ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Banza tayi mishi ya cigaba da janta da hira ganin ba kulashi zata yi ba ya sashi mikewa yana fad’in “Tunda kin min banza bara nayi abunda zai fi min.”
Kai tsaye tace “Kai dai ka sani…!
Fita yayi yana kiran K’arama ringing d’aya ta d’auka tare da shagwab’e murya tace “kaiii Bunkul sai yanzu ka tuna dani ko?
Murmushi yayi kamar tana ganin shi yace “Waya fad’a maki Hafsatu?kina a cikin raina…”
Dariya tayi mai sauti tace “Da gaske Uncle ?Ina Aunty Sumayya da Amir?
Windown su ya kalla sannan yace “Tana d’aki tana shirya mana kaya…”
K’arama ta shagwab’e murya tace “Gaskia kaje ka taya ta na yafe maka wayar yau tunda gobe zaku dawo…!
Cikin salon shi shima yace “Me kika tanadarwa dawowa ta Hafsatu?
Cike da kunya tace “Komai ma Uncle Ni dai kaje ka taya Aunty had’a kayan.” ta k’arashe maganar cikin sigar jan hankali.
Ido ya waro yace “Ba fa wani aiki bane Hafsatu……”
A Hankali tace “Duk da haka Uncle kaje…”
Lumshe ido yayi tare da kissing d’in wayar a hankali yace “Okk Bye-bye.” Shiru suka yi babu wanda ya katse wayar sai itama da ta rungumeta a kirjinta tsawon mintina sannan ta kashe ya koma dakin su a zaune ya iske Sumayya ta rafka uban tagumi ya zauna tare da janyota jikin shi yana rad’a mata kalamaj masu kwantar da zuciya ga mai jinsu…,
Murmushi ta masa yace “Sumayya kin San Allah Hafsatu bata d’aukeki a matsayin da ke kika dauketa ba, wallahi tana sonki da zuciya d’aya ki bar ganin laifinta ki tsaya kiyi tunani da kyau ita kanta lokacin da na aureta bata san menene duniyar ba kuma nima ban aureta da wata manufa ba na aureta ne saboda yanayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki.” Sosae ya mata nasiha cikin kwantar da murya har taji ta kuna fahimce shi……
Lumshe ido tayi tana lalubar bakin shi yayin da ta fara tsotsa cike da yinwarsu tabbas tayi missing komai nashi cikin k’ankanin lokaci suka lula wata duniya mai wuyar fassara…
Sae da ya tabbatar da ya wanke laifin shi sannan a hankali ya janyo wayashi cikin dabara ya turawa K’arama goodnight text yana murmushi tare da makaleta cikin jikinshi.
【】
Tunda ta tashi da Asuba ta shirya Udutti ta tafi makaranta ta shiga kitchen ta fito da kaza daga fridge ta aje ta huce sannan ta fito da hanta da kayan miyan da tasa Bala ya siyo mata masu kyau jawur dasu jiya duk da suna da markad’add’u a cikin frigde, wankesu tayi ta yanka slice sannan tayi grinding attarugu da albasa da garlic ta aje gefe guda, Man gyad’a ta d’aura saman fryingpan da wuta k’asa k’asa ta wanke kazar ta yankata ta bad’eta da curry da thyme da spices kala kala kafin ta juyeta cikin man ta zuba albasa da attarugun da garlic da tayi grinding a sama ta rufe frying fan din ta rage wutar sosai…
Tukunya ta kuma d’aurawa ta juye kayan miyan da ta yanka tare da ruwa kad’an ta rufe Sannan ta fera doya ta d’aura a saman wata tukunyar da sugar kad’an a ciki…
Kwakwata ta samu ta gurje bayan duk bakin ya fita sannan ta gurzata kanana kanana ta aje a fridge, Ganin kayan miyan sun dahu ya saka tasa abun kad’a kwai ta murje kayan miyar har sai da suka burgu sannan ta cire zare zaren kayan miyar tare da zuba mangyad’a da spices ta rufe, Cabbage ta yanka da carrot da hanta ta zuba a cikin kayan miyan har sae da ruwansu ya shanye sannan ta bude ta cigaba da motsawa a hankali sannan ta koma ta sauke doyar ta aje gefe……
Kazar ta bud’e ta iske ta dahu sosai cikin man har ta fara soyuwa yayin da tayi kore shar tayi kyau kayan miyan duk sun like a jikinta cigaba tayi da soyata sama sama sannan ta kwashe ta juye a warmer ta kai dinning…
