ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata kalleshi ba ta amsa “Na’am…!

Hannu ya saka ya tadota zaune yana kallonta cike da so tare da janyota jikinshi sosae yace “Ki tashi kiyi breakfast sae ki koma ki kwanta kin ji ko…”

Kanta ta sunne k’asa tana jin wata irin kunyarshi na ratsa ta sam ta kasa had’a ido da shi sae sunne sunne take cup din tea ya kafa mata a baki duk da yasan da zafi …

Ta kusa furzar da sauri tana kallonshi a shagwabe tace “Uncle da zafi ka bani…”

Kashe mata ido yayi yace “Ko?

Ta turo baki tare da janye jikinta daga nashi ta juyar da kai …Dariya ta bashi ya kara janyota tare da kafa mata cup din a baki wannan karon turewa tayi tana hararanshi k’asa k’asa tace “Uncle da zafi fa nace maka kuma ka k’onani…”

Kamar gaske ya dafe kai yana fad’in “Oh to yi hakuri muga inda kika k’one?ya k’arashe maganar tare da tura hannunshi a bakinta yana lalubar saman tongue dinta…sannan ya kai bakinshi dai dae nata ya hade su tare da tsotsar tongue dinta na yan mintina sannan ya zare yana kallon yarda ta lumshe ido ……

A Hankali yace “Ya warke ko?Shiru ta masa idonta har lokacin a lumshe…

Murmushi yayi mai sauti yana fad’in “Sorry bara na hura maki ya huce…!

A Hankali ya ciyar da ita har sae da ya tabbatar da ta k’oshi sannan ya mike ya mayar da plate din kitchen ya dawo d’akin

Kamar tayi kuka tace “Uncle ina son zan gayar da Aunty “

Hannu ya mika mata ta kama ta mike suka fita, d’akin sumayya suka shiga suka iske tana sakawa Amir kaya daga bakin kofa K’arama ta toge ta tsugunna tace “Aunty Ina Kwana?

Banza ta mata ta cigaba da abubda take Ma’aruf ya matsa kusa da ita tare zama bisa cinyarta yace “Tana gaidaki”

Tureshi tayi tace “Na dauka da Amir take”

Waro ido yayi yana murmushi don yasan tana sane da ita take ya janyota jikinshi yana fad’in “Da ke take Sumayya”

“Ok…”ta fad’a tana hararanshi

K’arama kam a sanyaye ta mike ta bar d’akin yayin da Sumayya ta bita da kallon sannan ta mayar da kallonta ga Ma’aruf cike da tuhuma kamar zatayi magana kuma ta share ta cigaba da shirinta shima wanka ya shiga ya shirya sannan ya kira Su Madre suka ce su suke jira, gurin K’arama ya koma yace ta shirya su tafi!sae da ta kuma wanka sannan ta saka wani atampha sky blue da ratsin orange a jiki ta dauko after dress ta daura sama tare da rolling da gyalenta powder kawae ta shafa tare da lipstick ta fesa turare……das ta fito da ita kamar ba ita ta dauki plate shoes orange ta saka tayi k’ok’arin dae daeta tafiyarta ta fita!a falo ta iskesu yayin da Sumayya ta bita da wani shegen kallo tare da kwafa ita kam hannun Udutti ta rike kanta a k’asa tayi gaba Sumayya ta mara mata baya sannan suka tafi…A Gaban mota Sumayya ta shiga yayin da Su K’arama suke a baya……
Ta glass din motar ya kalleta ya sakar mata lallausan murmushi tare da kashe mata ido ya dauko wayarshi yana latsawa sannan ya tashi motar …

Dan guntun text ya shigo a wayarta ganin sunan Uncle yasa ta kalleshi da sauri sae taga sam hankalinshi naga Sumayya ko mai yake fad’a mata oho ta ga dae tayi dan guntun murmushi tana harararshi……

Text din ta bud’e “Let’s stay this way forever. I love you” Abunda ya rubata kenan…Kallonshi ta kuma yi cikin sa’a suka had’a ido ya sakar mata mayun idonshi ta mirrow tayi saurin sadda kai k’asa cikin kunya…Taso ta tsayar da idonta cikin nasa amma ya mata kwarjinin da bara ta iya ba tana da tabbacin Uncle dinta na da kaso mafi tsoka a cikin zuciyarta idan tace bata jinshi a ranta ta yi karya mafi muni a rayuwarta tabbas shine jigonta domin ta d’ad’e da sanin haka…Lumshe ido tayi tana k’ara jin wata kaunarshi na zagaye mata duk wani tunaninshi sam bata ganin girmanshi ko shekarun da ya bata kaunarshi kawae take gani a zuciyarta ……

