ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

K’irarin ya sata washe jajjayen hakoranta tare da kaiwa Kundum duka a kirji har zaninta yana kwancewa tana fad’in “Dad’i na dake Kundum kin san lagwan Maitafasa, ta k’warank’watsa ni dake mutu ka raba!tahi ki hirya muje gano jinin alheri (Hafsuwalle) hinkafa kam har sae kin ture ta aradun Allah.”
Ard’o ya shigo yana kwalawa Inno k’ira kamar had’in baki mutanen gidan suka fito cirko-cirko ya bisu da kallon takaici yace “Wai wane irin iskanci kuke haka ne?me yasa idan an kira mutun d’aya sai ku fito kamar ku aka kira gulma ko me?!”
A Hankali suka fara watsewa ko wace ta kama gabanta inno ta fito yace “Biyo ni akwae zance inno…!
Bukkar shi ta bishi sai da suka zauna sannan yace “Yanzu Hakimi ya turo aka d’aukeni, Inno yazo min da wani gatsaren labari mai shegen firgitarwa …!
Dafe k’irji tayi had’e da fiddo da idanu tace “Me kuma ya faru Ard’o?Hala dai daga Hafsatu K’arama da mijinta ne?
“Ina fa wai Hafsuwalleta yake neman ya amra…” ya fad’a kai tsaye yana k’walalo idanuwa waje.
A Zabure tace “Kace me?Hakimi ke bid’ar amren Hafsuwalleta?Allah da gaske ko da wasa Ard’o?
“Aradun Allah da gaske yake Inno…!” Ya fad’a kai tsaye,
Kunya ce ta hanata rafka gud’a sai dai ta maida kanta k’asa tana fad’in “Allahu mai yarda yaso!kasan farkon rayuwarka amma baka san tsakiyarta da karshen ta ba…Allah ya sanya alkhairin shi lallai Hafsatu K’arama Haske ce garemu baki d’aya sanadinta komai ya canza.”
Ard’o ya samu Hafsuwalle da maganar tare da bata shawarwarin ta k’arbi zancen da kyakykyawar addu’a kada rashin Lado ya hanata auren wani, sosai ta karb’i shawararshi tare da amincewa da neman zabin Allah……
Ba’a d’auki lokaci ba aka saka ranar d’aurin aure da tarewa sam K’arama bata san da zancen ba saboda lokacin Ma’aruf yana k’asar waje sae dae shi ya sani a waya aka sanar mai……
【】
K’arama kam tun da suka tafi Madre ta d’auko wata ‘yar tsohuwa ta zauna tana taimaka mata, sosae take kula da Udutti don da Amir aka tafi… Hankalinta ya kwanta fatar jikinta ta nuna tsantsar hutun da take samu ga wani kyau na musamman da ta k’ara mai sanyaya rai…
Cikar kyau ta wanzu sosai a tare da ita ta juye izuwa fulanin usul sak mahaifinta Lado hatta gashin idonta gazar-gazar irin na Lado ne tare da girarta bakinta…Banbancinta da Lado bai wuce biyu ba ta fishi karan hanci da kuma sharp d’in idanun su wanda nata yake sexy eyes kamar na mage yayin dashi yake da rowbll…,
Kullum Ma’aruf zai kirata sau uku a rana da safe da rana sae da daddare sosai yake nuna mata soyayya duk da basa kusa amma shakuwa ta k’ara wanzuwa a tsakanin su duk wata kunya K’arama ta ajeta gefe soyayya suke murzawa kamar ba gobe babu wata kalma da zai fad’a mata ba tare da ta samo amsarta ba ta bashi ko dan bata ganin kwayar idonshi oho…! Dan Sai su fi awa biyu suna waya sai sun gama sannan zata bawa udutti su gaisa itama…
Sumayya kam akan magunguna suka d’aurata saboda cancer bata yi karfin da za’a mata Radiation therapy ko Chemotherapy treatment ba, sannan sun fad’a mata da kyar idan zata kuma haihuwa sosau ta shiga tashin hankali yayin da ta saka shi a gaba tana kuka tausayinta ya kamashi ya lallashe ta tare da bata baki har ya samu tayi shiru, k’yak’yk’yawan kashedi suka mata akan ta kiyayi abubuwan da take amfani dasu don da tayi k’arfi wallahi wahalar magani gareta don duk treatment d’in da za’a bata warkewa don zata yi spreading a pelvic d’inta sannan ta cigaba da spreading to other part na jikinta wanda ko an anyi treatment ta warke bayan wani lokaci kad’an za’a sake ganin ta b’ullo wani b’angare kuma a haka za’ayi ta wahala karshe sai dai a hakura har Allah yayi nashi hukuncin akai……
