ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar me rad’a ya juyo yace “Haka akewa miji idan ya dawo daga tafiya Hafsatu?

Ware hannu tayi ta rufe fuskarta ganin irin kallon da yake watsa mata tana murmushi… Sosai ya matso kusa da ita ya tallabo kanta yana kallonta har numfashin su na had’uwa a hankali ya kai lips d’inshi kan wuyanta yana fad’in,

“Kin manta kin ce kin tanadarmin abubuwa na musamman?!”

Ya saketa tare da yin baya ya ware hannayenshi yana jefa mata wani kallo na musamman alamar tazo gareshi… Cikin natsuwa ta shige jikin shi ya mayar da hannuwan ya rufe yana mayar da Numfashi itama zagaye waist d’inshi tayi da hannunta ta d’aga kai ido a lumshe…

Bisa lips d’inta ya d”aura hancinshi yana kallon eyelashes d’inta da suka yi gazar-gazar… A Hankali ya matsa ya zauna bakin gado dasu yayin da ta ware ta mashi oyoyo mai shiga rai sannan ta mike ta had’a mashi ruwan wanka da suka ji kayan kamshi ta dawo ta cire mishi takalma tare da d’aga hannunshi ta cire mashi rigarshi ya zama daga shi sai vest ta juya da sauri zata fita.

Janyota yayi ya zaunar da ita bisa cinyar shi yace “Ina zaki gudu baki k’arasa aikin ba ai…!

Rufe fuskarta tayi da hannu tace “Na gama mana…”

Lakuce mata hanci yayi tare da kama hannunta ya d’aura saman trouser d’inshi yace “Kin tabbatar kin gama hafsatu?

Murmushi tayi tana sake rufe fuskarta da hannu a hannun ya sakar mata kiss yace “Hafsatu Kunya!karki damu ki bani zuwa nan da gobe zan cire maki wadda ta rage maki…”

Mikewa tayi da gudu ta fita daga d’akin ta shige d’akin ta, ta dad’e zaune gefen gado tana murmushi sannan ta mike ta shiga d’akin Sumayya tama Amir wanka dake ta ihu zafi ya dameshi sannan suka fito da Sumayya suka zauna a dinning…

A Hankali Sumayya tace “Ki shiga ki kira Ya Ma’aruf K’arama.” Duk da taji ta sai tayi shiru kamar bata ji ba sai da ta k’ara maimaita mata sannan ta mike a sanyaye ta shiga d’akin shi shima daga bakin kofa ta tsaya tace “Uncle ka fito kaci abinci..”

Yana combing kanshi ya kalleta ta mirrow ya d’age mata gira ta juya da sauri ta koma tana fad’in “Aunty Gashi nan zuwa…!

“Huh.” kawai tace tana kokarin bud’e warmers amma K’arama tayi saurin karb’a ta bud’e mata cike da ladabi…

Waro ido Sumayyan tayi cike da farin ciki don favourable food d’inta ce Sakwara ta kalli K’arama d”auke da murmushi tace “Thank you Hafsat kin san ina son sakwara kenan?!”

Ma’aruf ya zauna yana fad’in “Shi yasa ta maki ai.” ya juyar da kai yana hararan K’arama yace “Banbanci ko?ni ina nawa Favourable food d’in…?!”

Rufe fuskarta tayi tana murmushi mai tsayawa a rai Sumayya ta janyo hannun K’arama tana hararan shi tace “Kayi hakuri ka ci nawa idan kuma bai maka ba Hafsat shiga ki had’o masa tea da bread…!

B’ata fuska yayi yana harararta yace “Son kai ko..?

Murmushi suka yi baki d’aya sannan tayi serving nasu kowa da plate d’inshi Sumayya ta tura masu nata a tsakiya tana fad’in “We are one family bai kamata muna raba plate ba yanzu.”

Su duka suka kalleta cike da farin ciki barama Ma’aruf da ya janyo hannunta yayi kissing cike da jin dad’i… A Tare suka yi lunch d’in cike da jin dad’i sai da ta janyo coconut drink sannan Ma’aruf ya ma Sumayya gwalo yana fad’in “She made me complete tunda tamun abunda nafi so a drink.”

Dariya suka d’auka baki d’aya sannan suka koma falo suka cigaba da firansu cike da jin dad’i!Shigowar Udutti yasa firan ya sake rud’ewa ta ishesu da tambaya da ihu har da tambayar K’arama “Aunty naga kina wa Mommah dariya ta baki fuskarta ne ki rama mari da dukan da ta maki ko kin yafe mata…?!”

