NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 3

_*♡AHUMAGGAH????*_ 
   _A nigerian historical fiction_             
   *_WATTPAD SURAYYAHMS_*        _Brilliant writers association_ 
     _Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_ 


_Bismillahirrahmanirrahim_ 


_3⃣-ROYALTY MEETS ELEGANCE♡_


Qarar da wooden door din ya saki ayayin da ake budewa shi ya daga ni a dan baccin bayan sallajn fajr dana keyi.

‘begham sahiba ce ta shigo Wato kyakyawar matar nan da Aka danka ni hannun ta jiya da daddare.

“..Tun Bata karasa sake handle din door din ba ta kafe ni da ido sai dai batace uffan ba anan nima Sai na dan dago na kalle ta Wani haske da taushin murmushi nagani akan cikakken dattijuwar fuskan ta daya sa naji duk baccin dake idanuna sun washe.

Gyaran murya tayi tare da cewa sallam

Na ansa ta a nitse na mike na karbi kayan dake hannun ta cikin ladabi na gaishe ta da “ina kwana” sai ta amsa min tare da miko min package din dake hannun nata
Tace min
Open!.babu bata lokaci Sai na bude.

Wasu jajayen doguyen Riga ne da dan kwalin su nagani ba ayi musu adon komai ba dana warware sai naga size dinsu dai dai kamar gwada ni akayi.

Begham Tace baccin ya ishe ki kuwa bahiyya? Nayi saurin gyada mata kai 

to ina waje Maza ki shirya da kayan hannun ki sai ki taho ki same ni.

Nace toh cikin mikakkiyar yanayi na tashi tsaye da kayan a hannu na kamar ba wacce ta taso daga baccin gajiyan ba.

nan na shiga toilet na wanke idanuna na fito na shirya cikin kayan Data zo Min da shin din tsaf  na fito na biyo bayan ta muka fara tafiya.

Akan Wata shimfidadiyar titi muke takawa

cikin wata katotuwar black and golden gate wanda bazan iya misalta tsawon shi Ba muka dosa.

Ba shakka shi nagani ajiyan da muka shigo cikin dare sai dai ayanzun nafi ganin girman sa,..tunda muka hau tafiyar nake raba ido nidai sai kalle kalle na keyi begham tana a gaba na tafiyar ta Cikin nitsuwa Wanda Daga ganin ta kasan ita din babban Mace ce

..,duk dama a jiyan cikin dare muka shigo wani Mamaki ne ya cika ni ganin yawan mutanen dake haraban gidan ana ta kaikawo kowa cikin samfurin kayar aikin sa.

Tun Daga tsarin kofar wannan katoton golden gate zaka iya cewa gidan wani babban mashahurin mayakin soja ne tsaban yalwataccen security armed forces dake kare gidan ta kowani fuska.

masu aikin tsaron gidan suna da yawa Wanda akallah uniform din jikin su ne ya banbance su da sauran tarin ma’aikatan dake shawagi wasu sunsa clayed brown uniforms wasu day wears,kowa na hidiman gaban sa.

Ina dauke idanu Na a kansu na ci karo da wasu irin dirarrun storey buildings guda biyu masu kama da ancient building of rustic architecture,to be honest,gidan babu maraban shi da gidan sarauta its huge, 8000 to 10000 times bigger than gidan dana fito.
…kuma kowane storey buiding yana da personal golden door dinsa wanda suka kere tsayin na farko dana fara gani yanzu

Da aka bude mana gate din farko wata haddadiyar parking lot na fara gani,acikin ta babu mota kwara daya da za’a baka wanda bazai fidda ka talauci na har abada ba.

Bayan manyan  driveways dake wajen, a Kusa da shi akwai katoton horse stalls wanda zai iya daukan dokuna dari zuwa dari biyu wajen is kind of grassy its like masu lura dasu ne kawai ke shawagi anan wajen.

View din ginin gidan gaba dayan ta is just like that of a royal kingdom  amma Kuma ba haka bane kai tsaye,sai ina ga kamar tsantsar tarin dukiya ce kawai take ambaliya bana wani sarauta ko Mulki ba .

anan Shashin ma gani nayi kowani ma’aikaci na yawo cikin specific tsarin uniform din aikin sa

Wata tsaftatacciyar iskan dana shaqo Ta ramin hanci na yasa ni noticing reference to nature dake zagaye da dogon Shararren streets din daya bada Undulating contours da layout din gidan cikakken tsari,its a Cool decorative greeny vegatation of palm trees sun jeru sunyi liff kamar da hannu aka zana su.

Gefe da wannan waje akwai jerarrun pebles back splashes wanda suka Dada fallasa tsafta da nitsuwa Da kuma kwanciyar hankali dake muhallin wajen 

a karshe dai
Wasu manyan multi purpose wood /metal furnitures zaka gani inda aka sarrafa su  a wani open space kamar lambun shakatawa

AHakan ma ba a bar cikin wajen haka ba sai da aka saka royal ottoman walls da relaxing benches hala ko dan Organisational functions.

