NOVELSUncategorized
KWARATA 71

???? —— 70
Bello yace kamar ya a ɗauremu ? Dady yace saboda ka lalacemin “ya a gaban idona har ina tsaye inabin layi a doka ƙaraurawa in hau saman ruwan ciki ɗiyar dana haifa , taya kake tunanin bazan sa a ɗaureka ba ? Bello yace gafara can itama ai wacce kake tunanin taka ruwan cikin nata itama “yar taka ce sakaran banza ka lalatamin duk wani tsari nawa ai duk cikar garin katsina da batsewar ta babu ubanda ya isa yasa a ɗaureni , bana ɗauruwu a wurinka kaidai sakaran banza mayen mace , to idan baka sani ba ka sani idan kuma ka sani ka ƙara sani Sultana ɗiyar Binna ce , wani irin juyi Dady yaji duniyar tayi mishi kanshi ya sara , cike da tashin hankali yace wane Binnan ? Bello yace Binna nawa ka sani ɗan uwanka da kuke Baba ɗaya dashi ƙaninka….
Saida Dady ya sakejin duniya tayi mishi ƙundubale yace Hajiyata ɗiyar Binna ce …..? Bello yace tabbas , wani irin haushi Dady yayi hafhaf kamar kare yace shikenan na kashe kaina shegiyar yarinyar nan tazo har majalissa ta sameni wai tana so taga bayan Binna dan wawanci da kidahumanci irin nawa ni idona ya rufe akan mace nace mata ai wani ya rigaki dan tuni an daɗe da tura Binna zuwa duniyar mutuwa , girgiza kai Dady yayi tare da cewa amma shu’umar yarinyar nan tacemin wane mai zarrar ne wanda yafi mace zafin nama….? Tabbas mutuwar ki ta zama dole abun kunya na rungumi ɗiyar ƙanina na farfaɗa mata maganganu masu girma na lashi bakinta na tura hannuna a cikin rigar nononta , na kamo hannunta nakai a girma na kai , idan har duniya taji wannan abun kunya sai tsinuwar mutane tahau kaina……..
Wato a wancan lokacin taso na faɗa mata wani abu , tabbas nace mata ni Yayan Binna ne , tana tare da wani ƙuduri a ranta tuni tasan wani abu ko kuma wani abu ya faru ya akayi ta shigo rayuwata ..? Wannan shine abinda ya kamata na sani farko kenan kafin inyi mata hukuncin daya dace da rayuwarta , shiru yayi yana nazari zuwa wani lokaci yace an kira Sultana nan ya akayi Hafsa ta bayyana wurin a maimakon Sultana ? Sultana tace zata zo sanye da niƙaf ya akayi Hafsa ta sako niƙaf tazo….? Mu kai Hafsa asibiti saita dawo dole duk zamu samu ansar wannan tambayoyin namu.
Cikin ɓacin rai Dady ya kalli Bello yace tun can baya boka yayi magana akan Sultana me yace wanda yasa muka toshe kwalwarta a kwalba….? Cikin tashin hankali Bello yace bayan Binna yazo yana farin ciki a gidana an haifar masa yarinya mace yace nasarar rayuwa yazo mishi , na tayashi murna sosai yayin da yake cewa ya samu mai share mishi hawayenshi tabbas nasara ce tazo , sai yace kuma yanaji a jikinshi ko baya raye “yan uwanshi zasuyi alfahari da jaririyar da zai sakawa sunan mahaifiyarshi.
