AHUMAGGAH 19

_The love triangle_
_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
*Argumentators and quesers kuna mugun sani ni nishadi,jiya saida na zauna kasa dan dariya????Ahumagga Arguments yasa ankasa gane cewa shin America a london yake koko UK a US yake tsaban ana so khal ya hadu da bahi????..so much love my fans kuna nishadantar dani aradu????.*
_1⃣9⃣-America meets london♡._
Da kaamil ya fada ma junnut khal ne zai kaita shopping sosai taji dadi aranta,dan haka 5/00pm dai dai na yamma suka nufi
Shopping mall su uku.
Toh Dan ma kar su takura shi sai yace kowa ya tuka motar kansa,3 cars ne suka bar compound din zuwa wata shakikiyar shoping store.
Babban International shopping store ne dan awajen babu inda basu tura kaya delivery kuma babu abunda zaka nema ka rasa.
She was soo happy
Tun Kafin su isa tayi waya da hilda yafi sau dari
In kaga yadda take zumudi ita kadai tana murnan khal ya kawo ta shoping zakace ba ita bace take cikin bacin ransa adazun
Suna parking kowa ya fito,dukan su da dark googles a idanun su
Tunda suka shiga ciki kowa na dube duben abunda ya masa,shikam Hannun sa na nade aljihun sa Yayi shiru sai binsu yake yi kamar zombie
Gashi hilda ta bata shawaran kar ta sake ta bar site dinsa,junnut tana so ace ana kallon su daga nesa asan shi nata ne,ita nashi ne amma tana gefen san ma sam sam bata gane ina hankalin sa yake ba
Har ta gaji ta ja jikin ta.
Suna ta zagayawa har ita tayi dan nesa da su chan kaamil yaga toy gun,bindigogin wasan yara na ak47 guda biyu,cikin son yasa shi magana
Sai ya dauko ya jefo masa daya shima sai ya cabe..
Kaamil yayi pose da daya a hannun sa,tun kafin khal din ya juya kan nashi gun din ya seta masa bindigan kamar wanda zai harbe shi
Junnut wangale baki tayi tana binsu da ido dan Tasha mamakin ganin yadda sukayi rige rige wajen nuna kwarewa da nuna ma juna bindigan kowannen su yana cewa dan uwansa.. “Freeze”!
Kaamil sai yaci fuska kamar da gaske,chan
Daga bisani duka suka fashe da wani sassanyar dariya
Hakan ya mugun bata mamaki Sai ta dakata tana satan kallon su basu wani lura ba.
Aje gun din a hankali khaldun yayi yana murmushi yana daga hannu sama alaman yayi surrender suka cigaba da dariyar
Cikin wasa yace ma kaamil
” pls Dont kill me captain you knw i cant live witout u”
Kaamil na rike da gun din yayi kwafa yana murmushi mai dumbin tasiri,yana tuno da wani al’amarri wanda daga gani yana sa shi kuka in ya tuno.
Fairly emotional ya furta i cannot kill you general..u tot me how to hold it…,sai ya shiga juya kan bindigan da yatsun shi yana cewa Ai bindigan ma ba bazata harbu ba in har kaine.
Shi dai khal bai sake magana ba
Sai kaamil ya aje gun din shima suka cigaba da murmushi suna tafiya side by side kamar yan tagwaye,.kaamil ya dan dube sa cikin kulawa yace,sa’ood nayi kewar ka sosai…har ban san ya zan fada maka ba..
…khal ya dada fadada murmushi yace baga mu ba?
Kaamil Yace yeah and i wll spend the night yau kam….agefen ka.
Junnut dake makale a baya tana jin haka Sai gata ta karaso kusa dasu,ba yabo ba fallasa tace ni kadai na koma gida kenan?….Gaskiya bazai yuwa ba,sukayi murmushi
Khal baice komai ba
Kaamil ne ya bata permission
Suna cikin za gayawan lokacin yamma ya farayi sosai waje ya kara rufawa,kaamil da junnut suna counter ana packaging kayan data debo dayawa iya son ranta duk dantayi show up ma hilda wai dan Karta raina ma khal din ta Aji.
Shi kuma khal yana baya wayarsa yayi kara sai yana dan zagaye yana amsa wayar charaf ya bi ta wani pink and white shelves na kayan mata
Duk abunda yake wajen pink da white ne,abubuwa kala kala na yan mata sai wanda ka zaba.
tsayawa yayi yana kare musu kallo wayar na kunnen sa yana sauraro,Wasu shegun box yagani wanda suka dauke masa ido an rubuta girls problem an manne edges din da silver glitters so majestic.. sai ya dauka box din slowly ya bude ciki yana kallo kayan make up ne na kece raini babu abinda babu aciki,kusa da shi kuma wasu manyan clay brown teddy bears masu angry and naughty faces abun dariya.