Sae da suka d’auko Madre da Abba sae Mamah hindu sannan suka tafi airport sam Sumayya ta hanashi keb’ewa da K’arama tana makale dashi duk da yana bukatar hakan, har Abba yace su taho su koma… A Hanya ya tsaya ya sayar masu fruit da yan tarkace sannan ya aje su gidansu Udutti ya wuce shima……

【】

Hafsuwalle kam zaune suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali ga wata soyayya da mutane gidan da kauyen ke nuna mata ko da yaushe Ma’aruf cikin aiko masu da kudi da kayan abinci yake duk da K’arama bata sani ba, sam bata da matsala a rayuwarta sae dae aure da aketa maganar tayi amma tace ba yanzu ba …

Lauratu ma duk da tana kauye tayi bul abunta domin Sallau bai rageta da komae ba!Ma’aruf ya aiko aka saka yaranta tare da wasu yaran na cikin gidansu makaranta a cikin gari sannan idan suka tafi tun karfe 8 sae 6 na marece zasu dawo saboda boko ce da islamiyya sannan kullun motar aikinsu zata zo ta dauki yaran ta kaisu Makaranta ta dawo dasu sam basu da matsala a rayuwarsu sannan duk abunda yake sam K’arama bata sani ba……

Kafin Ma’aruf ya bar k’asar sae da ya masu hanya Unicef ta dauki nauyin yima kauyen titi tare da gina masu karamar makarantar boko da karamin Asibiti !sosae Hafsuwalle take samun girma daga gurin ilahirin kauyen da makwabtansu ganin duk sanadinta suka samu cigaba ……
Maitafasa ma an ware mutunci bad’a bad’a da su Hafsuwalle soyayya take nuna mata kamar itace marigayi Ladon don bata kwana biyu bata zo ta ganta ba kuma bata zuwa hannu d’aya sae ta taho mata da tafasa da hura …Kundum ma ba laifi ta rage duk wani munahurci tana bin maitafasa so da kafa zamansu gwanin ban sha’awa sannan suma duk lokacin da Ma’aruf yayi masu aike akan debi wani abu akai masu…

Yauwa kamar kullun maitafasa tana tsige tafasa Kundum ta fito daga ban daki tana tsefe kanta tsaki Maitafasa taja tana watsa hannu tace “Wae Kundum anya gurin gyatumarki kikayi wayau kowa?

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????

   *SADAUKARWA……*

HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu

Missing Some one Likely to call her back 【Aunty Sis????】

   Page *89*


 *D*ariyar yak'e Kundum tayi tace "Oh ni Kundum me kuma nayi haka maitafsa?

Ta kuma watsa hannu tace “Banda rashin sanin ciwon kai da rashin fad’an gyatuma meye na tuge kai a makewayi?

Tab’e baki Kundum taya ta watsa hannu gaba ta fad’a bukkar ta tana fad’in “In ko rashin fad’an gyatuma ne Maitafasa to kema bana tunanin kin iske gyatuma a raye tunda kema kina toge kan a makewayi.”

“Ki kace me! ban iske gyatuma a raye ba?” Maitafasa ta fad’a cikin d’aga murya.

Banza kundum tayi mata ta mike tana watsa hannu tace “Ta kwarankwatsa Allahu ya kaimu lokacin da bature zai yi mani aike Aradun Allah ko kwayar hinkaha bakici…”

B’urum! Kundum ta fad’o tsakar gida tana fad’in “Me yayi zahi Maitafasa?ta kwarankwatsa ba haka nake nuhi ba…”

Banza Maitafasa ta mata kusa da ita ta motso tace “Haba Suwaibatu kakarsu Hafsatu da lauratu dan kin hanani kayan arziki me kika yi kenan?duk duniyar ga kowa ya sani sanadin jikarki kauyen ga ke ta bunk’asa, kowa yasan jininki jinin daraja da arziki ne Suwaiba!Idan kinga dama yanzu zakice a kwashe kwaltar titin kyauyan nan ko kuma ki hana kowa bi ta saman shi tunda mijin jikarki ne yasa a kayi shi, ko kuma ki rushe boko da arabi babu wanda ya isa ya tanka Suwaiba Mai abun Alkhairi kakarsu Hafsatu matar Bature. Aradun Allah yanzu baki da kamata a kauyen ga!aradun Allah haka nima banda kamarki yanzu ki ya heni nima na dangwali arzikin jikarki Suwaiba…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button