Na taya Binna murna sosai bayan ya tafi daga gidana nazo na sameka na faɗa maka duk yadda akayi , a wancan lokacin sai kace muje a faɗawa boka yayi bincike akan ita yarinyar , abinda boka yace mana bayan yayi bincike shine kawai a toshe kwalwar yarinya shine mafita , Bello yace da muka tambayi dalili boka yace idan yarinyar ta girma zatayi ilimi tunda Binna yana da ƙudirin haka akan ta , yarinya tana kishin mahaifinta idan ta tashi ta ganshi a harkar caca zatayi faraucin fitar dashi a caca ku kukace ya dawwama a caca da zinace² idan yana yinsu ya gama lalacewa a mantar dashi tunanin mahaifinshi bare yayi tunanin dukiyar da aka bar muku na gado…
Dady yace ya akayi tasan Hafsa ɗiyata ce ? Ya akayi tasan cewa nine baban Hafsa ya akayi ? Ya akayi Bello tasan ina tare dakai ? Bello yace bata san muna tare ba gaskiya nidai nine nayi mata waya cewa saina kasheta , shine tacemin idan na isa zan iya kasheta in kasheta a wurin fesra hotel ,
yayin da zata sauko daga napep sanye da niƙaf , muna zuwa sai muka ganka a wurin sai muka tsaya muna gaisawa saiga napep ya sauke mai niƙaf bayan dama wacce muke nema tace mana zata zo sanye da niƙaf bamu tsaya bincike ba muna ganin mai niƙaf muka rufa mata tunda dai ta sauka a inda Sultana tace zata sauka , ka tambaya lafiya ? Sai nace maka Sultana ce , kace wace Sultana sai kawai nace maka ruwana ne , kace kana sha ba tare da sanin ko wace ce ba , ni kuma naga abokin cin mushe ba’a nuna mishi sai nace maka ni kasheta zanyi bayan mun gama morewa kai kuma kace muje bayan ka kira wacce kake jira bata ɗauki wayarka ba , sai muka haɗu gaba ɗaya muka taho nan dan bamu da isashshen lokacin da zamu tsaya muyi magana mun barshi akan sai mun gama zamuyi magana , Dady yace to bana tunanin Hafsa tasan Sultana muje asibitin munyi magana daga baya…
A wahalce yace mai gida… Hawaye ya gangaro mishi daga cikin ramin kwarin idanuwan shi yace na bari kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba , tashi Mardiyya tayi ta matsa kusa da Al ‘ Ameen ta kama hannunshi ta riƙe tana kuka , cikin muryar kuka tace Uncle wallahi tunda har ya dake akan Sultana wallahi kafin in bar katsina saina korata zuwa duniyar mutuwa , dakel Al ‘ Ameen ya haɗiye yawun bakinshi cewa karki kuskura ki fara tunkarar yarinyar nan dan wallahi idan har mai gida ya sani naki ya ƙare farko ma kenan , gara ki koyi yadda zaki kyautatawa Sultana idan har mai gida yaga kina santa wallahi sai yaso ki har cikin ransa saboda yana ma yarinyar nan soyayyar dashi kanshi baya san kanshi , yana san Sultana fiye da yadda yake san rayuwarshi , ko wane awa ko wane minti ko wane daƙiƙa wutar santa sake ruruwa take a zuciyarshi ,
Batajin magana karuwa ce mai lasi da take karuwancinta cikin tako da ƙwarewa , duk inda bakya tunani sansanin yanki garin nan tayi suna amma a ɓoye take huɗɗoɗinta , tunda ta samu ta dafe mai gida ta watsar da ko wane namiji ta koma zama gidanshi tana kwantalarshi , mafita ɗaya shine mu nemi inda Sultana take sai ki shiga rayuwarta sosai a fili ki nuna mata soyayya , a ɓoye kuma sai muci gaba da ɗirkaka mata asiri har mu samu muga mun shafe babinta daga duniyar masu rayuwa , Mardiyya tace haka zamuyi Uncle Allah ya baka lafiya ya ansa da am3n suka ci gaba da tattaunawa.
