NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 2

Amma kuma bana iyawa dan nakance Toh meye amfanin fasa kawai tunda nasan bazan iya dawo da abbu na duniya ba?kuma ga junnut dina zata cika burin rayuwar ta.

Iyakaci ace na rabu da garin mu ne kuma an tsine min..besides garin sarki modibbo ba asali na bane kuma ba zuria ta ba.


A Yau safiyar liitinin sai
Na farka da fargaba da wani irin bugun zuciya,domin kuwa tun asubah ummah surbajo ta fito fili tana cemin nayi na bar mata gida kar curse dina ya shafe daya daga cikiin dangin ta..

 Nikam ban wani damu ba sai na roke ta wa’adin kwana biyu tace min babu komai.

 Munyi ne akan sharadin zanje na nemi sana’a mai kyau a cikin garin koda kuwa wanke wanke ne  a kasuwa kafin na bar mata gidan ta…
Dan haka ko zama banyi ba na fita neman abunyi sai dai bnci sa’a ba

Da safen washe gari ma haka na shirya na fita bansan kowa ba Haka na dinga tsagawa cikin garin kaduna ina neman aikin da zai rufa min asiri, Mutanen kasar kuwa akwai su da tausayi,ko da bazasu baka aikin ba su fiye wulkankta mutum ba

nakai yamma ina zagaye ga yunwa ga gajiya har sai da na iso bayan gari inda karuwai ke zama kafin,Da kyar na ci karo da wata mata wanda na lura kyau na ne kawai ya dauke mata ido ba abunda nazo nema ba.

Dana mata bayanin kaina sai Tace min zata koyar dani sana’ar saida abinci (sales girl) idan na kware kuma ta ga zata iya zama dani zata barni ina kwana a shago da sauran masu aikin ta.

Naji dadi sosai sai Nayi mata godiya nace mata akan gobe zan fara zuwa aikin..

Dana zo gida na fada ummah surbajo tayi murna sosai,har tayin yunkurin bani kudin gadon junnut datamin alkwari akan jinyar abbuh amma hakan naki karban ko sisin ta nayi tafiya ta.

Bayan watanni biyu,lokacin har mun rabu da ummah surbajo na kama gaba na 

aiki nake yi gadan gadan wajen anty hanne a restaurant din ta na bayan gari.

Ni ba wata cikakkiyar wayayyya bace amma bazaka ga hakan da sauri atattre dani ba ba

 sabida ina da mugun mugun kyaun fuska da abun da ake kira kyaun jiki..

As young as i am,a shagon anty hanne idan akwai musun da aka tabayi jar aka zuba kudi mai yawa to akan banbance kamanni na

Dan wasu sunce kamanni na da pop artist Ariana grande kamar an tsaga kara ne musamman idan nayo murmushi  wasu kuma suka ce nice ma indian movie star wato aishwairiya rai sabida kalar idanuna.

sai dai ni ba farar kalar fatan turawa nake dashi ba,fari na dai dai yake da na asalin iyamuran kudancin nigeria  irin bright yellow skin mulmulalle mai haske da laushi irin marar fidda kurji ko tabo din nan.

“Dama Abbu da ammu na farare ne,dan haka na dauko yalalen gashi mai tsayi irin na ammuh,
tsayin ta da dirin jikin ta ma kai komai nata na halittar jiki ban bari ba.

Idanu na ne kuma na dauko na abbu na dan shima kwayar idansa kalar ruwan tokace irin na aishwryr,gashi thy are well rounded and sunken su dai basu yi girma sosai ba, dan madaidai ta ne Wanda tsayi da cikowar eyelashes dina ya dada kawata su ya bani wani shegen fierce look.

Nidai Na kasance wata madubin dubawa dan ko babu kwalliya nasan ni mai kyau ce.

Anan kuma kyauna ya jawo na sama mana kasuwa sosai kamar ba nice aka ce aljanu sun Tsine min ba.

sai dai bana da son cika magana, hasali ma Tsaban yawan shiru na da kamun kai yasa anty hanne ta yarda dani sosai,yanzu awajen ta nake  samun kariya da cikakken tsaro daga komai, har da maza yan iska da kuma kawayen ta karuwai yan madigo.

Anty hanne ba musulma bace anma tana da dabiar daraja dan adam, akalla dai she is in her late 40s tana da dan shegen data haifa sunan sa chris,to tunda ta haihun sai ta bar sana’ar karuwancin kwata kwata sabida tasa tunanin rayuwar dantan anan gaba.

