ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Juyawa yayi a fusace yana kallon Hafsuwalle “Kinji Kunya Hafsatu kin saka an wulakantani a inda ba’a isa ba, tur dake!
Kuka ta saki da karfi tana girgiza mashi kai “Ka Gafarceni Ard’o Wallahi ban aikata abunda suke zargi ba”
“Tur Dake Hafsatu!Me yasa lokacin da Ladon ya nemeki baki nuna mashi aibun da abun zai haifar ba kin biye mashi kin saka an wulakanta mu !kin haifar mana da abun kunya a zuri’armu wa zai yarda d’iyar Lado ce ……!
Kundum tace “Can ta matse maku munafukai Sae a k’ara gaba Don Mai tafasa ba sakarai bace da zata karbi Shege!
“Bana son fa munafunci Kundum idan ina tsiyata ki daina saka man wagegen bakinki……!Mai tafasa ta fada tana watsa hannu gaba sannan ta shige gidan tana fadin “Wani kukan ma Sai ranar da Ladona ya warke……”
HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Assalamu alaikum masoya masu bibiyar ABINDA KE B’OYE..! fatan alkairi gare ku tare da d’inbin godiya, hakika muna jin dad’in yadda kuke bibiyar labarin tare da ganin d’inbin comment d’inku mungode Hajjafeedohm suna sonku baki d’aya????
_Ina kike *AMAL BAII..?* wannan shafin nakine danjin dad'inki ke kad'ai, mun gode da soyayya we love you muma sosai-sosai_????????????
Page *17-18*
Juyawa suka yi Hafsatun na kuka suka tafi ……Sauran mutanen garin suka bisu da ihu tare da zagi har suka bar garin ……
Koda suka koma Gida Ard’o duka mutanen gidan ya tara tsakar gida a fusace yace “Ni kam dae na yafe Hafsatu cikin yarana don haifi yarinyar da zata saka a wulakanta ni ba……”
Kuka Hafsatun take kamar ranta zai fita yayin da ta duk’a saman guiwarta tana bashi hakuri amma sam yak’i kulata ya juya zai tafi ……Inno ta kasa jurewa ta tareshi a sanyaye tana fadin “Ard’o ka saurareta dan girman Allah!ka gwada wanga jaririya ka gane ta halak ce mai yasa zamu k’ita?
“Saboda iyayenta yarinyar basu karbeta kuma nima na kasa gasgata Hafsatu akan Hafsatu yau aka wulakanta ni a ci man zarafi taya zan karbi Hafsatu?Ban hana Hafsatu rayuwa a gidana ba amma ko k’wayar hatsi ban yarje a bata ba……” Yana gama fadar haka ya juya ya bar gidan
【】
Bayan Sati biyu Ma’aruf ya bayar da Magunguna aka kawo ma Malan Ladon kafin su gama bincikensu a kanshi sannan ya koma gida ……
…
Tarba ya samu sosae gurin Madre da Abba……Sumayya kam sai iyayi take amma ya nuna bai san tanayi ba ……
Sae da ya huta sannan ya kalli Madre yana bata fuska yace “Madre karatu zan koma wallahi wannan aikin duk karyace an rigaya anyi eradicating cutar a nigeria hakanan muke wa mutane karya……”
Hararanshi tayi tace “Bana son haka Ma’aruf aikin naka kake karyata?
Langwabe kai yayi yace “Madre gaskia na fada ni karatu zan koma”
“Kace karatu zaka koma Ma’aruf Simple!
