ABUNDA KE BOYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Abba yayi murmushin jin dad’i tare da cewa “To my son Allah yayi jagora ya kuma baka nasara.” Ma’aruf yace “amin abba na gode sai na dawo.” Daga haka suka yi sallama abba ya fita shi kuma ya k’arasa gurin Madre ta bashi breakfast yaci sannan suka yi sallama tayi masa fatan alheri ya shiga mota drive yaja. wannan karan ma ba su yi sallama da Sumayya ba tana bacci ya tafi.
Yana sauka aka kuma had’ashi da wata sabuwar guider d’in, ta wannan karan tantiriya ce idanunta a soye suke sai dai kuma suna had’a idanu taji tana wani mugun tsoran shi ba shiri ta koma normal na matsayin ta na guard. Focal parson d’insa ne ya karaso sannan suka shiga mota suka wuce kauyan gwadabniya.
{{ }} {{ }}
Yauma kamar wancan karan mutanan kyauyan suka dinga gudu tamkar zunga zakuna, suna karasawa kofar gidan malan lado kundum ta fito da sauri tare da yank’are baki tana kiran Mai-tafasa…
“Wallahi ke dai kam kundum kin shiga uku sauran ki kirss ki lalace, aikin banza ke ba dai ajiki da bakin alheri ba sai akan su Hafsatuwalle, ! aikin banza ai na san dama yaune ake d’amrawa lauratu aure amma dan tsohon muna hirci kinzo zaki min gulma da…..” Bakinta ya mutu lokacin da taga shigowar su Ma’aruf cikin gidan.
Direct cikin d’akin da lado yake kwance suka shiga Ma’aruf sai faman toshe hanci yake sabida tsananin d’oyi, wari da hamami dake tashi a gidan, da kyar ya iya tsayawa a gurin lado yana mai gwaje-gwaje duk da anyi dama amma anga cutar AFP d’in sai dai rashin yin rigakafinta ya sanya yayi haka sannan kuma ba ita kad’ai ce tasa mai wannan larurar ba domin da itace zai iya moruwa da wani sashe na jikin shi amma wannan duk jikin shi babu mamora. “Mai kyau Allah yasa dai lado na zai warke?”
Cewar mai-tafasa tana dashare mai wawulan bakinta wanda yayi jawur gashi gaban ba hakura, banza yayi mata tare da bada wani magani focal person d’in ya d’ago lado ya bashi yasha sannan suka fito dan zuwa gidan mai unguwa sumai karin bayani…..
{{ }}
Tararwa suka yi an gama d’aurin auren lauratu da sallau akan sadakin akuyar da sallau ya bada, karasawa suka yi gidan mai unguwa mutane suka biyo su mata da maza yara da manya ciki harda mutanan gidan su Hafsatuwalle, ita kad’ai ce bata fita ba kasan cewar ko taje da zagi da cin mutunci zata dawo. Carpet focal person ya fito dashi daga cikin mota ya shimfid’awa Ma’aruf sannan mai unguwa ya zauna a shimfid’ar shi yana dasharewa Ma’aruf wangalelan bakin shi…
Banza yayi mai zai fara bayani sai ga lauratu ta karasa kusa dashi cikin farin cikin ta tace, “bature ashe zaka dawo garin mu? Ai munga kaya sunyi kyau kuma ankasawa Hafsat tayi kyau itama Allah ya biya.” Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin kafatanin ‘yan garin da irin halin su “bature nima yau aka d’amra aure na kaga mijina can sallau.” Muryar lauratu ta dakar mai cikin kunne, bin point d’in da tayi mai yayi da kallo har ya kai ga fuskar sallau yayi saurin rintsa idanuwan shi ya zura hannu ya Ciro 10k ya bata yace tayi hidima idanun mai unguwa akan kud’in yana son yasan yadda zai samu wani abun aciki kud’in.
AFP (Acute Flaccid Paralysis) ita ce ake cewa cutar shan’inna, sannan Likitoci sun ce a yankin kudu da Hamadar Sahara, mutum miliyan 12 zuwa 15 ne ke fama da cutar amosanin jini kuma kashi sittin cikin 100 suna Najeriya.
Ba a san haƙiƙanin yawan masu cutar amosanin jini ba, amma dai ƙwararru na cewa mutum miliyan ashirin zuwa miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ita a duniya. Haka kuma duk shekara ana haifar mutum kimanin 2,400 masu wannan cutar.