Mai gida ina ganin yarinyar nan sai an haɗa mata da roƙon Allah ko zata samu natsuwa sai inga kamar ba ita ɗaya bace ba , Ashiru ne yake magana da Dikko a waya , Dikko yace ita ɗaya ce tsabar iskanci ne kawai da raina mutane ka barta kaga yadda zan dawwarata idan na dawo , Ashiru yace to ai duk dai firgicin da nayi mata jiya wallahi yauma ta fita , Dikko yace ai dama nasan saita fita An mata halinta sai ita amma wallahi nine maganin rashin kunyarta , yau kuma ina taje , Ashiru yace wallahi mai gida tunda duhun asuba yarinyar nan ta tafi sabon layi can wurin one way layi ne na tsofaffin karuwai maza da mata , idan kana neman duk wani feƙaƙƙen ɗan iska daya ansa sunansa a harkar iskanci kaje wurin saika sameshi indai ya cika karuwa mai “yanci , tsofaffin karuwai ne da sukayi karuwanci shekaru da yawa da suka wuce sune suke rainon wasu ƙananan masu tasowa ,
Salati Dikko yayi tare da cewa innalillahi wa’inna ailaihir raji’un , wallahi saina zane An mata idan na dawo , wallahi ko zata mutu saina daketa saina dira kanta , cikin ɓacin rai Dikko yake magana shin mema tajeyi ne a wurin ? Ashiru yace mai gida wallahi ban sani ba , Dikko yace kenan tana nuna itafa duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar da ita akan duk abinda tasa kanta, wallahi ׳ nine na isa na dakatar da ita duk duniya baki da mai maganinki iskancin ki saini , kashe waya Dikko yayi bayan yacema Ashiru bara zan kiraka.
Da sauri na kwanta saman gado tare da jan bargo na lulluɓe gyara muryata nayi na maida ita yanayin muryar bacci na ɗauki wayata dake tsuwwa saboda kiran Dikko dake shigowa , ina ɗauka nace kai mai zuciya ya akayi ka sake kirana bayan kace baza ka sake kirana ba tunda banda wayau ,
Murmushin ƙarfin hali Dikko yayi tare da cewa key kina tunanin zan iya fushi dake ne dama ? Wai kamar ya kakejin girman soyayyata ne a zuciyarka , An mata yanzu ba lokacin maganar so bane ina kika je ? Ni ? Na faɗa tare da dafe ƙirjina nace kaji sharri ni kuwa ina zanje bayan saman gadona , ke ina kikaje ? Dikko ina kuwa zanje bayan bacci ma nakeyi kiranka ne ya tasheni , An mata ina kikaje nace , cikin kuka nace wai wannan wane irin masifa ne bayan ɗazu wurin 3 da wani abu na dare ka kirani kuma ka tabbatar ina gida , ke ji nan na rufe idanuwana yanayin fushi ya fara hawa saman kaina kafin in faɗa miki magana mai muni ina kikaje yayi maganar cikin murya mai tada hankali , saida naji wani fitsari²n tsoro ya kamani cikin rawar murya nace ƙofar gida kawai na leƙa na dawo ,
Waye yace ki leƙa ? An mata baki so dai ki zauna lafiya ko ? Dole dai sai kin ɓatamin rai ? Nidai ko An mata ? Dikkon naki ? Haba An matana faɗamin wai meke damunki ne don Allah , duk cikin lallashi yayi maganar , shiru nayi na kasa magana ina shashshekar kuka , cikin murya maisa natsuwa yace dole dai saina dakeki zaki natsu ? Ya tambayeni , cikin kuka nace kayi haƙuri don Allah , wallahi An mata bazanyi haƙuri ba saina zaneki faɗamin ina kikaje ? Sabon layi naje , tou waya aikeki ? Babu , badai zaki kiyaye fushin mahaukaci ba ko ? Idan har kika sabar wa da kanki “yan doke²n nan ko aure mukayi hankalin baya kwanciya sai na dakeki banda kyau ne idan ina yanayin fushi kuma na faɗa miki idan na ɓaci ba nine ba , me yasa kin raini da Allah ?
Ban raina ka ba , wallahi kin raina ni har kin faɗawa duniya kowa yasan kin raina Dikko , kayi haƙuri , hmmm banyi ba kuma wallahi bazanyi ba idan dai taƙamarki taurin kai da kafiya nace miki nine kangara idan har bazaki gaji ba nima bana gajiya tunda kema so kike ki zama kamar doki ko anhauki sai an dakeki ina nan dawowa babu daɗewa…… Yana faɗin haka ya tsinke kiran.
