AHUMAGGAH 2

Runtse idanu na nayi,dama saida jiki na ya bani cewa abbu zai iya cewa zai biyo ni yaga me na ke cikii
Ban tsaya sauraran komai ba,na sa gudu na fita agidan junnut zata bi baya nah ummah surbajo tayi sauri ta finciko ta tana cewa ke wai ina zakije? Bakijin magana ko
Maza wuce kije ki shirya yanzu zaki tafi, tace ummah zanbi bahiyya ne,sai bata kulata ba kuka junnut ta fashe da shi tace ummah Abbu baida lpya sosai dan Allah ki barni naje amma haka ummah surbajo taki sam tayi mata shiru junnut kuwa ta cigaba da kuka har saida ummah surbajo dan kanta ta gaji tace toh taje ciki tayi shirin ita zata bi bayana taga meke gudana kafin nan junnut ta amince ta motsa.
Nikuwa ina isa na haura kan abbu duk yayi wani iri,ga datti da kuran kan hanya ya shafu akan rigar sa yana ta habon jini.
Umaru ne ya taimake ni muka koma da abbu na gida,shima bai wani tsaya ba yayi tafiyar sa ya barni da Abbun a hannu a tsakar gida.
Zama nayi a gabansa shi yana daga kwance,har ya dan dawo hayyacin sa ya bude idanun sa ya kalle ni..,nan ya shiga yana tanbayata meya kaini gidan sarki.
Nikuwa a Duk tunani na nabari cewa yau komai yazo mana karshe tun da zan damka shi a hannun ummah surbajo akaishi birni ayi masa jinya,hakan yasa kawai na cije na fada masa abunda ya faru batare da yasan gaskiyan sirrina da junnut ba
Sai dai Har nagama nayi shiru banji ya ce uffan ba,hasali ma Idan ina maganan abbu kallo na kawai yake yana kada kan sa slowly nikaina bansan meyake tunani ba.
Sai chan naji Abbun Ya sake nanata min tambayar sa yana cewa bahiyyah Ahumaggahn ne suke riske adaren jiya?
Cikin dauriya da fargaba nace mashi eh..
Juya kanshi gefe yayi,ya barni cikin zullumi na tsawon mintuna ashirin
Chan Yace min yata bahiyya!
…kiyi hakuri da rayuwar duniya ki zama macen kan ki…,kar ki taba zubda kimar ki da darajar ki,sannan kar ki ci amanan kowa.
Mamakin kansa yasa na dago kaina na dube shi sai naga bama kallo na yake yi ba
Yace
Ni ahmadu yau naso ace qaddarar mu ta saba haka don kuwa har cikin raina nake jin ke din wata ce a duniyan nan kuna bazan taba yarda da sabanin haka ba.
Da Ahumuggah, sarki modibbo da aljanun sa duk sunyi karya su salwanta ikon ubangiji acikin rayuwar ki.
Kije inda zakije aduniyan na kuna kiyi aikin ki na kwarai,halal dinki kawai zaki nema bahiyyah,duk abinda ya saba haka kibar shi har abada..
Wani fat fat Zuciya ke bugu dan Dagowa nayi na kalle shi cikin sanyin jiki nace toh abbuh …
“Kallo na shima yake yayi sai TAri ya dan turke shi duk da haka bai fasa ba yace
Kinji abunda na fada miki ko?
Nace ehhh naji Abbu,mikewa tsaye nayi da sauri ina shiri shiga daki zan dauko masa magani..
Sai naga ya ware Hannun sa ya mika min,sai nima na riko shi tarin na dada hauhawan sa a hankali…sai naji ya dada rike ni dam dam duk yunkuri da zaiyii kuma tarin sai ya kara karfi kamar yadda ya ke kara karfin riko ni.
Idanun mu a take suke rine ni dashi sukayi jajir muna kallon juna anan abbu Yace min bahiyyah,muryana na rawa sosai nace naam abbuh …yace baki taba min komai na bacin rai ba a duniya
,shin haka zamu rabu bazaki fada min gaskiyar lamarin ki ba?…murya na na dada rawa na firgita kadan sai
Nace abbu?man take ya lura da cewa maganan ne yayi min nauyi abaki
Sai Yace toh shikenan bahiyyah ta
Na hakura Allah ya miki albarka daga nan,..bai sake kallo na ba ba sai aman jini daya shiga yi.
Kuka mai sanyi na fashe dashi,nikadai ina kanyi kamar wacce aka ma bishira da mutuwa,abbu sai ya kau da kansa bai ce dani uffan ba
Sai chan danayi zuciya ta tayi sanyi sai naga kamar bazan iya ba kawai sai na fara bashi asalin labarin abunda ya faru tsakani na da junnut ajiya cikin dare
Tun da na fara abbu yake wasu irin silent hawaye sai yayi shiru ya tsura min idanun shi labbansa dauke da karamin murmushi..
Hannun shi daya ya saka ya a shafo kaina dik jikin sa na rawa sosai
Yace ai dama nasani, Allah bazai taba bani kunya ba domin kuwa Allah baya tozarta bawar shi mai masa biyayya bahiyyah.
Da ace Jiki na ya bani cewa dagske Ahumaggah sun salwantar da rayuwar ki sabida ni da tun bayau ba na bar duniya nan..
Hakan bai faru ba shi yasa najira naji gaskiyan lamarin ki daga bakinki ki.
