ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A Sanyaye tace “Me ya sameta?
Zatayi magana ta hango Hafsa din tana niyar Fita daga gidan bayanta ta bi tana kwala mata kira amma ko ta juyo…… har sae da ta kai bakin bishiyar da take zama sannan ta zauna ta dauki wani katon Dutse ta daura a cinya tana girgiza kafa tare da murmushi……

Tsaye tayi tana kallonta sannan ta koma gida ta cigaba da aikinta sai dae duk jikinta yayi sanyi ……Sae da suka gama abinci sannan ta je da kanta ta janyota suka shiga bukkar su suka zauna……
Daga kai tayi ta kalli Ummansu Tace “Yaya Lauratu Baffa nake son gani……”

HAJJA CE????
&
FEEDOHM????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
_K.A.S Precious Hajja ce????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu

    Page *19-20*


*D*asauri lauratu ta kalli k'arama tana zaro idanuwa cikin tsananin mamaki ganin dare ne amma take cewa gurin baffa zata, cikin tsoro wanda ya bayyana karara a fuskar lauratu tace cikin sanyi, "K'arama ya zamu je can gwadabniya cikin daran nan tsakani da Allah?"

Baki ta turo cikin shagwa6a, kafin kace me tuni fuskar hafsat k’arama ta sauya tayi saurin kwantawa akan zanin dake shimfid’e a k’asa inda suke kwana tayi shiru tamkar me bacci Umma da lauratu suna ta tashinta amma tayi kamar tana bacci hakan yasa lauratu dubawa taga lallai baccin take sannan ta kalli Umma tace “Umma ‘yar rigimar Mu tayi bacci muma Mu kwanta yadda zamu tashi da wuri muyi sissikar nan.”
Daga kwancen da suke suka yi ‘yar hira kad’an abinka da gajiyayyu tuni bacci ya d’auke su gaba d’aya. Jin saukar numfashin sune yasa Hafsat saurin mikewa sai faman zazzare idanuwa take gashi yadda take yi d’in tamkar wata babba, sim-sim-sim ta fito daga d’akin ba tare da kowa ya ganta tayi kauyan gwadabniya harda ‘yar wakar ta.

Sai da ta fara lekawa d’akin mai-tafasa, ganinta tayi tayi bajebaje akan garu tana bacci baki sake hanci a sama sannan ta juya ta shiga inda lado ke kwance da fitilar kwai a kunne wadda take shirin mutuwa sabida k’arancin kananzir. Kallon fitilar kawai k’arama tayi sai ga haske ya k’aro lado kwance yayi fitsari gurin sai zarni yake babu me gyarawa suka had’a idanu tayi mai murmushi tare da k’arasawa gurinshi tana janyo tuwan da tagani wanda ko alamar ta6awa ba’a yi ba tace.

“Baffa bata baka abinci ba ko?” Ta fad’a tana shirin gutsurowa tare da kaiwa bakin shi yayi saurin bud’ewa sabida dama yinwa yake ji amma babu me bashi, yana ci yana jin kaunar ta na k’ara shigar shi, sai dai yana mamakin yadda yaga duk k’ankantar ta amma shigen surutu da iya sannan yadda zata yi komai, ta dad’e a gidan kafin ta koma gida, sai da ta dad’e a gurin bisjiyar kukan nan kafin ta shi ga ciki har lokacin babu wanda ya farka ta lalla6a tsakiyar su ta kwanta…..,

{{ }}

INDIAN NEW DELHI… All cikin university d’in cike take da al’umma kowa ka gani da abunda yake yi sannan babu ruwan wani da shiga harkar wani a cikin masu fitowa daga cikin wani katafaran hall harda Ma’aruf yafito hannunshi rik’e da brief case kai da ka ganshi kasan yana d’aya daga cikin wad’anda suka kwaso gajiya, tafiya yake a hankali amma shi a hakan mugun sauri yake, sai dai kai da kagan shi zaka ce ko baya san taka k’asa ne. Da d’an gudu budurwar ta k’arasa inda yake tare da sakar mata murmushi, kallonta yayi cikin takaici dayan baya buqatar komai yanzu banda ya kwanta gashi ita kuma zata uzzara mai, cikin tsuke fuska yace.

“Please n please Aisha kinga yanzun na fito daga lecture so ki barni naje na huta karki sa raina ya 6aci.” Ma’aruf ya fad’a yana kallon cikin idanunta, kasa musa mai tayi sabida wani irin kwarjinin shi take ji hakan yasa yan zuma matsawa tayi ya wuce tabi bayan shi da kallo cikin tsananin so da begenshi har ya tari texi ya shiga tana tsaye.