Ajiyar zuciya na sauke tare da goge “yar guntuwar zufar data tsattsafomin a goshina bayan Dikko ya kashe wayarshi , lallai wato duk safko na su a wajen suka kwana , kaje ka dakenin wallahi bazan daina fita ba , kai ƙarewar fitar ma ai barin ƙasar kayi baki ɗaya ko kai nace karka fita ne ko karkaje ? Ɗan rainin hankali kawai ,
Abinda ya kaini sabon layi neman wanda yasan Mamy nakeyi , kuma na samu wanda suka santa , kuma na tambayesu ko akwai wanda yasan wata babbar aminiyarta amma ta ɓace kuma ni bansan sunanta ba amma nasan shaƙiƙiyar Mamy ce sosai shin ko akwai wanda yasan aminanta , lissafi akamin nace to sun san wacece aka kwana biyu bata nan ? Sai sukacemin *Raga* ce , nace tun yaushe basu ganta ba ? Lokacin da suka faɗa yayi dai² da lokacin dana san tamin waya cewa inyi sauri na samu Binna za’a kashe shi.
Ina ne iyayenta suke ne ? Na tambaye su amma sai sukacemin gaskiya Raga babu wanda yasan daga inda tazo , wata tace amma naji ance bata lafiya tana asibiti , dana tambayi asibitin cewa sukayi gaskiya basu san asibitin ba , nace to waye yace musu tana jinya a asibiti ne ? Sai sukacemin gaskiya jinyar sirri takeyi , na nemi sanin asibiti sai sukacemin wani karuwanta ne kaɗai yasan inda take , wato kamar wanda suke iskanci dai , sai anjima zaizo nima kuma anjimar zan koma , matar data tunkari mutuwarta saboda ceto rayuwata saina ganta kuma sai naje babu wanda ya isa ya hanani fita ,
Dikko daga kan Sultana wurin Jiddah wayarshi ta sauka me yasa wata ta kwana gidanshi bada izininshi ba ? Ko an faɗa mata gidanshi gidan gwamnati ne ? Ita har ta isa ta daki ƙirji tayi iskancin data ga dama ba tare da saninshi ba ? Shike aurenta ko itace take aurenshi ne ? Daga yau idan Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida sai yaci ubanta sakarar banza wacce ƙwalwata ke ƙallon gusin…..
Jiddah tace Yaya ni kwalwata ke kallon gusin ? Dikko yace to akwai wacce nake magana da ita bayan ke ? Aike inama tantama anya kina da ƙwalwa a kanki ? Sakarar banza saboda wannan surutun banzar naki sai kin wahalar da rayuwarki , cikin kuka tace Yaya baki zakaimin ? Ba baki zanyi miki ba Jiddah surutunki yayi yawa gaki baki da sirri ko kaɗan , tou wani abu akace maka nayi ? Wallahi babu abinda akace kinyi sanin hali ne yafi sanin kama surutunki na sani zama ɗaya sai kin warwarewa mutum komai na rayuwarki anyi mutum babu sirri ina ma amfanin halinki da Allah ,
Wannan Mardiyya da kike gani sai tayi cinikin ki a gaban idonki ta sayar dake , Yaya wani abu tace wai ? Babu abinda tace nasan ke ba’a sakaki a kwana ba kinyi surutu kamar kamun hauka bare ita kuma mai wayau ta sakaki a lungu taita dukan cikinki kina bata labari , tunda Umar yacemin a gidan ta kwana nasan yau kin kwana ɗimi { surutu } wai anyi mace babu aji haba Jiddah wasu matan kamar ka biya kuɗi ka siya magana a wurinsu ni gaskiya bana san mace ba aji ki kama kanki tun kafin inyo miki abiyar zama….
Kishiya zakamin ? Tabbas wallahi aure zanyi kuma dana dawo zanyi shi in Allah ya yadda , kam bala’en nan ni zaka ma kishi ? Dikko yace tabbas kuma babu gudu babu ja da baya aure fa babu fashi ko a yadda ko kar a yadda idan dai har banyi auren nan ba tou ki tabbata mutuwa nayi……… Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.
