wulakanta amma shi yanada hakk’i akan ki…”
Wani shegen kallo ta watsa mai na irin zoka kwata d’in nan amma da yake ba kallonta yake yi ba sai taji be tanka mata, tsaye ta mik’e tana gyara su a cikin riga lokacin ya d’ago yana kallonta jin batayi magana amma ta mik’e, yatsina fuska tayi sannan tayi taku d’aya biyu tana ce mai,
“Oho ashedai nima ina da rana a gurinka Ma’aruf? Toh bazan bayar ba dan Allah kaje ka kawai waccan shegiyar yarinyar ta bata ai daman amfanin ta kenan, amma ni wallahi bazan bayar ba yadda ka fasa min bakin nan.. !“
Sumayya tayi maganar tana jan tsaki tare da rik’e kugu kamar yadda tayi d’azu,
“Tab lallai da ace ba uwa d’aya bace ta bamu tar biya ba da zan iya cewa ke d’in Sumayya tsinanniya ce, dan baki da mutunci ki haifi d’an da kanki sannan kizo kibashi abu yashi shine zaki ce min naje gurin wadda bata son meye haihuwa ba ta bashi…?!”
“Ashe kaji ni, ai wallahi Yaya au Ma’aruf ka d’ebowa kanka masifa dan sanin kanka ne bana kaunar kishiya amma kaje kayi min da yarinyar da ta tashi a gaban idona dan ka raina min hanka….”
Bata kai karshe ba taje an buge bakin nata, cike da masifa ta waigo tana zagi wa zata gani, kawai sai taga….. Shima Ma’aruf ganin haka yasa shi saurin mik’ewa yana kallon su baki bud’e…..
readers
Hajjafeedohm
Wannan shafin na duk wani makarancin ABIN DAKE B’OYE ne, mungode muku da soyayya tare da binmu sau da kafa, harda real mai dambun ‘yan gayu na kabeje bana zogale ba mun gode muku all????
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *87*
A tsaye taga Mama Hindu kanwar Mamanta fuskar nan a d’aure cikin b’acin rai take kallonta bayan duk taji abinda take fad’awa Ma’aruf d’in dan haka ranta ya b’aci sosai tace.
“How dare you da zaki zauna kina fad’awa mijinki uban ‘ya’yanki wannan maganar Sumayya? Bari kiji in gaya miki mu d’ukan mu ann aikin banza ne a yanzu a wajanki domin sai kin nemi aljannar ki a gurin shi sannan zaki shiga aljanna, sannan nonon mahaifiyar shine kawai baki shaba amma Hafsat itace taci kashinki taci fitsarinki amanki wawuya sakarai kawai,
Sannan da kike cewa ba zai yi aure ba ke yanzu me zaki iyayi mai Sumayya? Bayan kin rigada kin wulakantar da rayuwar ki wannan abun da aka gaya min shine daliliin da yasa kika ganni a cikin gidan nan, domin koda Ma’aruf be auri Hafsatu ba toh sai nasashi ya dad’a yin wani auran.”
Baki Sumayya ta turo tana yatsina fuska tare da bubbuga kafafuwa tamkar k’aramar yarinya, Maman hindu d’in ta kalla tare da cewa,
“Gaskiya ni dai Mamah kiyi shiru ya kike min fatan kishiya bayan kefa Mamah baki da ita kuma itama Madre bata da kishiyar nan sannan har Ummata tabar duniya batada kishiya, Yaya Najib da Yaya Suhaima dama Yaya Maryam duk babu me kisha ko mata biyu a cikin su sai ni za’a sawa ido ni wallahi bazan yadda.”
Tayi maganar tana kuma sakin kuka, kallon banza Mamah tayi mata shi kuma Ma’aruf gabaki d’aya an sashi a duhu ya kasa gano inda maganar Mamah ta nufa dan haka beyi k’asa a gwaiwa ba ya tambayi Maman hindu,
“Mamah meke damun Sumayya wanda har yasa kika taso tun daga Adamawa zuwa nan har ma da kwararamin gwaiwar yin wani auran..?!”
K’arasawa tayi wajan shi ta k’arbi Amir, Sumayya ta kalla tare da cewa,
“Zo ki karb’e shi maza-maza ki bashi yashi sakaran wufi kawai, Sumayya waya gaya miki ana fushi da ‘ya’ya amma dan sakarci ke jariri ma kike horawa da yinwa..”
Amir ta k’arb’a sai hararar shi take yi kafin ta fito dashi tasa mai a baki, ganin tana bashi yasa Mamah ta koma kan Ma’aruf dake faman kallon Sumayya dan karta kashe mai yaro tunda yaga alamar yau hauka takeji, muryar Maman hindu yaji tana cewa.