Lumshe ido yayi yace “Eh Madre
Murmushi tayi tana girgiza kai sannan ta janyo wani littafi ta mika mashi tana fadin “Ka duba wannan littafin akwae addu’o’i da yawa a ciki sannan yau kayi istihara ka nemi zabin Allah akan karatun ko barinshi Kafin na Fada Abbanka ……”
“Thank you Madre……”ya fada yana murmushi
Daga haka suka cigaba da firansu……
Bayan yayi istihara ya fadawa Madre din cewa yana tunanin Karatun nashi alkhairine Ita da kanta ta fadawa Abbanshi……Abunka da masu kudi cikin kankanin lokaci aka shirya tafiyarshi kasar India ……Kuka kam Sumayya tasha shi kamar zata mutu……
【】
Su Hafsuwalle rayu suka fara yau da dad’i gobe ba dad’i Har Hafsat K’arama ta fara wayau dukan gidan daga Lauratu Sae Umma ke daukarta tun tana ganin mutanen gidan tana mika masu hannu alamun su dauketa har ta daina sae dae idan Lauratu na aiki ta rarrafa kusa da katuwar bishiyar kukar dake gaban gidansu ta zauna anan zatayi wasanta ita kadae har sae lokacin da Lauratun ko Umman suka gama aikinsu sannan su dauketa su shigar da ita gida ……Wani Sa’in har a gama Magrib tana zaune gurin sannan ko zatayi kukan duniya babu wanda zai kulata daga iyalen gida bare ya dauketa ……Gashi Allah ya zuba mata wani irin kyau kamar ita tayi kanta da farin jini ga mutanen waje amma na gidansu basu kaunarta……
Lokaci na kara ja Har Hafsa karama tayi shekara hudu da haihuwa lokacin ta fara magana sossae sae dae bata cika surutu ba idan kaji tana magana to da Lauratu takeyi……bata kula ko wane yaro kamar yarda babu mai kulata,Duk wani hidimarta ta ya koma hannun Lauratu abunda ke hadata da Ummanta idan sunzo bacci!amma zata wuni tana wasanta a bakin bishiyar kukar ita kadae saboda duk sun hana yara tsaranta wasa da ita……
Cikin lokacin kankani ta gane wani irin kuka na masifa duk in lokacin Magrib yayi haka zatayi ta ihu tana zambarwa tare da mike mike kamar zata shid’e ……Tun abun baya damu Umman har ya fara damunta yarinya zata wuni tana wasanta amma da Magrib tayi ta gama walwala har sae dare ya take !wani sa’in ma haka za’a wuni ba’a ganta ba Sae gab da mangrib sannan Lauratun Zata ganta zaune kusa da katuwar kukar dake gefen gidan……
Cikin Dan lokacin Sallau yaron kanwar Ard’o ya nuna yana son Lauratu da aure ……Dukkan mutanen gidan kin amincewa sukayi wai kada a goga masu abun kunya……Amma da yake Tsaye yake ya nuna babu wanda ya isa ya hanashi auren Lauratun tunda ba ita ce tayi abun kunyar ba……
Ba dan anso ba aka saka baikon Lauratu da Sallau……Da yake gidan gandu ne anan ya yanki fili ya yi karamin dakinshi ……
Lauratu na Zaune tana wanke kwanunkan da sukayi amfani dasu, Ummansu kuma tana surfa masara……Mutanen gidan kowa na aikin gabanshi masu yada masu magana nayi masu habaici ma nayi amma babu wanda ya kulasu ……
Hafsa karama na zaune bakin bishiya tayi bud’u bud’u da jikinta ko riga babu a jikinta d’iyar kara ta hada tana saka mata kayan leda hankalinta kwance sae murumushi take zubawa kamar tana wasa da mutane……
Jummai ta gifta ta gabanta tare da kwallo da kayan wasanta tana hararanta tace “Shegiyar yarinya ita ba gidan ubanta ba amma ta cika mana gida da tarkacen hauka…… “
Dagowa tayi tana hararanta cikin maganar da bata biye mata baki ba tace “An Dummai Allah ya isa ……”
Finciko ta tayi ta wanka mata mari sannan tace “Shegiya mara kunya ni zaki ma Allah ya isa to k’ara man Allah ya isan ki ga yarda zanyi dake a gidanki”
Dukar da kai tayi tana surutai kasa kasa tare da hararan jummai ta kasan ido, lauratu tayi saurin zuwa gurin ta kamata tana fadin “Me yasa kika mata Allah ya isa K’arama?
Shiru tayi tana kallon katon cikin Jummai sannan tace”Ba abincin amarya bane ta zubar!Kuma sae na fadawa Ayd’o Mijinki ya satar mashi kaza kun dafa a daki kun cinye”
“Eyeh Ni zaki jawa Sharri k’arama”Jummai ta fada tare da fiddo idanu waje sannan ta bar gurin buguzum buguzum tana waigensu kai da gani kasan bata da gaskia……
Da Kallo Lauratu ta bita sannan ta ja hannun Hafsah din suka nufi inda suke aje ruwa tana fadin “Kar na sake jin wannan maganar kinji ko ?sannan waya fada maki Sun Saci Kazar Ard’o K’arama?
Kallon lauratun tayi da idanuwanta da suka rine suka koma jawur dasu wanda har lauratun sae da ta tsorata ta saketa tare da ja baya sannan tace tace “Ni na gani kuma idan karya nayi ki duba cikinta akwae sauran naman da bai narke ba……”
Dafe kirji tayi tare da ja baya tana kallon Hafsa tace “Na Shiga uku ni Lauratu ya za’ayi naga cikin mutun K’arama ?
Shiru ta mata ta debi ruwa tana sha lokaci guda idanuwan suka washe suka koma fararensu tas sannan ta nufi bukkarsu ta bar Lauratun tsaye tana kallonta……
Da Sauri ta nufi gurin Ummansu tana fadin “Umma kin ga Idon K’arama kuwa?