Amma sai bata bar bayan garin ba sabida sana’ar da ta bude na saida abincin domin anty hanne karshe ce wajen iya dafe dafen abinci,wani salon girkin abincin ma koya take yi a online kuma duk iya wahalar yinsa 
Sai ta koya kuma kaga ta iya tsaf 

Sana ‘ar ya karbe ta,dan Akallah itake da babban shagunan dake ciyar da kowani mahaluki da zaizo wajen 

Dama chan Kowa yakan so abinci ta,Toh tunda nazo sai abun ya dada bunkasa,har daga wajaje daban daban ana shigowa neman abinci wajen ta,”
Tana mutun ta kowa amma
Da zaran ka nuna kai mayen mata ne sai ta bata rai ta kora ka.

dan kuwa har yau anty hanne bata gaya ma kowa cewa ni ba kowa bace illah marainiya.

Asali ma cewa take ni yar uwan ta ne nazo daga kauyen su..

Itama tana da kyau dan kuwa cikakiyar shuwa arab ce daga maiduguri amma mahaifiyar ta yar garin katsina ce.

Kamar uwa haka ta zame min,girki  da sarrafe sarrafen abinci babu wanda take koyarwa fiye kamar ni.

Idan muna aiki tare sai Tace min kar nayi samari har sai na tara kudi na nemi ilimi mai zurfi..

Hakan kuwa har fara saka wa araina sai na zage sosai ina aiki,ita kuma tana aje min kudin har na koma wanu makarantar gwamnati ina dan cigaba da karatu na.
A ss1 suka sake maida ni,amma danayi term daya aka gane ina da hazaka sai aka cilla ni aji biyu na

Kafin ace shekara ta zago na waye tar har turancin broken din nan na iyashi sosai kamar dashi aka haife ni

Sai dai a rayuwa nafi bada aikin anty hanne muhimmanci dan ko makarantar na shirya zanje, inta aikin saisa abinci ta kama nakan iya ajiyewa na rana guda don kawai na kula mata da business din ta,
Sosai ta rike ni kamar jinin ta,itace tayi sanadiyar kwace fuskan maraici da damuwa acikin zuciya ta
Sai nake ganin to meye a duniya nan wanda bazan iya mata ba?.

Gashi Yanzu Na kanje wajaje dayawa aika,banki,
kasuwa da sauran tsabgogin business, domin a shekara guda danayi anan kasuwan cin anty hanne ya dada habakan da yasa ta bude shagon saloon na mata ana mata service din pedicure and manicure.

Tsaban gatan da tayi min sai ta barni ina zuwa chan ina raba kafa ina tayata aikin manicure idan na kammala saida abinci na,musamman wekends da bani da makaranta
Kuma duka aiki biyu tana biya na.


At 15years jiki na ya dada bayyana kyaun sa na ban mamaki…

Girman da ya dan bayyana a kirji na ya shiga ruda mazan banza har na fitan hankali

A ciki kuwa harda saurayin anty hanne wanda ta kama da kyar  kwara daya akan shi zai aure ta ya rufa mata asiri.

Shikuwa brother felix tunda yaga na habaka sai ya samin kahon zuka.

Tun abun baiyi tsamari ba har masu jin haushi na suka dauki wannan daman suna kai mata gulman cewa na fara girma zan kwace mata manemi.

Kwance tashi har anty hanne ta fara sauya min fuska, .nikuma sai na dauke wuta ma saurayin nata dan ko gaishe sa banayi 
Yanzu

Duk da haka ban tsira ba,don a ranar da ta gane cewa asali ma baiya da niyyar auren ta dan Kudin ta yake so yaci sai taji haushin sa har sukayi kaca kaca yaje ya sha giya ya bugu sosai..

Gashi dama shima a gidan mu yake kwana tare da anty..
To daya shigo
Maimakon yaje ya bata hakuri sai ya taho dakina ya farmin da niyyar yimin fyade.

 Ihu nayi masa ina kwarwa

Ita kuwa anty hanne data fito sai ta hada har da kishi da rudewar tunani ta hada harda ni ta kora mu a rayuwar ta.

Ranar Nayi kuka sosai,dan kuwa na fahimce ta itama sosai

 ba a son ranta tayi min haka ba sai du su arna dama basu cika daukar qaddara mai muni a rayuwar su ba.

Tasan babu laifi na,amma sai tasa aranta nice sanadiyar rabata da mijin data sha wahalan samo shi don ya rufa mata asiri ya aure ta 

Ni kaina na fahinta wato samun miji Ba abu ne mai sauki wajen tubbiyar karuwa ba

 Dan haka na yi tafiya ta uwa duniya a duk dama bansan ina zanje ba.

Kaya na da kudin aiki na da anty hanne tabani sune kawai a hannu na danko wayar salula bani da shi.