Haka kawai suka bashi sha’awa sosai gashi daya sa hannu akai babu wance ta fado aransa sai yarinyar daya fi tunawa a kullum in ya rufe idanun sa.
I really want her to have this. .Zuciyan sa ya furta yana zaro wasu park din chokolates dake wajen all togther ya hada.
Yasan shi ba irin mazan nan masu boye boye bane dan haka ya kira attention din service yayi marking abubuwan da yaga sun masan aka shiga tarkatawa ana binsa da su
Lokacin su junnut har an gama zasu fita tana ta lekawa ko zata gansa sai bata hango sa ba
Ya gama call din amma Daya ga hakan Wayan sa ya mayar Ya sa a kunne dan haka kaamil yace mata suje waje kawai kafin ya gama ya karaso
Kayan daya saya duka duka sunci 2 packages manya amma anyi packaging dinsu ne in form of Oder bags dan haka komai a killace yake kamar weding gifts.
Yana fitowa sai ya samu har sun fara driving sun gano shi lokacin yana shiga car din sa shima
Amma along the way sai babu shi babu mai kamannin sa.
Har suka kai gidan after 20 minutes
kaamil yana can sama a dakin sa junnut kam tunanin ta yana kan hanya ne,1hr shiru zai iso ne bazai iso ba sai gashi har dare ya rufa babu shi babu alaman sa
Abun ya dame ta ta same kaamil da complain
A tare suka kira layukan sa amma shiru baiya shiga
Haka kaamil ya lallabata da cewa khal bazai taba kwana awani waje ba zai taho anjima.
Haka dai har tayi bacci ta farka bata gansa ba,da asubahi ma zaune take kanta kife da gwiwa abakin gado
Ta rasa meke mata dadi,Zuciyan ta cike da cunkushewar tunanin kar dai dan tace zata kwana agidan ne yaki ya dawowa.
****
Bangaren bahiyya kuwa By 8.am in the morning yau basu da komai a schl sai da yamma by 4 shidin ma extra class ne.
Dan haka as early as posible suka bude eatry lounge dinsu suka fara aikin dafe dafe cikin nishadi da jin dadi
Simple snacks drinks,smoothies cappucinos da duk wani launin coffe da ice cream duk zaka samu awajen
So most of wayanda
Suke zuwa musu inba yan african countries masu cin nigerian dishes ba to samari da yan mata ne students masu qwiuyan girki da son shakatawa
Yau Da ciwon kai bahiyya ta tashi dan haka batayi aikin serving oder ba
Sai ta tsaya tana dafa coffe da sauran kananan abinci jasmine kuma tana serving oder.
8.40 dot Wani mutum ne ga shigo eateryn sanye da plain riga baki mai v neck ta dan kama shi kanshi sanye da hular facing cap black mai shegen kyau….
Wasu sun dan kalle sa,wasu daga Dai daikun customers dake wajen kuma basu kula ba suna harkan gaban su
A last seat din dake facing end wall ya daga wani high school kid ya zauna inda babu wanda zaiga fuskan sa face wanda zai kawo masa oder
Yasmine ne tazo a madadin bahiyya sai ta ajiye masa venue palate agaban sa tare da cewa sir pls place ur oder tana yi tana duba ko zata ga fuskansa da kyau amma bata gani ba..
Dama Sun saba ya wancin customers har counter ake binsu ayi oder wasu ma daga inda suke zaune zasu bayar amma ganin shi ya dan banban ta shiyasa abun ya bata mamaki sosai.
Shikuwa Canko su kawai yayi Baiyi browsing ba
Yace ta kawo masa plate biyu da tea guda biyu
Cikin ranta She was like what?,ta juya gabar da yamma
Abun ya dada bada jasmine mamaki
gani tayi shi kadai ne awajen tambayar kanta take how can he manage 2 plates and 2 teas?
Toh abunka da babu ruwan ka da rayuwar wani sai ta juya Ta tafi da sauri
.
Tana isa serving board kuwa gulman sa ta fara yi musu,dija ta ce kinga face dinshi? Tace ahh,shine kuma zaici abinci har plate biyu!
Kar dai venom ne ya shigo mana kinsan shi da son cin abinci..,oya kuku go an check in shine mu gudu kar ya hada da hanjin mu ya cinye..cikin raha dija ta fada
Yasmine kuwa fargaba abun yasa mata,tace ah ‘a nidai bazan iya komawa ba ni tsoro ma nakeji,he dint really show his face amma dai inaga mutum ne
She was bit scared
suna ta hiran su
Suna hada abincin bahiyya batace musu komai ba
cikin ranta take wondering kowaye wannan din haka kawai take jin wani iri yau aranta.