Dikko yana kashe waya Jiddah ta kira Momy ta fashe da kuka , cikin tashin hankali Momy tace me akayi miki ne ? Momy wai Yaya aure zai ƙara , Momy tace ƙarya yakeyi babu auren da zaiyi , cikin kuka Jiddah tace wallahi da gaske yake duk abinda yayi rantsuwa akanshi ba wasa yake ba Momy tabbas aure zaiyi , Momy tace wace ce zai aura ? Jiddah tace Momy ban sani ba kuma yace min wai kar Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida bakiji zagin da yayi min ba har cemin yayi ƙwalta tana kallon gusin , Momy tace gidan banza gidan wofi gareshi har kema baki sake kwana ki tattaro kayanki ki taho , Jiddah tace Momy cewa zaiyi nayi yaji kuma kinsan bazai ce in dawo ba , Momy tace ki barshi dan ubanshi zai dawo ya sami ki taho , kamar dai Jiddah bata yadda ba amma ƙarshe dai ta haƙura Momy ta turo driver ya ɗauketa su Jiddah an sauka a gidan gwamnati.
Misalin ƙarfe 12:30pm na fito harabar gidanmu zanyi aike , Ashiru na gani shida wasu irin tiƙa²n mutane harda waɗanda suka zauna dani a goruba lokacin da Dikko ya saceni a wurin bikin birthday ina , shima ɗayan na sansa Dikko yaje dashi anguwarmu ranar daya takamin mage wanda nace jikinshi har wani mai² yake saboda girmanshi kamar an shafa mishi mai , ashe Ashiru ɗan ƙarami ne ma akansu , nafa firgita da ganinsu amma saina basar na kira mai ba filawowi ruwa na aikeshi , zan juya naji suna cewa aiko mun kamashi ba’a nan zamu dakeshi ba tafiya zamuyi da ɗan iska , ji nai cikina ya juya ƙulululu irin kukan nan da yakeyi idan yaji tashin hankali , da sauri na fara tafiya saboda wallahi basu da kyan gani naji wani yana cewa kun gane karmu daki Yazeed muyi masa kashedi idan mukayi saurin dukanshi mai gida zaice mun daki abokinshi kawai dai mu fara worner shi idan baiji ba sai muci uwarshi kawai.
Da gudu na shiga cikin palo har ina faɗuwa da sauri na miƙe nayi cikin ɗakina a tsorace , Kaka ma kanta da take zaune tamin magana bana jinta , ina shiga ɗaki wayata na ɗauka na fara kiran Yazeed babu ɓata lokaci ya ɗauka babu ko gaisuwa nace masa su Ashiru suna nemanka zasu dakeka fa , murmushi Yazeed yayi tare da cewa ki kira DK ki faɗa masa cewa yaranshi su fita hanyarki dake dani idan ba haka ba zaku samu matsala keda shi , nace ai nima yace zai dakeni ne idan ya dawo , Yazeed yace ba komai faɗa masa haka kawai , ba tare da tunanin komai ba na katse kiran Yazeed na kira Dikko.
Shima babu wani ɓata lokaci ya ɗauka nace Dikko ya ansa da na’am yaja na’am in a cikin murya irin ta sakakkin “ya “ya nace kaga yaranka su fita hanyar ni da Yazeed idan ba haka ba dani dakai zamu samu matsala , murmushi Dikko yayi yace wannan ba tunaninki bane yarinya ashe har yanzu kina wasa da mahaukaci to ki sani da abinda zakiyi da kanki da wanda aka sakaki kiyi komai naki na sani kuma ni halinki da rayuwarki sai in rubuta littafi akanki ,
Cikin ɗaga murya nace to me yasa suke binshi me yayi musu ne ? Murmushi mai sauti Dikko yayi tare da cewa bana cikin yanayin faɗa yanzu amma ki bari idan ina fushi saiki taɓoni ko kuma ki bari idan na riƙeki ina baki wahala ki tambayeni anan ne zan baki ansar tambayar da kikemin zararra kawai dake , kaine zararre , ai ni dama tuni na zare , Dikko yanzu me Yazeed yayi ma yaranka ne ? Duk abar maganar zare².