Babban abunda dake janyo mana vaginal cancer wanke farji da sabulu ko wane irine kowa hatta virgin soap da muke ganin danshi akayishi to duk cuta ce, sannan yawan cushe cushe a al’aurar mu ko hayaki na itacen da bamusan daga inda suke ba wani ma ganye kawae zai samu ya debo yayi had’e had’enshi ya kawo maki ke kuma ki saya kina washe baki ke zaki burge miji!Je ki burge mijin yar ‘uwa zuwa lokaci mijij zai burke ki……!A Yanzu mata mun dauki Almiski mun bashi wani matsayi na babba a rayuwarmu muna ganin yana matsemu ko?tabbas zai matseki amma bayan ya dauke damshi da ni’imar da Allah ya baki!ki k’watanta zuba ruwa a cikin auduga zatayi taushi da dad’in tab’awa ki tsira tsinke a ciki zai wuce cikin dadin da kwanciyar hankalu sannan ki zuk’e ruwan ki matsewa zata matse ta dunkule guri daya sam bata zatayi dadin tabawa ba bare ma tsinki ya shiga …haka al’aurarki take da zaran kin zuba miski zaya zuk’e damshinki sannan ki matse kamar yarda kike so amma babu sauran ni’ima da ta rage maki ……Almiski da muke amfani dashi wallahi tallahi yana da mugun illa garemu mata yakan daukewa mace danshinta gaba daya ya rabata da ni’imarta mun ga matan da hakan ta faru dasu sosae !bawae an hanaki amfani dashi bane aa ana amfani dashi duk bayan daukewar al’adarki don ya kawar maki da karnin jini kamar yarda NANA AISHA RD tayi amfani dashi kuma itama ba can cikin al’aurarta ta saka ba a’a waje waje take sakawa!Sannan ku lura da kyau kun gane Almiskin da muke amfani dashi yanzu wallahi ba pure bane an riga an mashi hadi anyi ha’inci a cikinshi wani salon ma da aka zo mana dashi wai har da sabulun Miski ake sayar mana mu dinga tsarki dashi anan zaki lura kamar yarda syka hada sabulun haka suka hada miskin da suka sayar maki !Akwae matan da duk lokacin da miji zai rabesu sae sun saka miski a jikinsu me kenan?…Yar ‘uwa kada gurin neman gira ki rasa ido wallahi duk yarda namiji ya kai ga sonki da kin rasa wannan gurin kin tashi aiki!Karki je gurin faranta mashi ki kwari kanki ki nakasa kanki ki zalunci kanki Karshe kina gani ki zama wulakantatta ya auro wata ya barki da raino idan ma ya maki adalci bai turaki gida ba…
Me zai hana ki saki kayan mata ki mata ya’yan itatuwa?Me zai hana ki bar wanke farjinki da sabulan mata ki zauna a ruwan dumi?Me zai hana ki kiyayi cushe cushe domin inganta lafiyarki ?Me zai hana ki rike Allah da biyayya domin dorewa zaman lafiya?Me yasa su maza basa shan kayan da zasu kara ni’ima?ko basa so su burge matayensu?koko sanin ciwon kansu sukayi?sae ke yar’uwa ?duba da kyau kiyiwa kanki karatun ta natsu!komai da lafiya a ke komai in babu lafiya shagarle……
Cikin d’an lokaci Sumayya ta samu sauki ta warke ras!sosai Ma’aruf yake kula da ita sannan ya kan bata lokacinta dai-dai gwargwado yakan guji yin waya da K’arama a gabanta duk lokacin da zai kira K’arama sai ya fita harabar Hotel d’in da suke ya samu k’eb’ab’b’en guri sannan ya kirata… Ana gobe zasu dawo Nigeria bayan sun dawo daga sayayyar kayan tsaraba mai taxi ya taya su shigar da kayan su ciki sannan yayi hanyar fita yana latsa wayar shi kallo Sumayya ta bishi dashi tare da tab’e baki tana hararan shi, juyowa yayi suka had’a ido ya sakar mata murmushi yana fad’in “Wannan hararar na meye my dear?
Tab’e baki tayi still tana hararanshi sannan tace “Ka je kayi abunda ke gabanka, bana son burin kunya ni.”
Dariya ya saki mai sauti yace “Me ye na borin kunya Sumayya!matata fa zan kira shine borin kunyar?!”
Tsaki ta saki taci gaba da jera kayan su a jaka dawowa d’akin yayi yana dariya ya zauna yana fad’in “Toh Na ma fasa.”