NOVELSUncategorized

KWARATA 22

???? —— 22

              Saida na tattara duk wani abu da nasan ina buƙata na adana shi a ma’adar da nasan bazai wulaƙantu ba , ko wace macen da zamu koma da ita gidan nice nasa aka kwashe kayan kowa aka kai gidan da zamu koma da zama…


         Kafin azahar har mun gama saboda babu mai gado a cikinsu duk dai katifa ne kuma babu macen dake da ledar tsakar ɗaki saini !

      Saida na tabbatar an ajiye komai a mazaunin daya kamata , sannan na shiga wanka , kafin in fito an share gidan ƙwal gwanin burgewa , Hafsa tazo sai kashe sulfie sukeyi ita da sauran jama’ar tamu ,

      Ina fitowa daga wanka tace uwar room maza ki shirya kizo ayi dake kar a baki labari , Amisty ce tace babu wani uwar room uwarmu ce gaskiya a wani cire room kawai mu kirata da mother , shewa sukayi dukansu lokaci ɗaya suna cewa uwa…

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘160 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

      “Yar gajeriyar dariya nayi cikin sigar barikanci na wuce ɗakina banyi musu magana ba , hotuna sukaci gaba dayi har na gama shiryawa nima na fito !

Ina fitowa suka ɗauki sowa domin sun san mother tasu ba daga baya ba wurin iya ɗaukar wanka ,  banje koya ba kuma babu wanda ya ɗorani nice na koya dakai na kuma ni na ɗaura kaina , banda uwar ɗaki nice uwar ɗakin kaina kuma nice uwar ɗakin wasu ,

        Amisty ce ta bani kujerar roba na zauna, da “yan daba da duk wata kwartuwa mun hallara wurin, bayani na farayi musu kamar yadda muka saba a duk lokacin da muka zauna…

       Hafsa kuwa ciro wayarta tayi ta faramin vidio kamar yadda naga ta koya kwanakin nan, saboda haka sai nayi shiru yayin da su Amisty suka ci gaba da goga bayani tare da ƙara ƙwarara wa kowa guiwar shi a cikin harkar bariki !

      Komai ɓaro ɓaro sukeyi suna sakin maganganu yadda harshen kowa yake iya furtawa, Hafsa kuwa abinda yasa banyi mata magana ba na lura da halayyarta tana da saurin hasala sannan kuma tana da ɗauka da ajiyewa , na ukku kuma abinda na lura da ɗabi’ar ta zatayi tonan asiri haka kuma zatayi cin amana zata tona asirin wanda suke tare idan suka rabu …

     Ni kuma banda haƙuri idan abu ya ɓatamin rai saina bigi mutum nake samun natsuwa , tou zan ƙyale Hafsa amma nasan irin zaman da zanyi da ita , sannan nikam dai sirri na ƙarya takeyi taji shi kuma anƙi a rabun da ita dan idan har na rabu da Hafsa zata yankamin ƙunya biyu dani da “yan team inta zamu zama abokan hamayya , kuma babu abinda zai hana asirce asirice saboda su sun ta allaƙa da malam tsibbu amma maganinta ɗaya shine zan sace wayarta ta ɓace kwata kwata babu layi babu wayar bare kuma tabi tsohon tarihin jerin kira ta samu wasu lambobi, idan taƙamarta sabko tabbas ni a wurin na kwana ,

     Har aka gama zaman ban sake cewa umm umm ba, bayan an gama duk suka zagayeni akayi ta hotuna , duk wanda yaga hotunanmu yasan ni iskanci na ya fita daban a cikin nasu, yadda suka bani shugabar iskanci tabbas iskanci ya fito a tattare dani…

      Bayan an gama hotuna muka fito ƙofar gida , saman motar Hafsa nayi tsalle na haye , Hafsa tace bari in ƙara ɗaukarki hoto murmushi nayi tare da cewa ngode , ɗaukana tayi nanma kowa ya ƙara yayyaɓeni sai an mana maza da mata duka Hafsa taci gaba da bamu filasha !

       Saida ta gaji da ɗauka sannan mukayi sallama da ita , ta wuce gidansu mu kuma muka koma namu gida , dukanmu a ɗakina muka sauka , har dare suna nan domin Amisty zata kwana wurina ne kuma ma dai ta dawo wurina da zama kwata kwata…

    Bansan abinda yasa ba kuma ban tambayeta dalili ba , sai dare sosai su A ` i suka tafi gida , Nana da Karima kowa ya shige ɗakinshi muka rage daga ni sai Amisty, addu’a nayi na kwanta bacci ,

        A ɓangaren Hafsa kuwa dan ta wulaƙanta ni ta tozarni a idon Dikko idan ina da sauran mutunci ko ƙima ta kakkaɓe a wurin shi , duk hotunan data ɗauka gaba ɗaya ta tura mishi su , da vidio maganar dana fara da kalaman batsar dasu Amisty sukayi , da kirana da uwar gidan kwarata da akeyi duk saida ta bawa Dikko labari bayan ta gama tura hotunan da vidio ‘,

     Idan ran Dikko yayi dubu saida ya ɓaci amma bai nunawa Hafsa ba ranshi yayi mishi babu daɗi ba dan baiyi tunanin irin wannan hotunan zata riƙa kawo mishi ba , kawai dai ya ɗauka hotunan Sultana zata turo sai kuma idan tana zaginshi sune kaɗai zata faɗa , amma wannan vidio ya girmi ganin idanuwanshi maganganun sun girmi jin kunnuwanshi ,

