AHUMAGGAH 14

To duk ana maganan hadin auren nan ne amma dilshad bata fito fili ta fayyace ma jahan khatun komai ba sai dai inzatayi abu ta bata umarni wanda dole ne suke cikewa babu tambaya.
Daya fito zai tafi Toh Jahan khatun din ce ta masa rakiyar har bakin inda jet dinsa inda zai tashi
Daga nan Tafi mintuna goma tana tunani Bayan tafiyar san babu wani bata lokaci ta juyo a haukace dan kuwa har yanzu
Kanta bai dena juyawa da abubuwan da mijin ta ya gama fada mata game da maganan auren junnut da khaldun saood da sukayi da dilshad ba
Kafin su rabu Agaban sa kam bata nuna komi ba amma ayanzun Tafiya take cikin sauri da hatsala bata ko damu da yadda jelar abayan ta yake bin kasa da shara yuuuuu yana sandarewa ba.
burin ta bai wuci taga kawai ta isa gaban dilshad khatun ba
cikin dacin rai da bambami take sauke maganganun zici
Ya za’ayi mamah tayi min haka?
Ohh dama shiyasa ta bada junnut hotunan sa’ood ranar dan tasan zatayi nata zabin kuma bazata zabi dan ciki na ba?
Toh A gaskiya bazan iya ba,i cant let that happen jinin wancen mayyar bazai bi jikin yata junnut ba,tsaban idon ta ya rufe cikin sauri a durkufe ta saka kafa cikin babban falon dilshad babu ko sallama ko gyara dilshad din ne a zaune agaban ta akan throne tana binta da ido
Data juya ido Wani tsawa mai birkitarwa ta ma bayin wanda atake suke zame suka bar harabar wajen baki daya
Cike dauriya ta Dan rusuna kai,muryan ta har na srkafewa cikin tuhuma bacin rai da nuna rashin fahimta bata tsaya yin wani gaisuwa ba ta fara da cewa
Na kasance mai maki biyayya tunda har kika sani na so kuma na raini dan wanda nafi natsana a duniya kamar dan ciki na
tace Tunda junnut taxo gidan nan hoton saood kawai ake nuna mata why not my son kaamil.?
“MOther,..pls ki gaya min dalilin da junnut zata auri sa’ood ba dana kaamil ba
…yafi shi kyaune?aji kudi ko gata ?
Why….why mother sai ta juya kai tana hushi mai zafi
Kallon ta kawai sarauniya Dilshad takeyii batace komai ba har sanda ta gama bambamin tayi shiru kafin
Ta sauko daga kan kujeran mulkin ta tsaya da dan sauran karfin ta
tace
“Hmmm lallai Kina da yawan mantuwa khatun,.wai shin kinga laifi na dana fiye son na dauke wahalar yi miki tunani akan abunda xai fishe ki da rayuwar ki.?
Tabbas nace junnut khaldun zata aura
Ba kaamil ba
Domin kuwa Junnut da kaamil duk jinin mu ne kin sani na sani kowa ku maya sani
amma tsakanin kaamil da sa’ood
Ke kinsan waye dan halak acikin su.
Bayan firta wannan kalman Wani shiru ne ya tsinke a wajen kafin dilshad ta cigaba
Shin in na mutu haka ke zaki tafiyar da rayuwar ki babu tsari?,banyi tsammanin dan nace haka har ya dame ki ba dan kuwa gata mai girma zan miki da auren nan
Dada Matsowa kusa da ita tayi kamar wacce zata mata nasiha,tace dube nifa, na tsufa kuma mutuwa ta na ke hangowa,toh Wani amfana zakayi idan Shi kaamil ya auro junnut,cikar burin yan uwantakar mu?in na mutu ai zaynobia bata ma duniyar ai
Ohhh my zain,yarinya ta mai tsananin biyayya
,Allah ya sa jikata junnut ma ta sha jinin ta
Ke kuma sam bakijin magana ta khatun,da kinaji da tuni kin koma chan nigeria inda mijin ki ya gina musamman domin ki ,ai ko ba komai dai tasan ba tsoron ta kike ji ba da kika ki gidan miji kika zauna agaba na.
Baga shi kin bar tan ba?Toh nidai yau naga sauyin yanayi a halayen hamood har da furucin sa.