Abbu yace”Kinyi sadaukarwa mai girma bahiyyah ta”
Junnut ma yata ce bazan so ace hakan ya same ta ba,kuma naji dadi daya kasance babban burin ki ne masamu lpya na rayu awani wajen koda baki tare dani.
,…Allah ya sa sadaukarwan ki ya zamto sanadiyar wanke hakkin junnut akaina wanda halin rashin lpyata ne ya jawo mata wannan mummunan qaddarar a cikin rayuwar ta.
Allah ya bata abunda za taje nema..
Nikam babu abunda nakeyi sai kuka,zuciya cike da kaunar mahaifi na da kyar na iya tsagaitawa har nace ameen.!
Yau Ji nake kamar nafi kowa sa’ar uba a duniya , dan kuwa abbu is the most simple and most understanding father a duniyn nan..Duk da haka hakuri na shiga bashi ,amma sai ya jawo ni jikin shi ya rungume ni
Sosai.
Tarin ne ya sake
Addaban sa amma bai sake ni ba.
Yace na barki da duniya bahiyyah ta amanan kanki yana hannun ubangiji na
Albarka ta na tare dake Kar ki manta da wannan
“Kar ki ci amanan kowa don nasan da tarbiyan dana baki zaki iya zama da kowa..!
ke da junnut tamkar wani haske ne,dan haka kar ki sake ki bada fili ma shaidan har babban aminiyar ki ta dawo abokiyar gaban ki”..
Karshen maganan abbu na kenan sai yayi kalman shahadar sa ya bar duniyan mai gaba dayan ta..
Naji bakin ciki marar misaltuwa sai dai Ban iyayin wani kuka ba sai hawaye da dan addu’oin dana koya a chan islamiyar su ummah surbajo
Rabuwa da mahaifi irin nawa da zafi,anma Hakuri da juriya na wajen Allah na mika gaba daya,na kuma roke shi sai na samu sauki.
A daddafe naje na fada aka zo aka suturta abbu aka kaishi gidan sa gaskiya.mafi akasari daga mutanen garin mu sun dada jin tausayi na aransu
Tsegerun jiki kowa sai cewa sukeyi nayi na bar garin,acewar su tsinuwar aljanu dake kaina shiya kashe abbu na.
Ina daga tsakar gidan su junnut na rafka uban tagumi ina hawaye,sai naga an shiga daki da ita,anan suka gama duk wani maganan su banji komai daga ciki
A Ciki har da maganan cewa ummah surbajo zata tafi da ni kasar nigeria nan da cikar awa biyun da sarki suka bani akan na bar garin.
Junnut ne ta sa ta dole ta aminta da hakan,Sai dai sanin halin sarki modibbo ya sa surbajo ta shiga fargaban rike ni
Damuwar ta ba dukiyar da zata bayar ba,kar muje dani na zamto mata fitina tunda anriga an jefe ni da bakin aljanu.
To lokaci ya kure kuma Babu wa’adin warware maganan sosai don haka,naa amince da shawaran ummah surbajo
Buri na kawai ta fitar dani daga nan yankin lami lpya
Toh da su junnut suka tafi
Umma surbajo sai da ta dada jadadda min cewa a zamu tafi taree amma ni bazan zauna da ita ba sai dai na nayi gaba na kana rayuwa ta nikadai acikin garin kaduna nikadai
Haka rayuwa ta tsara min wannan ranar kuwa bana taba mancewa da ita a kundin tarihin rayuwa ta
Rana ce da na rabu da abbu da junnut,nayi karya ma abbu kuma na bar garin da gawar mahaifiya ta yake shinfide na har abada.
Tin da muka dauko hanya sai nayi shiru,har wani kwalalan zazzabi sai da ya kama ni. .
Ummah surbajo ma tausayi na take ji sosai azuciyan ta shiysa har ta fara tunanin zata kyale ni nayi kwana ukun zaman makokin mahaifi nah agidan ta..
Araina nikuma nasan junnut zata yafe min tunda ma abbu kawai na gaya ma sirrin mu kuma shima gashi ya bar duniyan nan Yau daga ni sai ita sai Allah muka san gaskiyar labarin rayuwar mu akan Ahumaggah
Daga nan Ni kaina bansan yaushe muka iso nigeria ba.
Har muka iska sauke mu a garin kadunan ban ma lura ba sai da naga mutane suna hulda da junan su gwanin ban sha’awa
Kasar kuwa akwai kyaun tsari da yelwatan arziki, uwa uba ga kabilu masu kyau da al’adu na ban mamaki.
Haka kawai naji iskan kasar ta amshi zuciya ta tafiya ta nakeyi ina bin ummah surbajo kamar dama kasata ce nigeriar.
Nan inda muka sauka anace ma sunan anguwan badarawa,gidan ummah surbajo irin duplex din nan ne mai tsafta dashike ma bata da miji mukadai ne kawai agidan babu kowa..
Yau kwana hudu da isowar mu dan Ban bar gidan ummah ba tukun sabida jikina yaki ya sake ni,a kullum na kwanta sai nayi mafarkin abbuh yana min murmushi.
Ummah surbajo kuwa a shirye take,. dan naga ta cika min alkawari na data dauka ma junnut na kulawa dani ,dan tun zuwar mu naga ta sa an kira likita dan nigeria agaggauce har gida kuma yake zuwa kaina yana duba ni
Gashi a kullum jikina sai ya tashi
Wani bin idan abun ya dame ni sai,har nakanji kamar na fada ma ummah gaskiyan lamari