NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 2

_*♡AHUMAGGAH????*_ 
   _A nigerian historical fiction_           _*WATTPAD SURAYYAHMS*_   
  _Brilliant writers association_ 
_2⃣-the cross roads♡_
Cikin daren A daddafe muka iso gida,samu mukayi abbu ya riga ya dauke motsi amma kuma numfashin sa bai dauke ba.


A gefe na ajiye maganin sa duka muka zube gwiwar mu agaban sa muna jimanta yanayin sa he is kind of stable now  

nan na fita na shiga hade ruwan magani tare da ruwan zafin da junnut zata dan tsaftace jikin ta ita kuma tana dakin tare da abbu tana tallafa masa.
 Babu abunda junnut take yi sai hawaye.

Abbu yayi luiii da shike ma bayada karfin magana sai ido yake binmu da shi har muka gama duk abunda zamuyi.

Anan Bamu kama hanyar gari ba sai da na tabbata junnut tayi wanka ta dan kimtsa kanta kafin na gyara na abbu kwanciya na fito na rakata har layin gidan su  sannan na dawo.

Cikin wani irin yanayin tunani nake tafiya,babu abunda nake tunowa sai alkawarin mu da junnut da yadda komai zai zamto min daga gobe..

Shekara ta goma sha hudu ne kawai a duniya dan haka bansan ko hukuncin dana yanke dai dai bane ko ba dai dai ba.

Washe gari Da safe Bayan na hada ma abbu na maganin sa na bashi ya sha,sai nayi zamana gaban sa na tsura masa idanu na bance uffan ba…,na dade a haka ina tunani dan a daren jiya ma ko tunanin kiftawa baizo min ba,yanzu ma kallon shi kawai nake ina tuno irin rayuwar farin cikin dasuka bani shida ammuh a lokacin da bankai haka ba  

Tabbas ummah surbajo tana da ilimin da zata sama min mafita game da rashin lpyar Abbu..
So nake abbu na ya warke sosai ya rayu koda babu ni atare dashi…

Sanyin safiya na kan busowa na fito nayi alwala nazo kan abbu nayi masa karatun qur’ani dai dai inda na kama..

Chan naga Abbun Ya farka ya bude idanun sa amma ko tashi da kyau bazai iyayi ba.

A Yadda na saba wanke shi nayi masa alwala haka nayi ta taimaka masa har yayi sallah…

Dan kadan ya sake shan maganin sannan ya kwanta yana kallo na,sosai yanayin sa ya dada rikita ni..

Gani nake idan ya kwanta baccin hala bazaima tashi ba tsaban wahalar dayake sha da jikin nasa.  

 Dana ga kallon
 nasa yayi yawa
Chan sai abun ya fara bani a kwakwalwata ko dai wani abun yake bukata ne?sai nima bance komai ba,inda yabi da ido nake bi sai banga me yake kallo ba face ni,sai na tashi tsaye Ina dan dube dube ko zanga ya min alama..
 Murmushi kawai yaso yayi amma Wani tari sai ya shake shi,karasowa jikin sa nayi a dame nace sannu abbuh…
Tarin bai tsagaita ba sai naga abbu ya ruko duka hannaye na

Yace bahiyyah,jiya a ina kikaje kika samu magani?

KAllon sa nayi A hankali na furta “jeji”,wani runtse ido naga yayi alaman baiso yaji hakan ba amma baya da karfin da zai yi scolding dina..
Yace ke da junnut kuka je ko?
Toh meya faru da ku  naga jini a rigar ta,ke kuma har yau idanun ki basu washe ba..shin bazaki fada ma mahaifinki damuwar ki ba bahiyyah?

Yadda yayi maganan sautin muryansa na karkarwa yasa  Sai nayi shiruuu tsawon lokaci kaina a kasa bance komai ba.

Muna cikin haka aka yi sallamah agidan mikewa nayi na fita abbu na bina da kallo mai dauke da alaman tambaya.

Dogaren sarki nagani,yace Aika ne daga gidan sarki modibbo akan cewa naje cikin gaggawa 

Abbu dai bai sake tanka ni ba Nan na shirya kaina na nufi gidan su junnut.

Junnut ce take gayamin cewa a jiya data shigo gida cikin dare ta cikaro da tashin hankalin  ummah surbajo sai ta tutsiye ta  da fada har da mari har sai da tayi mata karya akan abunda ya faru sai dai ta juya kan labari ya koma kaina kamar yadda muka shirya.

Kenan ummah surbajo ta rike cewa nice akayi wa fyade ba junnut ba, kwata kwata batason abunda zai shiga rayuwar junnut anan gaba dan haka ta sata agaba akan maganar.

