ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL


Idan ka gansu bazaka tab’a tunanin kishiyoyi bane zaman su gwanin ban sha’awa sukan fitar da lokaci suyi wasa kamar volleyball da lido, table tennis da golf idan su Udutti sun tafi school Ya Ma’aruf kuma ya fita aiki sai suyi tayi.


After one year

Bayan shekara d’aya K’arama ta haihu ‘ya’yanta ‘yan biyu sak mahaifin su, mace da namiji ne sam haihuwar bata bata matsala ba saboda a gida ta haihu tare da taimakon Sumayya shagali sosai aka yi don har su Maitafasa da kundum da ‘yan gidan Ard’o sai da Ma’aruf ya saka aka d’auko su ranar suna yara suka ci sunan macen aka saka mata AMINATU yayin da Namijin kuma AMMAR wanda Sumayya ce ta zab’i sunan da kanta…

Rainon yaran ya koma hannun Sumayya baki d’aya tana masifar nuna masu gata kamar yarda K’arama ta nunawa su Udutti. Da farko Sumayya ta d’an fara nuna alamun damuwa akan rashin haihuwar ta ganin K’arama ta haifi nata kuma sun mugun bata sha’awa amma da taimakon K’arama Sumayya ta washe ta fauwalawa Allah ta cigaba da addu’o’i… A lokacin Ma’aruf ya mayar da K’arama makaranta inda taci gaba da karatunta hankali kwance…

Ba tare da sanin K’arama ba Ma’aruf ya samarwa Sallau Mijin Lauratu aiki a wani company dake buga robobi shi da kanshi ya sayar masu d’an matsakaicin gida ya zuba masu kaya dai-dai gwargwado sannan ya samu mota ake je a d’auko su suka dawo cikin gari…Ranar da ya kai K’arama gidan ta ga Lauratu har kuka tayi saboda murna yayin da ta rasa bakin da zata gode mishi dan yayi mata komai a rayuwar ta. Ganin taki barin kukan har lokacin da suka baro gidan yasa yayi parking gefen titi ya kashe motar tare da b’ata rai yace “Zan fita idan kin gama kukan ki kirani sai mu wuce.”

Wata irin runguma ta mishi tana girgiza kai yayin da bakinta ya rasa kalmar da zai furta. A Hankali ya d’ago kanta yana kallonta sannan ya saka babban d’an yatsan shi ya goge mata hawayen tare da sakar mata lallau san murmushi yace “Na san me kike son Fad’a bara na fad’ar maki kiji.” Gyara murya yayi yana kwaikwayon Muryarta ta yarinta yace “Bunkul ta k’warank’wata aradun Allah nagode maka na kuma gode maka gobe zaka k’ara man k’ankayar nonon shanu mai zak’i (Ice cream).”

Dariya ta saki tare da kai mashi dukan wasa tana hararan shi tace “Ni ba haka zance ba fa.” Ta kwantar da murya tace “Uncle wallahi ban…”

Hannun ya d’aura saman lips d’inta yana jefa mata harara yace “Indai kin san ba abunda na fad’a zaki ce ba to kiyi man shiru zaki fi birgeni idan kika kuma haihuwa man wasu twins d’in nan da wata Bakwai…” Ya k’arashe maganar tare da ja mata hanci…

Jikin shi ta shige tana sunne kai tare da dariya k’asa-k’asa daga haka kukan ya kare yaja motar shi suka koma gida cike da farin ciki…

TWO YEARS

Shagwab’e Fuska tayi tana kallon Sumayya tare da d’aura mata Ammar a cinya tana fad’in “Kinga ko Aunty wallahi yaron nan ya fiye rigima.”

Harara ta sakar mata tana murmushi tace “Ai dama bance ki d’aukar man yaro ba bare ki zo kina bani labarin rigimarsa.”

Udutti ta shigo hannunta d’auke da Aminatu ta fad’a saman kujera tana turo baki K’arama ta matsa tana tambayarta “Menene my Udut?

B’ata Fuska tayi tace “Aunty fitsari ta man a jiki kuma fa yanzu nasa kayan…!”

Harara Sumayya ta watsa mata tana fad’in “Kuji kinbabbiya ke bakya fitsarin ne an gaya miki?common bani d’iya ta nan…!

Ma’aruf dake tsaye bakin kofa ya saki murmushi mai sauti wanda ya janyo hankalin su… rige-rige ake tare da shigewa jikin shi K’arama da Udutii suka fara fad’awa yayin da yayi masu kyakyawan masauk’i kafin Sumayya ta k’araso da su Aminatu a hannunta tana dariya tana fad’in “Yau mun yadda an rigamu amma Allah ya kaimu gobe.” sannan itama ta fad’a jikin su suka d’auki “Oyoyo gaki d’aya!

Kissing yama ko wace a forehead harda su Aminatu sannan K’arama ta k’arbi briefcast d’in hannun shi da yake ita ce da girki ta shige part d’in shi…

Suna shiga ta sake masa oyoyo d’in shi na musamma mai shiga rai tana zagaye da waist d’in shi ya d’ago kanta ya had’e goshin su yana kallon cikin idonta a hankali yace “Kin kawo min haske a rayuwar gidana Hafsatu Allah ya maki albarka…”

A Hankali tace “Kaine silar komai Uncle ban…” Cakulkuli ya mata tayi shiru tana dariya yayin da yayi sama da ita ya direta saman gado sannan ya zauna saman cinyarta yana shinshina wuyanta cikin sanyin murya tace…

“Uncle please…, yayi saurin zura harshanshi cikin bakinta wanda lips d’in yasha red d’in janbaki, a hankali ya zare bayan ya d’ora hannunshi d’aya saman na shanunta yace cikin muryar rad’a,

“Nace bana son wannan Uncle d’in da kike cemin, please karki ja ki haramta min kanki ki canza min suna now.”

Kamar zata shid’e sabida abunda yake mata, da kyar tana wani irin nishi tace,

“You you’re my everything my first and last love, you’re the father of my children you’re the angel from about who takes my pain my love for you is so strong it always just the same, I love you my sweetie pie and I need you right now…”

Tana gama fad’a ya zura bakin shi cikin nata ya fara tsotsa Yaya hajja baki bud’e sai da Feedohm ta tunrsire da dariya sanna tasa hannuta ta rufe idanuwanta sannan ne ta ankara ashe sun gama Feedohm ta ja hannunta suka fito suna dariya….

Alhamdulillah
Muna godiya da Allah da ya nuna mana karshen wannan littafin lafiya ABIN DAKE B’OYE. Kuskuren dake ciki Allah Ubangiji ya yafe mana baki d’aya

Wannan page d’in sadaukarwa ne ga duk wanda ke bibiyar wannan littafin tunda farko har karshensa Mungode sosai Allah ya bar kauna #HajjaFeedohm suna kaunarku sosai da sosai????

Gaisuwa ga duk ‘yan WATTPAD sis Rufaida Omar maitafasa na gaisuwa tace kwarankwatsa tana yinki, ‘yan Haske fan’s kuma bamu manta kuba Allah yabar so da kauna????

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button