ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Banza ya mata ya juyar da kai gefe guda tare da fita daga gidan suka tsaya jikin motar yanawa Focal person magana ……

Lokacin Lauratu ta iso garin tana hango dandazon yaran da matan aure da itama ta kutsa kai cikinsu ta tsaya gaban Ma’aruf din tana sauraren abunda yake fada duk da dai ba ganewa take ba saboda mafi maganarshi turanci yafi yawa ……

Uban Ihu Jaririyar ta saki tana kuka …
Kallonta yayi ya dauke kai saboda baya kaunar kuka yana fadin “Bar nan gurin……”Fuska a daure

“Ina Saurarenka ne Bature……”ta fada tana jijjiga yarinyar,Cigaba da kukan jaririyar tayi tana mutsu mutsu a bayanta ……Kukan ya fara isarshi cikin tsawa yace “Shut up ki bar nan gurin……”

Dariya tayi tace “Ba sunana Shutu ba Sunana lauratu!yar kanwata kuma Hafsatu……”

“Hafsah……”ya fada yana kallonta “Kawota mu gani……”ya karashe maganar tare da mika mata hannu

Da mai unguwa ake kokarin kwanto yariyar tare da mika mashi”Me yasa ba’a saka mata kaya ba?ya fada idonshi na kan yarinyar……

“Bata dasu Bature shegiya ce ita ce warda Uwarta taci amanar mijinta da ka dubo yanzu……”Cewar mai tafasa sannan ta kalli lauratu tace “Karbeta ki bar nan tun kafin na fasa maki kai……”

Fitinannen kallo ya watsawa Mai tafasar sannan ya fito da kudi akalla sunkai 50k ya mikawa Focal person din yace “Ka sayar mata duk abunda ya dace……”Mikawa lauratun ita yayi ya bude mota ya shiga Sannan Focal person din ya karbo sample Urine din da akace a kawo suka shiga motar suka tafi ……

Mai tafasa da sauran mutanen garin Mamaki ya hana su magana har sae da suka bar ganin kurar motar su sannan Mai tafasar ta juyo da niyar Zazzagawa Lauratun ruwan masifa amma ta nemeta ta rasa……

Lauratu kam bayan gida ta zagayo ta shigo ta karare ta shige bukkar Malan Lado ……Kwance ta iskeshi kamar kullun idonshi a rufe sae dae hawayen dake zubowa……kwanto jaririyar tayi ta daura mashi saman kirji ,ya dube ido da sauri yana kallonsu ,lokaci guda ya fara gyada kai yana murmushi dake dauke da hawaye yana kallon yarinyar ……
Jikin lauratun yayi sanyi tace “Baffa yarinyar ka ce ko?

Gyada kai yake da sauri yana murmushi ,Itama murmushi tayi ta janyo kwanon furan da ta gani gefe tana fadin “Baffa ka sha?

Girgiza mata kai yayi yayin da murmushin fuskarshi ya bace ,Shiru tayi sannan ta dauke diyar daga jikinshi ta dago kanshi tana bashi furar……
Sae da yasha sossae Sannan Jaririyar ta tsangare da kukan da yasa Mai tafasa da kumdum suka nufo bukkar suna fadin “Wane Shegene anan ciki?

Kwantar dashi tayi da sauri ta dauki jaririyar ta fice ta yar kofar dake bayan bukkar ta bi ta karare ta fita ,Suna shigowa suka ga babu kowa……

Kundum tace “Lado hala wannan Shegiyar yarinyar ce ta shigo……”
���� ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ����
                  ��

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM��
&
_K.A.S Precious HAJJA CE��

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu

    Page *13-14*

*S*hiru yayi ba tare da yayi magana sai faman binsu da kallo yake har suka fita suna wa lauratu masifa ga bak'in cikin ganin uban kud'in da aka bayar wai a siyama jaririya kaya.

“Kur’anin Allah ko Mai-tafasa? Ina tausayin Hafsatuwalle duk ranar da lado ya samu sauk’i. Cewar kundum tana kokarin fita daga gidan gashi daga ita sai karigirji da zanin tsohowar atamfa wanda yaji dunyi ta d’ora akanta ko yaya ta d’aga hannu gashin hammata ne cacim tamkar zakayi kitso.

“Humm ! kaji ki Kundum da wani zance, yo ce miki aka yi yadda zai yi? Jira kawai nake aradun Allah yaji sauki har gida zamu je ya tona mata asiri, dan taga ba magana yake yiba shine zata mai sharri muguwa kawai.”

“Mudai muna jiran ganin irin hukuncin lado, dan a lokacin ne Abunda ke b’oye zai hito hili…”
Kundum Tana fad’a tabar gidan da ragowar guntun gulman ta, lado kam yana ciki kwance yana jiyo su ji yake tamkar ya tashi amma ba dama hawaye suka zubo mai kafin kuma yayi murmushi yana kallon kirjinshi dai-dai inda laurtu ta d’ora mai jaririyar.

