AHUMAGGAH 13

Inda aikin sojan na sa ya sa baiya cika zama sosai Hakan ya sa jahan Aarah ta fuskance bakar azaba da fitinan su na tsananin kishi daga wajen jahan khatun da sarauniya dilshad mahaifiyar ta.
Jahan Aarah ta sha wuya sosai,gashi Allah bai bata ciki akan lokaci ba most time sai dai taga jahan khatun Tayi ciki amma banda ita
To da shike Allah ba azzalumin bawar sa bane cikin ikon sa sai duk wani cikin da jahan khatun keyi da yayi kwari sai ya bare dakansa
Har aka shafe shekara biyar babu wanda ya rayu
Ahakan ma Sun sha daura ma jahan Aarah laifi da zargi da duk wani kazadi akai,amma haka dai ta cigaba da hakuri dasu Har Allah ya zo ya bata cikin khaldun sa’ood babu wanda ya lura.
A lokacin kuma har gen hamood ya cika 4yrs couse ya rikide daga aikin sa na navy yaje dawo babban army officer still a kasar american.
Ranar daya zo hutu Sosai yayi murnan samun cikin jahan Aarah Murna marar misaltuwa,domin kuwa ta kasance matar so a duniyan sa!
Sabanin dilshad da yarta khatun da abun ya matikar bata musu ransu.
Dama asiri mai karfi sarauniya dilshad din ta saka jahan khatun tayi akan jahan Aarah tun farkon auren su akan bazata ta taba haihuwa ba
Ko da su ka zo suka ji zancen ciki sai abun ya matukar basu mamaki gashi matsafiyar su tace dasu akwai rabo a tsakanin su har da kari.
Jahan aarah kuwa Tana da hakuri sosai ga juriya da yawan biyayya ma mijin ta
ahaka cikin azaban fitinan su har ta raine cikin khaldun saood a masauratr dilshad batare da ta gaya ma mijin ta wani abu mummuna akan su ba.
Tun baya ganewa har ya zo ya fahimta Sosai
Toh bayan jahan Aarah ta haifi khaldun sa’ood ko shekara biyu mai kyau baiyi ba sai ga cikin subaya ya shigo mata a bazata.
Nan ma jahan khatun ta tada borin kishi da masifa,har sai dilshad ta tursasa gen hamood ya karbe khaldun saood a hannun jahan Aarah akan su ne zasu rike shi kuma sune zasu raine shi
Shikuwa baiyi musu ba ya dauko yaro ya bar musu shi.
Jahan Aarah tayi kuka sosai dan a duniya idan akwai abunda take so to danta sa’ood ne.
Wannan biyayyar da gen yayi shine abu na farko data kasa nuna hakurin ta akai
Toh sanadiyar nuna wannan fushin jahan Aarah ne ya jawo dilshad ta saka dokan cewa gen ya fitar mata da jahan Aarah a kingdom din ta kuma baza a bata khaldun din ba
Hakan ya jawo sanadiyar dawowar jahan Aarah kasar nigeria cikin garin kano,inda har ta haifi subaya ta raine ta.
‘Toh Tun wannan time din jahan Aarah bata sake komawa lorestan ba sai dai subaya da gen hamood suje,har shekaru suka shude su dilshad girma ya zo suka saduda suka fara barin khaldun shima yana zuwa ma jahan hutu nigeria sama sama.
Sun so ace khaldun ya tsani uwar sa ya fifita su amma Ikon ubangiji ya sa duk tsananin biyayyar gen hamood
Da kuma irin rainon da suka daura khaldun din akai bai hana dukan su jin kaunar jahan Aarah kamar yadda ya kama ta ba.
Toh A lokacin da gen ya tafi da Jahan Aarah nigeria kari na farko suka ci watanni biyu achan da mamakin sa ya dawo persia ya samu Jahan khatun itama tana dauke da cikin wata daya.
Ba’a wani jima da haifar subaya ba jahan khatun ta haifi yaron ta mai suna KAAMIL HAMOOD
Sai ya zamto khaldun saood
Da kaninsa kaamil sun taso tare a acikin kingdom din dilshad khatun
Tun khaldun na shekara 12 aka tura sa fannin marine soja,shikuma kaamil na kaiwa 15 shikuma aka kaishi navy a cahn kasar america
Anan har suka girma gen yayi retire ya samu duk wani matsayin daya ke dashi a yanzu suma yaran sa suka samu ingantaccen rayuwa.
Within the years Rayuwar su gaba daya ta sauya
yanzu dilshad ta dada tsufa sai tayi sanyi ta bar jahan khatun da hidima da ragamar rayuwar su,sun yi munafurcin har sun gaji jahan Aarah bata kula su ba,karshe ma da suka ga ta kyale musu gen da yayan nata gaba daya dan dole suka hakura suka dena shiga damuwar ta
ba kamar da chan ba.
Haka rayuwar su ta kasance
Sarauniya dilshad ta hakimce tana controling duk wani hidiman auren gen hamood da kuma rayuwan yayan sa Sa’ood,kaamil da subaya.
Gashi Acikin sun nan babu wanda bata iko da shi,dan direct zata kafa musu doka kuma ya zauna kenan har abada..
Shiyasa ma tun farko ta sa yarta jahan khatun ta rike khaldun saood kamar dan cikin tan batare da wani ha inci ba
A yanzu Jahan khatuun tafi nuna soyayyar ta da duk wani daukawar ta akan khaldun saood fiye sa dan cikin ta kaamil kuma Duk wannan yana daga cikin umarnin sarauniya dilshad
Aganin su bakin cikin su shi zai kashe jahan sannan su zasu yi yadda suke so da rayuwar khaldun anan gaba.
Jahan khatun itace babban yar sarauniya dilshad sai wata da ake cewa jahan zainobia.
Jahan zainobia bata da irin muguyen halayen uwarta dilshad khatun bare kuma sistern ta jahan khatun
A africa jahan zainobia tayi aure ta haifi yarta mai suna JUNNUT,
WAnda aka dauko ta shekara guda kenan da watanni 4 da suka wuce daga chan yankin jinsin fulanin dake kusa da gulf of eden da bahar maliya.
Junnut itace asalin jini kuma jikar sarauniya dilshad ta karshe a masarautaran khoshirdy dynasty.
#FOLLOW SURAYYAHMS
COMENTS AND
Share share❤❤