 Gidan dai duniya ce

Ido na ya gaji ne dan Bazan iya daukar komai da komai ba, dana bayyana muku tsarin,basket ball and handball court,swimming pools,arch statues,water  splashes,da luxurios garages and gym din dana gani.

Domin kuwa iya kallo nayi,amma Ni kaina bazan iya Fadan komai tsala tsala ba har muka shiga wata hall way daya miko mu wata tsaleliyar royal palour,kai wannan ya wuce nace dashi palor bari akira shi da royal hall kawai
  
Wata mata ce ta shigo ta same mu nan suka gaisa, begham tace mune baqin albarkarciya jahan Aarah Allah ya sa bamu iso mata cikin takurawa ba”…

Matar tayi  mana murmushi da gefen idonta ta kalle ni sannan Tace”barkan ku da zuwa begham ai dama ku take jira amma kujira ni anan ina zuwa.. sai ta koma ciki Babu bata lokaci..

Nikam cigaba da kallon duniya nayi,..duk kauyanci na yau saida ya fallasa kansa

design din cikin gidan ya wuce mahadar Da za’ace dashi luxury Meets royal elegance.

Domin kuwa an hado tarin lush materials in bold colours like turquoise and ornate patterns

chairs and sofas anyi sune da wani irin design din silk and velvet.

Sannan an hada tsadaddun setin gadgets and kuma daidaita marching textures kamar su velvet couches din,metal light fixtures,wood tablets and glass decors.

A takaice dai duka  Furnitures Dake Ilahirin gidan an kera su ne da elm, marble,hickory and chery,sannan dukan handles din furnitures din su anyi shi ne da Tsadaddun brass knobs wanda ya hada da hannun  drawers,cabinets da tuff boards ga kuma airmores.

A gefe dani kadan  akayi ma zaunin wasu shegun hand crafted brass and copper lanterns dake fidda wasu irin launin haske daya dada kara ma wajen touch of royal sophiscation and warm elegance.

Ban san Sanda na karkato wuya na leka Sauran hallways din ba its like A saman kowani hall Dake gidan akwai crystal chandellier Mai mugun dauke ido Then finally The wall scounces.

Shigowar wannan matar ya dakatar dani Daga duban wani Iri ne,as expected da murmushi kan fuskan ta tace mana ki shigo bismillalh sannan tayi gaba Muka fara binta abaya.

Tun Kafin muyi nisa begahm ta dan dube ni, wani Kallon gyara kimtsi tayi min wanda ya jefa ni cikin nemowa kaina nitsuwa Da kama kai.

dan haka Ne ma ban kara kallon sunnah ma komai ba har muka iske wata amazing royal palour Bazan iya Fadan me ya kumsa ba Tsabar haduwan shi.

Tuni matar da ta kawo mu ciki tayi gefe ta tsaya

Ni kuwa alokacin Wata kyakkwiyar mata ce ta dauke min ido, i bet she is in her early fifties azaune agaban full size screen tv take xaune tana amsa waya tana dariyar ta mai cike da nuna kasaita da aji.

Kallo daya zaka mata kace sarauniya ce
domin kuwa jikin ta sanye yake da wani tsadadden grey gown mai dauke da ratsin black diamond stones kanta tamke da Nadin turban Shi kuma baki.

Haka muka jira ta gama amsa wayar ta,data juyo ta kalle ni wani Murmushin dana gani shimfide a angelic face dinta yasani naji ciki na yayi kugi har gabana yana dif dif shi kadai 

A duniya Bayan mahaifiya ta  wannan mata to me She Is the most beautiful creature anyone can think of.

Ido kawai tayi ma dayan matan ta fice ta bar mu da ita MU ukU.

Sai naga begahm sahiba ta rusuna da sauri cikin girmamawa tana cewa,

Allah ya ja zamanin ki jahaniyah mai Tarin albarka ga nan yarinyar da aka bani na kawo ta wajen ki.
A Nan ma murmushi kawai matar tayi
 mikewa tsaye tayi cikin Salon kwarjini da kasaita ta iso gareni.

Wani nitsatsen Kallo ta bini dashi A sanda take faman daidaita Kasaitacciyar tsayuwar ta agaba na

Karkwawa hannu na ya fara yi dakanshi duk Tsoro da fargaban inuwan ta  ya cika min mara tam da fitsari sai Zaro ido waje nake ina sadda kai.

Da shike batace mjn uffan ba Wajen wani shiru ya dauka kamar an kashe maraya,nidai ko da ba’a gaya min ba a irin wannan kallo Nata Nagane Cewa ta takarance ni tsaf daga sama har kasa Babu ragi

..sai da taja sight relieve kafin tace min “Ure most welcome”..ta na fada Da sauri na dago Na dan kalle ta dan kuwa sautin muryan ta mai mugun tsada ce sai dai barin baki ya hana ni amsata

Tace Begham ki kira min adama kuzo tare In 5minutes.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button