Aisha budurwace kyakyawa gata da kamun kai, ba ‘yar kowa bace hasalima da shocolaship tazo university d’in. Tunda idanuwanta suka dira akan na Ma’aruf taji duk duniya babu wanda take so bayan shi, da ta ganshi zata je inda yake wai ko zai kulata amma ina tayi hakan yafi sau d’ari hakan yasa duk tsananin kunyarta sai da ta tunkare shi akan suyi friendship amma kullum da uzurin da zai kawo mata duk da irin nacin da take mai.

Ma’aruf na komawa hotel d’in da yake brief case nashi ya ajiye kafin ya cire kaya ya shiga bathroom, wanka yayi sannan yayi alwala ya fito, pray mat ya shimfid’a yasan ya jallabiya coffee color ya hau yayi sallan asar, sai da ya idar sannan yayi shafe-shafen shi lokacin aka yi nooking door d’in ya bud’e ya kar6i odern abincin da yayi, dawowa yayi ya zauna a kan pray mat d’in yafara cin abincin tare da kunna t.v yana kallo. Sai da ya kammala komai sannan ya koma kan bed, laptop ya kunna ya fara laluban focal person d’inshi dan yana son yaji karin bayani akan gwajin da suka yiwa lado…..

{{ }}

Yanzu kam baki d’aya al’ammuran hafsat k’arama ya fara bamawa kowa tsoro kasan cewar duk wanda yayi wani abun a gidan sai ta tona mai asiri, har wannan lokacin iyalan gidan nan babu wanda ko da wasa ya ta6a d’aukarta yara sa’aninta da wad’anda aka haifa bayanta duk basa kulata, jin dad’in ta kawai taje jikin bishiyan kuka ta zauna anan zaka ga farin ciki da nisha d’inta.

Zaune take yan zuma jikin kukar hannunta rik’e da wani kara karami sai kallonshi take tana dariya gashi daga ita sai pant yayi dukun-dukun da jirwayen fitsari hancinta duk majina ta bushe, Ard’o ne yazo wucewa da yaron shi a kafad’ar shi sai mika mata hannu yake Ard’o na bigiwa wai baxa shiba. “Ayd’o yana wasa ka bashi ni muyi taye.”

Hafsat k’arama ta fad’a tana kallon Ard’o ya wurga mata harara “ke ki raba kanki da iyalina idan ba haka ba kaniyar ki zanci.” Cewar Ard’o yana gyara wa Tanimu d’anshi rikon da yayi mai ta kuma kallon shi idanunta jawur kamar taruwar jini tace.

“Iya julai (zulai) matar Ard’o tana shama hira (fura) daka iteye (ajiye) a taki (d’aki)…” Numafar gidan Ard’o yayi yana shiga rumfar shi ya hangi zulai akan nono da furar daya ajiye yace sai dare zasu sha.

“Zulai ! ya fad’a yana zaro idanuwa tare da ajiye Tanimu a kasa ya k’asa ciki yana kare mata kallo jikin ta sai rawa yake yau asirinta ya tuno tana goge baki Ard’o yace “daman kekike shanye duk abinda na kawo gidan ga amma kike cemin awaki ne ke shigowa ciki? Yau dai k’arama ta tona miki asiri kuma zan d’auki mataki akanki kinsan halina…”

Yana fita tayi kwafa tare da yin alwashin cin kaniyar hafsatu karama tunda ta tonata bayan shekara da shekaru babu wanda ya sani. Ita kuwa Umma Hafsatu har ta dena damuwa da halin da Hafsat k’arama ke yi dan idan ta hanata tonan sililin ma kamar k’ara zuga ta ake yi……

FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》

               ????????
                  ????

© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s

    *_NA_*

FEEDOHM????
&
_K.A.S Precious HAJJA CE????

SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu

    Page *21-22*

Hutun da yazo ne kwana biyu wanda sati biyu kawai zai yi ya koma shiyasa shi shiryawa dan komawa katsina, cikin shirin shi ya fito na blue jeans da white d’in t.shit hannun shi d’aure da whech mai ratsin color blue a jiki sai cover shoe white da siririn glass a fuskar shi yayi hanyar side d’in Madre.

“Ahh Ma’aruf yau kuma sai ina? Cewar Abba dake kokarin fita suka had’u a k’ofar parlorn. Kallon shi Ma’aruf yayi tare da yin k’asa da idanu yana sosa cikin dumbujejan lallausan gashin kanshi yace “Abba zan shiga katsina ne ina son zan nayi solving problems na wannan men d’in, so yau zan shiga gobe ko jiba zan dawo.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button