{{ }} {{ }}

Lauratu na shiga kauyan su da farin ciki dan har tama manta da zance wani 6acin rai sai da tashiga gidan su taji fad'uwar gaba ta k'arasa cikin rumfar su. 

A zaune ta ga Umman ta tayi ta gumi wanda daga gani tayi nisa cikin tunani, duk sallamar da lauratu keyi Umma bata jita ba sai da ta k’arasa kusa da ita tare da janye hannun ta wanda ta tallafi habarta dashi tace “Umma na lahiya ko?” Kallon lauratu tayi tare da k’ak’alo murmushi wanda be kai cikin zuciyar taba, “me zata cewa lauratu bayan duk tunanin ta yana kan yadda taga tun yanzu ana muzguna musu ! ana kyarara su tamkar tumaki, koda yake yanzu tumakin su sun fisu daraja da kima a idanun mutanan gidan.” Umma Hafsatu ta fad’a cikin zuciyar ta, ganin irin kallon tuhumar da lauratu ke yi mata ne yasa ta kara wani murmushi cikin sanyin murya tana kallon Hafsat dake hannunta tace.

“Ba komai lauratu ina nan ina tunanin ku karkuje wasu suyi muku wani abun. Har kin samo mata kamfai d’in?

Umma ta fad’a cikin yana yi na bagarar da tunanin lauratu da ta kafeta da manyan idanuwanta. Zama lauratu tayi akan langa-langan data kwana akai jiya sai faman k’ara yake k’arass-k’arass ta bud’e guntun d’ankwalin da ta nad’e Hafsat dashi tana nunawa Umma kanfan (pant) da ta sai mata tare da cewa.

“Eh Umma na samo kuma munje gidan Mai-tafasa har muka tarar wani bature mai kyau yazo yana duba Baffa. Sannan Umma ya bada kud’i yace a siyawa Hafsat kaya amma banga mutumin ba sabida na zaga gurin Baffa har yaga Hafsat yayi murna.”

Hirarsu suka yi ba tare da kowa ya lek’osu ba. Ganin rana tayi ne yasa su fitowa tsakar gida dan su kamawa mutanan gidan aiki. Da sauri Bultuwa ta janye kwanan garin dake gaban ta ganin Umma na kokarin kar6a dan ta tayi tankad’an cikin nuna kyama Bultuwa na sosa cikin hancinta tace.

“Kaunan Hafsatuwalle ki bani guri da wannan kazamin jikin naki. A kul ! na sake ganin kinzo wai da nufin ki kamamin aiki na bana so.” Cak… ! Umma ta tsaya tana mata kallan mamaki lauratu ta sunkuyar da kai cikin takaicin ganin yadda ake musu wulakanci Mai-aya dake rik’e da tukunya tace.

“Aikuwa dai gara kiyi kayanki kar a goga miki cikin kato kema wataran kiyi.” Wata mata itama dake gefe guda tana yiwa yarinyarta tsifa gashin yarinyar jawur kamar anrina shi ga uban kasa akai amma jira ake a tsefe ayi kitso ba tare da an wanke ba tace, “Bultuwa kinyi dai-dai tallahin Allah k’ara da kika d’auke kayanki.”

Jin maganganu sunyi yawa ne yasa Umma da lauratu komawa cikin rumfar su, zama suka yi akan mayafin lauratu da ya zamar musu kamar da6en kasa Umma na kuka k’asa-k’asa ta kalli lauratu da itama hawayan take yi “lauratu kiyi hakuri kuma ki yadda dani cewar Hafsat ta lado ce k’anwarki ce karki biyewa bakin mutanan nan….”

Lauratu ta gir-giza kai sannan tace, “Umma rik’eta naje na dawo yanzu.” Kar6arta Umma tayi tana kallon lauratu “ina zaki kuma da rana haka Laure???”

“Umma gidan mai-unguwa zani ana bada tuwon sadaka nima bari naje na kar6o mana.” Tana fad’ar haka ta fita bata jira cewar Umman ba…..

{{ }}

Yana komawa cikin hotel d’in da aka kama mai ya cire kayan jikin shi tare da shigewa toilet, wanka ya dingayi sabida shi a tunanin shi ya kwaso wannan warin da yaji a gidan da suka je, sai da ya tabbatar ya cud’a ko’ina sannan yayi alwala yafito jikin shi d’aure da towel hannunshi da small one ya k’arasa jikin dressing mirrow yana goge jikin shi mai d’auke da kwantaccen gashi mai yawa a k’irjin shi da hannayen shi da kafafuwa.

Tsaki yayi ta faman saki yana tuno yadda yaga suna shiga kauyen daga manya har yara dukun-dukun dasu hanci duk majina sunyi fututu kamar suna birgima a jar kasa, suna hango mota kowa ya fara gudun shiga gida, yaji haushi sosai sai kace wasu 6arayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button