Im sure matar sa ta fara cin galaba akansa da bin malamai da yan tdubbu,na lura ma yanzu itace uwar sa da ubansa wai bakiji meyace min ba?wai ni na jira dansa yazo da kansa kafin subi umarni na
mmmmmmmm
Toh Idan baki bari yarinyar nan ta rike mana dan masu gida ba nan gaba zamu zama tarihi marar ma’ana a rayuwan nan.
Mijin da kike takama da shi din sai mun rasa shi ni dake kuma gaba daya duniya zata zage darajar mu.
A razane jahan khatun ta dago cikin wani irin yanayin barazana,tace zan rasa mijina fa ki kace?Akan Aarah?tabbb ashe a nigeria za a fara kuwwar tashin duniya,dan kuwa tana daf da konewa kurmus. why r u saying all this wai ma Mai kike nufi ne mother
“Murmushi mai sanyi dilshad tayi tana mai sauke ajiyan zuciya,tace
Please Do not pretend khatun nidake ne anan babu wani batun boye boye
Tuni jahan khat ta sauke kanta ta kasa tayi tsit,wani shiru wajen ya dauka for some moment
Data dago, Eye ball to eyeball suke kallon juna
With much seriousness dilshad tace khatun
Kiyi tunanin Wata rana dole gaskiya zai fito kuma dole hamood zai san cewa Kaamil danki ba jinin sa bane jinin saurayin ki ne dan sarki maheer
Hamood zai san kin rike cikin wanda suka raba shi da iyayen sa acikin gidan sa.
kinga ke zai rabu dake haka nima zai watsar da ni dan babu cin amana a tarihin zuriar yan uwantakan mu da shi
Amma kuma akwai tarihin HALACCI da kuma SOYAYYAH da shi kuma zanyi amfani na daure tasirin auren ki kafin na barki a duniya
Yes,Idan kika ce na nuna hutun saood ma junnut dan ta so shi fiye da kaamil ne bakiyi dai dai ba.
Ai nima Ina son kaamil din amma bada junnut ba shiyasa kikaga ban hada su ba tun farko,daga yanzu junnut itace makamashin rayuwar ki
Da babu gwara ba babu dadi
Ki dena tunanin sihiri ya binne gaskiyan maganan asalin kaamil tunda Wata rana nikaina zan mutu,kisan kuwa komai kararre ne.
Dokace Dole khaldun sa’ood ya auri jinin mu junnut kuma wannan shine kullin auren da zai baki daman zama a rayuwar hamood na har abada koda asirin mu ya tonu
Nasan hamood da matarsa bazasu so su tozarta rayuwar dansu ba kinga kenan junnut zata kasance qashin kifi a wuyar su Duk abunda zai faru bazai yi muni ba kodan darajar wannan aure,kina fahinta ta?Kinji ko bakiji ni ba?
Jiki a matukar sanyaye jahan khatun tace naji,
Lallai nayi wauta mamah! Agafarce ni
Toh tun daga wannan lokaci suka hade kai akan maganan,sai dai kuma babban abunda yasha musu kai shine yadda auren zai kasance
Shin ayi aureb tun a yanzu a kuruciyar ta ne koko su jira sai yarinyar ta kai munzalin da zata iya murza musu kambun su da kyau?
Bayan kwana biyu junnut din ce kwance akan wata sharbeben canopy bed wanda yasha kwalliyar dark purple and silver linens.
Maid ce ta shigo ta rusuna a kasa tayi gaisuwa,junnut bata ma sanda da ita tsaban yadda tasa hankalin ta gaba daya akan game din data keyi
Haka baiwar tayi dakon jiran ta har wajajen mintina 10 sannan ta juyo tana da kyankyami dan haka ta yamutsa fuska cikin kasaita tace meye hakan?
Maid sai ta dada matsawa baya Tace Ranki shi dade sarauniya dilshad ce ke neman ki m.
Follow#Surayyahms
Jumuat and Happy weekends dearies,mutane dayawa suna dashi a pc so try and share with masu nema,keep sharing ur views and
Fatan idan mun dawo da sabbin posts ranar monday naga coments din dayafi na posts din wannan satin zafii???? i so much apreciate ur tarin coments
Ahumagga real fans,surayyhms novel grop,zinne smart grp,zauren brilliants,zbi,san,muneera nvl grp uwa uba zauren mai dambu Love u much guys????????????