An mata yarana kenan wanda nakan ɓata musu a ko wane lokaci kuma sukeyin haƙuri dani , na saka baƙin ciki a zukantasu yayin da su sukeyin farin ciki , kuma suyi haƙuri basa zuciya dani , kinga su kansu suna kishina tun kafin ni inyi kishin kaina , suna jin baƙin ciki tun kafin ni inji baƙin ciki , suna tayani kishinki tun kafin ni nayi kishin naki , sunji baƙin ciki na samun kishiya a soyayyarki tun kafin ni mai san naki nayi kishin rabamin zuciyarki da kikayi gida biyu , ni ɗaya nake ko a gidanmu kuma duk zuciyar macen dana shiga bana gogewa har abadan duniya amma ke har kina tunanin jinjina soyayya ta data wani Yazeed , ni zaki ma soyayyata kishiya ko ? Hmmm idan har na barki kin huta dai² da saƙon ɗaya da tunanina kice ba Dikko nake ba. Yana faɗin haka ya ajiye wayarshi.
Cikin tashin hankali na sake kiran Yazeed bayan ya ɗauka na faɗa masa Dikko yace bazaiyi haƙuri ba , Yazeed yace sake kiranshi kice masa yayi haƙuri yaranshi su fita hanyar Yazeed , nace tou , wayar Dikko na sake kira amma sai bai ɗauka ba , nan fa na samu aikinyi ,
Har aka kawomin saƙon dana aika a siyomin ban daina kiran Dikko ba , ganin bazai ɗauka ba yasa na kunna data ta yana online kuwa kenan yaga kirana ɗauka ne bazaiyi ba , voice note nayi masa cewa Dikko kana ganin kirana bazaka ɗauka ba , ya gani kuma na tabbata yaji amma bai bani ansa ba ,
Whatsapp video call na kirashi ya ɗauka yana kwance saman gado yana cin cingom cikin salo mai ɗaukar hankali , murmushi nayi dana ga fuskar Dikko a kusa dani nace mutumina kaine a kwance haka ? Wani irin kallo yayi min amma baiyi magana ba , cikin sakin layi nace Dikko kai kana da kyau sosai wallahi kana burgeni matuƙa , har yanzu idonshi akaina yake amma baiyi magana ba yana kallona cikin wani irin yanayi , Dikko kayi haƙuri don Allah tsoki yayi tare da cewa ai kina so dai yarana su fita harkar Yazeed ko ? Nayi shiru , tunda kina san Yazeed na bar miki shi kuma insha Allah duk wani wanda ke ƙasana bazasu sake rabaki da Yazeed ba , na haƙura dake An mata na fita harkarki kuma ki goge number na a wayarki nima zan goge naki kowa yaje yayi sabuwar rayuwa ,
Dan kinga ina sanki zakiyi tamin wasa da rayuwa to na daina sanki ko diamond ce ke na haƙura dake bana so aje akaima Yazeed , yana faɗin haka ya kashe , wani irin tashin hankali naji kamar an tsinkemin jijiyoyin lumfashina , musulta irin tashin hankalin da naji akan kalaman Dikko bana iyawa , cikin kuka na sake kiran wayar Dikko amma yaƙi ɗauka wayyo Allahna kardai mutumina da gaske yake ?
Murmushi Dikko yayi da yaga Sultana tana ta kiranshi yace haba An mata ai tuni kin faɗa tarkona na , tuni na dana saka miki maitata a zuciyarki , murmushin mugunta yayi cewa bari in barki saina gasaki dayi miki rowar muryata nima yanzu zan ɗana irin iskancin da kikemin idan kikaji azaba dana dawo ke da kanki zakiy ta haɗani da Allah muyi aure , “Yar yarinya kawai dake kin maidani abokin wasanki , da girmana kin maidani kamar ƙaramin yaro in biye miki inta sakin layi ko girmana baki gani haba An matana so hauka ne …..?
Tun wurin 12 da wani abu nake kiran Dikko bai ɗauka ba har zuwa yanzu wurin 3 na kasa daina kiranshi kuma ko tausayina Dikko bayaji yaƙi ya ɗauka wayana ni kuma na kasa haƙura ,
Saida aka kira la’asar na ajiye wayar naje nayi wanka nayi sallah na shirya na fita daga gidan na nufi sabon layi…..
25/10/2019 ????????
PLS CLICK ON THE ADS