“Ma’aruf ka koma can asibitin muma yanzu drive zai maida mu can gidan Madre, idan komai ya lafa lokacin sai muyi magana akan matsalar Sumayya d’in….”
Yace “toh Mamah amma ku bari na kaiku da kaina mana.”
Mamah ta kad’a kai alamar a’a sannan ta d’ora da cewa,
“Zo ka tafi ai tare nake da drive kai dai kawuce kawai.”
Mik’ewa yayi ganin haka yasa Udutti saurin tashi itama tare da rik’e mai k’asan riga, kuka take yi tana cewa,
“Papa please take me out, bazan zauna a nan ba Mami dukana zata yi please…. !“
Kallon Sumayya Mamah tayi cikin takaici bata yi magana ba ta kalli Ma’aruf dake niyar lallab’e Udutti tace.
“Tafi da ita Ma’aruf ba kowa yaja wannan abun ba face uwarta, dan haka tafi da ita inda hankalinta zai kwanta.”
Yace “Toh Mamah.”
Daga haka ya mik’e tare da kama hannun Udutti suka nufi k’ofa, nan da nan Sumayya ta fara bala’i tama manta da cewar Maman Hindu na nan.
“Wallahi Allah ya isa, ai ni Matar shi ce amma me yasa ba za’a dinga kula dani ba sai wata can banza wawuya sakarai ‘yar kauye za’a wani…..”
Tassss! Sumayya taji wani gigitaccen mari, aikuwa ganin wanda yayi mata yasa ta kuma rushewa da kuka tare da ture Amir daga shan nonon da yake yi ta ruga da gudu cikin bedroom d’inta tare da kullowa. Kokarin dawowa ciki Ma’aruf yayi dan ganin yadda Mamah ta mareta da hanzari Mamahn ta nuna mai hanya ba tare da tace komai ba, jikin shi duk a sanyaye ya juya suka tafi ita kuma ta fito tasa drive ya maida ita gidan Madre bayan ta tsaya a super market ta siyi madarar da zata dinga bawa Amir.
Sai da K’arama ta kwana uku a hospital sannan aka sallamesu kasan cewar ciwon dake goshinta ya warke befi sauran k’arashe ba, sai gocewar kashin dake hannunta shi kuma sai a hankali, a tsakanin ranakun abubuwa da yawa sun faru, ana sallamar su gidan Madre suka wuce acan suka tarar Mamah tayi musu lafiyayyan girki mai rai da motsi, sai da Mamah tayi wa K’arama wanka kasan cewar bazata iya ba sannan suka koma parlo akaci aka sha, wajan karfe 7:08pm sai ga Sumayya babu abinda aka nuna mata hakan yasa ta shiga ciki ta zauna sai faman hararar K’arama take yi.
A d’add’are K’arama tace,
“Aunty Sumayya sannu da zuwa ina wuni..?!”
Mtwwwwwww! Sumayya taja wani shegen tsaki mik’ewa tayi ta nufeta zata d’auke Amir dake kan cinyar K’arama Maman hindu tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa,
“Kul Sumayya! Kika sake naga kin tab’a yaron nan wallahi sai na lahira ya fiki jin dad’i marar kunyar yarinya.”
“Toh wallahi ni dai a d’aga min yaro daga kan wannan wawuyar yarinyar mayya da iyayenta suka kasa kula da ita sai aka bawa wani…”
Babu wanda ya kulata ganin haka yasa ta saki kuka nan ma still akayi mata banza sai ma hirarsu da suka ci gaba dayi, K’arama kuwa tunda tayi kasa da kai bata sake d’agowa ba har sai da taji shigowar su Abba da Ma’aruf, tana d’agowa suka yi ido hudu ya sakar mata wani kayataccen murmushi tayi saurin maida kanta k’asa kirjin ta na bugawa kartaje ko aunty Sumayya ta gani.
Duka guri suka samu zama suka yi yayin da Abba yabi Sumayya da kallo wadda ganin shi yasa ta fara kukan kasa-kasa sab’anin da datakeyi kamar an doketa ya kalleta yace,
“A’ah Sumayya ya da kuka kuma a gaban yaranki?!”
“Abba Maman jindu ce.”
Ta fad’a tare da yin shiru tana turo baki kai kawai ya kad’a Ma’aruf ya kalleta suka had’a idanuwa, baki ta murgud’a mai tare da hararshi. Muryar Abba suka ji yana cewa.