Gurin miyar ta koma ta iske ta d’an soyu ta fasa kwae ta zuba akai taciga da juyawa a hankali har kwan ya murje yayi fari-fari sannan miyar ta washe tayi kyau, curry ta kuma zubawa ta k’ara spices sanna ta rufeta tayi k’asa da wutar sosai yadda ba zai kama ba…
Maimakon ta saka ponded engine sai ta d’auko turmi ta wanke sannan ta saka doyar ta cigaba da dakawa har ta daku tayi laushi da santsi sannan ta dauko madara peak ta zuba akai ta cigaba da dakawa!sae da ta tabbatar da sakwararta tayi lafiya lau sannan ta kwashe ta mulmula a leda ta saka a warmer ta rufe sannan ta d’aura k’wak’warta(Coconut)bisa wuta ta zuba ruwa kad’an Sae da ta dahu tana kumfa fara sannan ta sauke ta zuba peak biyu da sugary kad’an ta juye a jug ba tare da ta tace dussar ba ta saka a fridge, Zuwa lokacin miyar ta soyu don haka ta kwasheta ta kai ta ajiye…
Tsohuwar dake zaune da ita ta tayata gyara falon ta goge sannan ta gyara mata kitchen…
‘Dakin Ma’aruf ta koma ta gyarashi sosai ta saka turaren kamshi da freshner sannan ta koma d’akin Sumayya itama ta gyara mata kafin ta shiga d”akinta ta fad’a wanka ganin har karfe 12:30pm Kuma yace mata biyu zasu iso…Simple Make up tayi cikin lace sky blue da ya mata masifar kyau d’inkin riga da siket ya fito mata da sharp d’inta sosau. Tana sallah taji tsayuwar motarsu wani dad’i da fad’uwar gaba ya ziyarce ta lokaci guda, A hankali ta matsa jikin window ta d’age labule tana lekensu…
Ma’aruf ta hango Yana d’auke da Amir cikin kayan Pakistan na maza sosae kayan suka mashi kyau bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ta saki labulen ta jingina tare da dafe kirjinta. Shigowar su falo ya sata fita da hijab d’in a jikinta Sumayya ta fara shigowa da gudu ta rungumeta tana murna, Ita kanta Sumayya sai ta samu kanta da zagaye K’arama da hannunta tana murmushi!Turus Ma’aruf yayi ganinsu a haka kuma ba karamin burgeshi suka yi ba kusa dasu ya matsa ya rungumo sumayya ta baya tare da K’aramar baki d’aya K’arama ta fara janye jikinta sannan ta dukar da kai tace “Aunty Sannu da zuwa…”!
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE B’OYE……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S.Precious HAJJA CE????
*SADAUKARWA……*
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *90*
*【End】*
'Dan murmushi Sumayyar tayi tana k'ok'arin danne wani bak'in abu da takeji yana taso mata tun daga k'asan zuciyarta tace,
“Yauwa.” sannan tayi cikin Falo ta fad’a saman kujera tare da dafe kai tana rintsa isanuwa, K’arama kuwa Sam bata kalli inda Ma’aruf yake ba ta d’auki Amir ta koma kusa da Sumayyan ta zauna tana murmushi sannan tace,
“Aunty Ina wuni, Ya hanya?Ya kuma jikin?!”
A Hankali tace “Alhamdulillah…”
Shiru Suka yi yayin da Ma’aruf ya shige part d’inshi yana harararsu cike da jin dad’i yace,
“Ni baza ai min sannu da zuwa ba ko?”
Tab’e baki Sumayya tayi don tasan ba da ita yake ba sannan ta mike ta shige dakinta, K’arama kam mikewa tayi ta nufi part d’in Ma’aruf ko zata taimaka mashi da wani abu… Ganin shi jingine jikin window ya sa jikinta yayi sanyi sai take ganin kamar rashin maganarta ya sashi jin ba dad’i ita kuma har ga Allah saboda ganin Aunty Sumayya yasa bata nuna mishii jin dad’in dawowar shi muraran ba kuma tana ganin MIJINKA SIRRINKA ne ba gaban kowa ya kamata ka masa wasu abubuwa ba.
A Hankali ta tako ta tsaya a bayan shi tare da k’iran sunan shi a hankali cikin muryar da bata san tana da ita ba tace “Uncle…”
Har cikin magudanar rashin yaji maganarta saboda komai nata daban ne amma yayi mata banza don yana bukatar ta sake k’iran sunan shi cikin sigar da tayi a yanzu…
Cikin sanyin Murya ta kuma cewa “Uncle good afternoon, Ya hanya?” Ganin yak’i juyowa yasa ta shagwab’e murya kamar zata yi kuka tace “Uncle nayi laifine daga dawowar kuwa wayyo ni hafsat?