         Tabbas zai takawa Hafsa burki da irin wannan vidio kuma zai tsawatar da ita zai gwalashe abun idan ba haka ba irin wannan vidion na An mata zasuyi ta yawo a social media shi kuma idan har haka ya faru baiji daɗi ba,

       Tunani dai barkatai a zuciyarshi , amma ranshi da zuciyarshi yafi bashi cewa kayi mata magana gaskiya shekaru biyu idan suka tafi a haka kaga zakayi takon saƙa da karuwa mutuncinka martabarka da ƙimarka zai zube a wurin al’umma ga siyasa bata raina abun magana, sai ka tsaya takara zaka gane abun ya zama shirme, shawarar da zuciyarshi ta yanke shine ya fita daga harkar taron yara don asali nasaba da mutunci gidansu ba iri ɗaya ne dana gidansu Sultana ba.

      Burun duniya akan shi ɗaya tal mahaifinshi ya dogara yayi tsayuwar arfa wurin ganin ya zama mutumin kirki ya fito cikakkan mutum ya kashe kuɗaɗe da yawa wurin ganin ya tsaida ni a saman ƙafafuwana ,  mutane suna cewa duk “ya “yan da aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗora musu gurɓatacci ne , mafiya yawansu basu da tarbiyya , ni kam ba lalatacce bane domin idan nayi duba da yadda nazo…

       Tsoki yayi tare da kiran Hafsa yayi mata tatas yace daga ita harma Sultana duk zaici mutunci su bayasan maganar Sultana haka kuma itama bayasan ta sake shiga sabgarshi ko kiranshi ta sakeyi ko text wallahi sai yasa an kulle mishi ita , yafa ci uban Hafsa sosai ya ƙara da cewa itama Sultanar ta sake ambatar sunanshi wallahi zaici ubanta ne, saida ya tata iskanci mai isarshi ya kashe wayarshi,

        Al ‘ Ameen yace mai gida lafiyarka kake ta faɗa , idanuwa jajir Dikko yace Al ‘ Ameen idan aka ce maka na taɓa zina tsakaninka da Allah zaka yadda ? Al ‘ Ameen yace mema yasa kake faɗar wannan maganar don Allah ka daina abinda ma bazai taɓa yuwuwa bane ba…

      Idon Dikko cike da hawaye yace kasan yarinyar dana shaƙe a asibiti ? Al’ Ameen yace Eh nasanta mai gida , Dikko yace kaga ai yarinya ce sosai ko ? Al ‘ Ameen yace Eh , Dikko yace wallahi da nayi auren wuri ina iya haifar yarinyar nan , amma tsautsayi da ƙaddara yasa na saki wani irin ƙatoton layin da inaji kamar in cakawa kaina wuƙa in mutu kawai in huta,

      Murmushi Al ‘ Ameen yayi tare da cewa haba mai gida ina kai ina haifo mai shekarun yarinyar nan , da kayi aure kam da wuri baka tsaya karatu ba kuma gashi har yanzu duniyar nemanta akeyi duk wanda kuɗi yayi ma yawa so kawai yake a kirashi ranka ya daɗe , duk dai haka gaskiya baka haifi yarinyar nan ba , tsoki Dikko yayi tare da ɗaukar wayoyinshi ya shige ciki , gefen gado ya zauna tare da zagba tagumi ya fara tuno wa kanshi ko shiɗin waye…..


         WAYE DIKKO…?

Dikko Umar Kurabau shine cikaken suna na…


         Mu cikakkin asalin “yan cikin garin katsina ne , bamuyi rayuwa a ƙauyen kurabau ba haka mahaifina da kakana basu rayuwa a wannan ƙauye ba , amma kakan dadyna shine yayi rayuwa a cikin wannan ƙauye dake ƙarƙashin kauyen rimi local government…

            Mutane ne masu cikakken arziƙi da wayewa kuma sarautar kauyen a gidansu kakana take wacce suka gada suma tun iyaye da kakanni , ko a wancan lokacin mutanen kurabawa tuni su wayayyu ne kuma tuni suka waye da ilimin zamani !

        Kakan dady na duk da yake bakauye baya da kidadanci haka kuma bashi da jahilci , wayyen tsoho ne da yasan rayuwa , kuma tsohone mai cikakken ilimin addini,

        Abinda ya kawo kakana cikin birni shine neman ilimin zamani , kuma shima mahaifinshi shine mutumin daya fiddoshi dan neman ilimi bayan ya tabbatar daya haddace al’kur ani mai girma a saman kanshi kuma yasan littafai na musulinci .

         Karatun boko bai wani bashi wahala ba saboda yana da ilimin addini sosai , saida kakana ya gama karatun sikandire sukul { Secondry school } ya koma kauyen kurabau,

       Mahaifinshi yace tunda ya ɗagawa ƙauyen na wasu shekaru ya haƙura kawai ya koma cikin garin da zama , dan a samu ci gaban rayuwa !

      Mahaifinshi da kanshi yazo ya nema mishi wurin zama sannan ya bashi kuɗaɗe ya kama kasuwanci ya nemi abinda zai dogara da kanshi, dan a wancan lokacin idan mutum yayi secondry sch anan yake tsaya dan duk wanda yazo wannan matakin gani ake an ƙure.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button