“Kwaryan Garin kaduna na shiga ina browsing ko ina da idanu na,Tun bana son kashe kudina har nafara tabawa
Daga inci wannan sai inci wannan
Wani abin ma da kudi na amma da kyar na samun wajen kwana mai mutunci.

Kwana biyu kacal nayi ina gantalin neman mafita makaina kwasam ranar sai nayi dare a wani hanya..

Dama wani hanyar nake bi idan zan shigo gari to bansan cewa ana fashi awajen ba sanda nayi kuskuren shiga cikin su har hukumar tsaro suka kama ni cikin rundunar yan fashi..

Naci kuka kamar zan fidda raina amma babu wanda ma ya saurare ni

Haka aka kulle ni har tsawon kwana 10 Wanda Da kyar da wahala na fitar da kaina,Anan kayana da kudi na suka salwanta suka bace na dawo daga ni sai ikon ubangiji na.

Gefen wani dakali na zauna Damuwa sosai ya fara shiga raina

Gashi Tunda aka sake ni a station ban ci komai ba ga yunwa ga tashin hankali gashi gaba daya na rasa gane ina zanje guda daya domin ataimaka min ko da na kwana koda zuwa gobe na nemi mafita.

Haka na ta zaga garin kaduna da kafata ta karshen ta a wani babban masallaci mai site din mata da maza na dan rabe

Juyi kawai nakeyi,kalar tausayi inda yunwa da bakar gajiya ya riga ya galabaita ni 

 kwance tashi nake kamar taliyar dayaji ruwa, gashi ni sam ban iya roko ba.

Duk sai na rasa meke min dadi
A duniyan nan,baccin ma yaki zuwa sai dai nasha ruwa nayi sallah.

Chan dai da yamma yayi sosai inata murkusu su saiga wata mata kanar daga sana ta taho da awarar ta  leda mai zafi yana buso qamshin dadi sai kuma Tayi min tayi da fara’ar ta..

Ni kaina nasha mamakin kaina dan ko irin Ja din nan banyi ba n tsoma mata hannu na fara deba bibbiyu ina kaiwa bakina

 cikina dayaji saukar abu mai dumi har wani kugi yake shi kadai daga bisani matar sai ta tsura min idanu kawai tana min kallon anya lpya kuwan..

“Ban ma lura ba sai da na farga daga abun dana keyi,sikini na sauke kaina kasa cikin jin kunyar ta har Hawaye naji na neman kufce min,sai na maida su dai na yi controlling kaina cikin dabara na tsame hannu na pretending to be ok!

Matar Ba yadda batayi dani nacinye ba amma haka naki fir harda mata karyan cewa zanje gida dama jiran lokaci nake yi..
Sai nayi mata godiya

Tace toh bakomai hakan yasa na tattara kafata bayan isha’i na tsaga dare na cigaba da tafiya..

A Duk sanda na tuno da abun da ya faru dani a hannun polisawa da barayi sai naji tsoro ya taba ni sai nayi sauri na nemi gefe na zauna,

Chan kuma sai na tashi na cigaba da tafiya kamar na mance

 Acikin daren har Wani unguwa na kai kaina bansani ba,wajen kuwa shiru ne babu hayaniya daga ji kasan anguwan manya ne.

Normally nabi kan shimfidddiyar titin na dan sauka cikin wata siririyar hanyar data bi bayan anguwan ni kadai ina tsagawa kamar wata mayyyah don ko fargaba bana ji

 buri na na samu wajen da zan dan fake zuwa gobe amma har yanzu ban gani ba sai ma dada zilma kaina cikin ciyawa nake yi

Ina dada kaiwa ciki bayan wani anguwa,sai naga  duhun dake gabana ya dadu yayi yawa,tsoro sai yasa ni kawai na tsaya ina tunanin kar nabi hanyar nasake jefa kaina cikin wata masifa.

  Gefen wani old abandoned mtn stall na zauna na rafka uban tagumi..

Anan Ko minti biyu banyi wani rudadden kara ya firgitar da  ni sai da na fada kasa na toshe kunne na.
Karar kamar na bindiga ne amma banga kowa ba tukuna

Wani rawa jiki na yakeyi shikadan sa Da kyar na dawo hayyacina anan ne ma na fara jin sautin Maganganu
sama sama a kusa da ni,da wani uban speed kirji na ya kara bugun shi

Sai nayi saurin labewa da kyau jikin shagon,nasa ido ina kalle kallen hanyar da zanbi na arce na bar wajen acikin hanzari

Ina kuwa saka kafata zan gudu sai naji an dafa ni…
Numfashi na ne ya dauke chak,
Daga juyawa ta sai naga mutumin  daya dafa nin ya sulale kasa ya fadi jikin shi da gefen kansa duk jini..