Murmushin yake Sumayya tayi cike da nadamar abunda tayi zata yi magana K’arama tace “Waya fad’a maki duka na tayi?wasa muke yi fa ranar…!

Tab’e baki Udutti tayi tana kallon Ma’aruf tace “Papa ni za’a maida sakarai ko?bayan har da jini a fuskar Aunty mai kyau ranan Momma kice mata tayi hakuri…”

K’arama ta jata ta shige da ita d’aki don ta gaji da surutunta itama Sumayya bayan su tabi ta zauna a sanyaye tana bata hakuri akan abinda ya faru a baya…

Waro Ido K’arama tayi tace “Dan Allah Aunty ki daina bani Hakuri wallahi ban d’auki komai ba kuma na yafe maki da zuciya d’aya…!


Daddare bayan sun gama dinner Sumayya ta ja Ma’aruf har d’akin K’arama suka zauna anan ta nemi su yafe mata su duka sannan ta k’ara da fad’in ta basu sati biyu domin K’arama ta mori mijinta itama, sosai Ma’aruf d’in yaji dad’i ya rungume su baki, d’aya tare da k’warara masu albarka baki d’ayan su sannan Sumayya ta mike ta barsu su kad’ai tana kokarin danne kukan dake niyar kwace mata…… Tana fita shi kuwa janyo K’arama yayi jikin shi yana rad’a mata kalamai masu dad’i da sanya natsuwa sam kasa bari yayi suyi wanka saboda yayi missing d’inta fiye da yadda bata tunani sannan ya kashe lamp tare da rufesu da bargo…

Duniyar Ma’aurata suka lula mai cike da kwanciyar hankali, wannan karan ma cikin natsuwa ya tafiyar da ita har suka samu gamsuwa su duka biyun kafin bacci yayi awon gaba dasu manne da juna cike da kwanciyar hankali.

Zama suke cikin jin dad’i tare da kwanciyar hankali Sosai suka had’e kansu yayin da Sumayya taja K’arama jikinta itama kanta K’arama tana k’okarin kyautatawa Sumayya sannan takan guji duk abunda zai bata mata rai a zaman su… Wani abun burgewa ma dasu idan suna zaune baka gane wacce ke da girki a cikin su suna respecting junansu ko kad’an basa shishshigewa miji a gaban juna duk wani abunda zaki wa miji sai kun shiga d’aki daga ke sai shi sannan ki nuna masa soyayya…

Sam Sumayya ta gyaru ta daina shan komai sai dai idan sun tashi su markad’a ganyen zogale su zuba peak su sha a tare ko kuma su markad’a kankana da peak su sha a tare don gani suke duk abunda za suyi mijinsu za suyi mawa sannan idan har suka yi sake baya samun gamsuwa gurin d’aya daga cikinsu to wata na iya shigo masu. Sam ta rage son jiki takan zage ranar girkinta suyi abinci mai rai da lafiya tunda dama ba rashin iyawa bane tsabar lalaci ne komai a tare suke sannan yaran Sister Maryam suka zo masu yawo haka suma akan kai su Udutti gidan… Har numbern beeba Sumayyq ta goge daga wayarta don bata bukatar sake had’uwa da ita…

Cikin lokacin ne ya d”aukesu su duka ya kaisu katsina Gidan hakimi acan K’arama tayi mutuwar zaune ganin Ummanta zaune a matsayin matar hakimi bakin ta yaki rufuwa murna sosai tayi bama kamar yadda taga hankalin Umman nata ya kwanta ita kanta Umma taji dad’in ganin su yayin da tayi ta nan nan da Sumayya da Udutti da Amir don baza ma ka tab’a tunanin K’arama ce d’iyar ta ba……,

Kwanansu biyu a gidan sannan ya d’auke su ya kaisu kauyen su Lauratu nan ma tayi mamakin canzawar kauyen sai da lauratu ta fad’a mata cewa Ma’aruf ya saka hannu aka canza masu komai, sosai ta jinjina mashi tare da bashi matsayi na musamman azuciyar ta kwannansu d’aya suka je suka gaido da Maitafasa itama ta nuna masu gata sosai kaya sosai suka jide masu sannan suka juya zuwa gida Maitafasa ta kalli Kundum tace…

“Tun randa kika tona ABIN DAKE B’OYE nike ta ganin alheri, haushi na d’aya da baki fad’a ba har ladona ya rasu da yanzu dashi za’a ci wanga arziki amma ba komai rayuwa ce.”

Duk jikin Kundum yayi sanyi hakan yasa ta kasa cewa komai sai sharar kwalla da takeyi da bayan zani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button