Mafi akasarin inda ake samun yawan wannan cutar ta shan’inna shine a kauye, cutar AFP na samuwa ne ta hanyar kazanta, rashin tsafta sune suke kawota, kuma tana samuwa ta kananan yara daga shekara 1 zuwa shekara 5. Malan lado yana d’aya daga cikin wad’anda ke da cutar sai dai rashin kulawa da rashin yadda da rigakafi da kauyan suka yi shine ya janyo mishi samun matsala a cikin jikin shi, wani lokacin idan ciwon ya motsa jikin shi babu inda yake mai aiki ko kuma yayi ta cewa a matsamai jiki sabida yadda yake ji a haka har…” Ma’aruf ya zaro idanuwa kirjinshi na dukan uku-uku ganin wata hallita tazo ta zauna akan cinyar shi sai wangale mai hakora take yi tamkar wata aljana. “Allahumma ajirni filmusibati fakalufli min khairu minha.”
Ita kawai Ma’aruf ke fad’a a fili, ganin haka ne yasa guard d’inshi saurin zuwa dan ta d’auke ta sai taga idanuwan yarinyar sun koma wani irin abu tayi saurin matsawa baya tamkar wadda aka kafe ta tsaya. Masifa ‘yan garin suka fara masifa ita kuwa Hafsat k’arama ta juya tana kallon Ma’aruf wanda ke zaune cikin tashin hankali da tsananin tsoro, sauran kiris ya saki fitsari ya jiyo muryar mai unguwa na cewa.
“Ke shegiya yarinya k’arama kin tashi daka kan bakona ko sai na ham6are ki ja’irar yarinya fitinanniya…?” Ya fad’a yana kokarin tashi yaji ya kasa, shi kam Ma’aruf daya tambatar da cewar mutum ce sai ya dawo cikin mode d’inshi amma duk da haka kirjinshi be dena bugawa ba ya kalleta yana kokarin mikar da ita yaji tana shafa mai sajen da ya kewaye fuskar shi da hannuwanta masu bududu da jar kasa, ya lumshe idanuwa zuciyar shi na shirin fitowa waje…. “K’arama zo mutai gida gurin Umma mun barta ita d’ai.” Lauratu ta fad’a tana karasawa gurin tare da kallon Ma’aruf tace “bature Hafsat ce wadda ka siyawa kaya shekarun baya…” Tayi saurin jan hannuta shi kuma jin sunan yasa shi saurin bud’e ido……..
FEEDOHM????
&
HAJJA CE????
???????? ABUNDA KE BOY’E……
《Almost True Life Story》
????????
????
© HASKE WRITER’S ASSO
Home of expert & perfect writer’s
*_NA_*
FEEDOHM????
&
K.A.S Precious HAJJA CE????
SADAUKARWA……
HAFSAT 《Ummana》
HAFSAT 《Miss Xoxo》
Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu
Page *23-24*
Da sauri ya mika mata hannu yana kiran “Common ……”
K’arama tayi saurin fincike hannunta daga Lauratun ta dawo tare da zama saman cinyarshi ta zuba mashi manyan Idanunta !Kallonta kawae yake, yarinya mai kyau amma tayi duk’u duk’u da ita ……Idan baka kai zuciya nesa ba sae ka rantse ruwa bai tab’a hawa jikinta ba……
“Yaro Ummana tace idan yaya Lauratu tayi aure dakinta zan koma……”Maganar da ta doki kunnenshi kenan yayi saurin maido natsuwarshi ……
A Sanyaye yace “Ko……”
Mai’unguwa yace “K’arama da k’warank’watsa na mike sae na ci Ubanki idan baki d’aga man bak’o ba……”
Hararanshi tayi k’asa k’asa tana turo baki tace “Balan Sauka in ba! b’arawon masara……”
“Uban Waye b’arawon “Ya fada a harzuke sannan yace “Kai bawale je kace Uwar wanga diya ta sameni gida idan rana ta take……”
Ma’aruf ya kalli guard dinshi a raunane don har ga Allah ya gaji da zaman K’arama a jikinshi yace “Dauk’e ta zan tashi……” kafin ya rufe baki ta sakar mashi fitsari a jiki da sauri ya runtse ido zuciyarshi kamar ta fito dan takaici
Zaro Ido tayi tana fadin “Sir wallahi baran iya taba ta ba ji kamar wata Vampire……”
Lauratu ta matso a sanyaye ta kama ta da kyar suka shiga gidan tana turje turje ……
A hankali ya mike ba tare da yace komae ba ya bude mota ya fito da robar swan ya fara tsiyayawa inda ta mashi fitsarin !Gashi duk inda ta taba a jikinshi kamar an debi bakin tukunya a shafa a gurin !tsaki ya saki lokaci guda ya shige motar yana kakkab’e jikinshi……Mai’unguwa ya rakashi ya rufe mashi motar sannan guard dinshi ta shiga suka tafi ……Suna tafiya mai unguwa ya fada gidansu yana kiran “Ke Lauratu fito”