Da sauri na tsunguna akansa ‘na tsura masa ido sai naga yana kwace idanunsa da kyar yana min alaman na taimaka mashi.

Daga gani yasha tsere dan haki yake yi irin na gajiyyau   
Kafin ma ya bide baki yamin magana sai na ji maganganun wasu mutane,a iya turancin dana iya wajen anty hanne yasa na gane cewa kashe shi suke neman yi shiyasa suka biyo sa nan

Sai na yi sauri nima na dauke numfashi na,na ruufe shi da ciyawan wajen nikuma nayi gefe da shi ina lekowa haka na jira har saida mutanen suka bar wajen.

Nan na shiga duba mutumin nan har nagane cewa.An harbe shi a gefen kafada ne 
Ne toh jini na zuba sosai sai  kawai na yage dankwali na na daure wajen..

He looks very healthy and rich kaya masu shegen yau da tsada ne ajikin sa sai naga kuma ya tsufa sosai akalla zai kai shekaru saba’in ko tamanin a duniya.

NAsan bazan iya daukar sa ko motsa shi ba,dan haka na shiga jejin wajen na shiga nemo mana hanyen mafita..

Karshe dai akan bola na tsaya na taho da sauran tsimammen giyar da aka sha ala watsar da broken botles da aka jefar kan wata open dump

 daukowa na yi na zauna na goge na kimtsa,da shi nayi jinyar sa duk dama yaban wahala sosai, mutumin nan yayi dauriya iya dauriya sa shure shure da komai har Allah ya bani sa’ar cire masa harsashin bindigar agafen kafadar sa..

 Babu magani mai kyau ko wani mafita dan haka sai  mutumin nan ya sume min

Daga nan Mutumin nan bai farfado ba har sai da gari ya waye ni kuma ban yi bacci ba don tsoro haka na tsaya gadin sa.

Da ya dago lunsamshun idanunsa  ya kalle ni sai yace meye sunana  nikuma nace mashi suna na bahiyyah.

Yace min ya gode sosai da na ceto rayuwar sa amma nataimake
Shi mubar nan wajen dan yasan za’a sake dawowa neman sa.

Banyi musu ba na tallafa masa da kyar dan kuwa bantaba ganin dauriya da gwarjini irin nashi ba.

Haka muka dafa juna muka shiga wani waje chan bayan garin inda babu mutane sai go naki da shukoki.

Sai dai na lura raunukan jikin sa ya takura masa sosai kuma yana shan wahala.

Muna kaiwa wani waje naga ya sake ni ya dan kwanta,yana dan dauke numfashi.

Tausayinsa duk sai ya kamani dan Ji nayi kamar wani mutuwar zan sake gani agaba na, dan haka na shiga hade haden ganyen kusa dana nesa mai amfani da marar amfani har naci sa’a  na gogga ma mutumin nan ya dan ji dama dama ya farfado.

Sai Yace min na fita bakin hanya na nemo masa aron waya zai kira azo adauke sa

Cikin mamakin ta ina zan fara nema Nace eh?

Bai kula ba Yace kije kiyi sauri..kinji yata..?

“Yanayin da yayi maganan yasa ni na mike tsaye Bansan meyasa ba sai naga kawai naje bakin hanya..da shike wajen baya ne sosai babu kowa

Nikaina Na kai wajen minti 10 kafin naga wani saurayi akan machine roba yazo wucewa.

I know i have to be smart sai na sa masa hannu na tsare shi a nitse.

Cike da wayo da iya magana nace mashi dan Allah ya taimaka min

 nace dani da mahaifina ne muka zo wucewa sai mukayi hatsari kuma wanda ya buge shi ya gudu gashi babu wayar da zan kira gida.

Naga fargaba a idanun saurayin amma dashike
I look very cool and innocent gashi ina da kyau mai jan hankali, a haka har ya biyo ni na nuna mashi mutumin a matsayin mahaifi na ..
Saurayin ya jimanta har da cewa zai taimaka mana amma mutumin sam yaki,shidai kawai yafi damuwa da yayi kirar da wayar sa.

 Bayan ya gama kirar sai
Yace masa ya tafi babu damuwa za’a zo adauke mu.

Nima Godiya na masa kamar da gaske

Shikuwa haka yaki tafiya shima sai ya zauna damu har kusan mintuna ashirin
 duk ya dauka ko mahaifina na gaskiya ne dan kuwa sosai mu kayi pretendingn hakan

“chan bada dadewa ba sai naga wasu kerarrun motoci har guda biyu manya manyan jeep daya an rubuta GMC YUKON daya kuma TOYOTA RAV4.

A rayuwata inba a tv na ni bantaba ganin irin su ba..

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button