Dan akan junnut umma surbajo bata da sani bata da sabo.

ummah surbajo gani take idan ta kyale maganan har ta bada junnut goyon baya ta boye ma sarki,toh hala wani abu zai iya biyo baya.

junnut tace min yau din ma ita tasaka ta agaba akan dole sai taje ta fada a gaban sarki modibbo,da taki data so haka har magana yaje gaban sarki shine aka aiko a dauko ni.

Daga nan Bamu wani bata lokaci ba muka kai kanmu gidan sarki modibbo muka aiwatar da plan din mu na cewa ni Bahiyya nice Ahummaga suke riske ni ba junnut ba..
Sai muka juya kan labari muka shirya duk yadda zamu samu hadin kansu.

Toh Kamar yadda aka saba jama’a sun taru sarkin matsafan da aljanun sa duk sun hallara za’ayi min hukunci.

Ganin mun yi tsuru tsuru muna rarraba idanu salon marasa gaskiya ga idanun mu kuma cike suke da hawayen tsoro sai yasa basu kulaba,tashin hanklin mu yasha masu sarki modibbo kai har yasa ba a bata lokaci wajen zurfafa bincike akan lamarin ba aka yanke hukunci.

 A wannan lokaci koni bana kuka da jimamin da kawata junnut keyi,Abbu na chan gida bai ma sanda haka ba.

Anan fada kuma Sabida babu mahaifina awajen sai aka bani sharadin awowi biyu da cewa na tattara kaya na na bar garin an shafe ni a zuriar su,sannan ina gani boka da aljanun sa suka gama tsubuce tsubacen su akaina ina jin su bance uffan ba. 

A Duk ilahirin jinsin zuriar fulani dake fadin jejin Nan basu kai kimanin dubu daya da dan dori ba dan haka kusan kowa yaji abunda ya faru dani 

Wasu sunji bakin ciki sosai,wasu kuma Sunyi murna musamman yan mata sa’oin mu da suke ganin  nice matoshiyar sa’ar su wajen samun mijin aure.

Junnut kam gaba daya sai ta birkice,itakadai ke rike dani tana jimami har muka kai kofar gidan su.

Muna Isa kuwa na samu har bakin nasu sun zo wanda zasu tafi da ita chan birni..
 Dana shigo gidan ma,sanda
Ummah surbajo tayi min fada sosai akan abun da ya faru damu jiya nida junnut din

Tace duk gangancin mu ne ya jawo mana.

Don junnut bata manta marin da ta karba ajiyan data dawo cikin dare jikin ta duk wani iri ba…sai nayi  tunani wai don ma junnut batace ma ita akayi ma fyaden ajiyan ba kenan?ashe kuwa da ta fada gaskiya hala ummah surbajo ma kawai zata iya kashe ta har lahira da fada.

Haka mukayi tsuru tsuru muna bata hakuri,da shike ma ummah surbajo tana da ilimin bature da yelwatan tunani Daga baya Sai ta shiga tausaya mana gaba dayan mu.

Dataga inata kuka sai da tayi kusan sani zazzabi da nasihan ta,aganin ta duk tsumayin rabuwa da aminiyata ne ya kawo ni gidan nasu a yanzu da bani da wata rayuwa mai daraja a idon kowa agarin.

Hakuri ta bani sosai tana cemin
Allah ya qaddara nan ne karshen gabar kawancen ki da junnut.

Kema yau zaki bar cikin wannan jinsin ga Junnut itama zataje chan nahiyar da ta dubi kudu wato chan persian empire asalin cikin kasar iran wajen dangin mahaifiyar ta.

A Cewar ummah surbajo,asalin mahaifiyar junnut jinin sarauta ce ta wani babban daula zuriar sarauniya DAWLAT KHATOON dan haka su kayi alkawari zasu rike rayuwar junnut a matsayin yarsu ta har abada gashi kuma yau sunzo cika alkwarin su.

Ita kuma ummah surbajon zata koma da zama na dindin a kasar nigeria chan cikin jahar kaduna.

 Muna cikin saurarar ummah sai ga umaru dan mashayin garim ya taho  gigice ya zube gaba na.

Yace baahi,ki taho,baba ahmadu mai magani…yana magana yana hako yana nuna hanya
A take naji yawu na ya dauke chak kaina yana wani iri bugu…
Nace mene ne,ina abbuh?

Su umma da junnut duk sukayi tsaye suna kallon shi da fuskan razana kamar yadda na ke binshi da kallon nima

Nan umaru ya sanar dani cewa ai yana tahowa ne yaga abbu na akasa kan hanya yana ta aman jini

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button