AHUMAGGAH 3

Begham Tace toh angama ranki shi dade sai tayi waje ta barmu Atake.
Matar Bata sake kallo na ba ta Juya ta koma kusa da tsakiyar hall din,Sai da ta dan bani Rata tukun ta juyo tace yarinya Meye sunan ki?
Ban bata lokaci ba na dago Cike da dauriya Nace”sunana
…bah…i..yyah
Bahiyyah…
Sai Tayi Shiru Bata sake cemin uffan ba But She was looking at me closely like a true royal queen of dynasty
yadda ta nade hannayen ta da su kaji jan qunshi da kwalagwalai yasa naji tamkar ina gaban wata sarauniyar matan duniya ne Gaba daya
Ita kuwa kallo na takeyi har Sai da ta lura na natsu kafin ta sake sauke ajiyan nunfashi
Cikin nitsuwa da sanyin kalami ta fara min magana.
Tace sunana jahan Aarah nice matar wanda kika taimaka a wancan daren da baiyi da manufar alheri a cikin rayuwar mu,miji na Ya fada min sunan ki bahiyyah But na sake tambayar ki ne sabida waka daga bakin Maishi yafi dadi…
Anan Wani nitsuwa maganan nata ya sakamin dan cikin kasaitaccen yanayi ta karashe shi,sai Nayi shiru na bata full attention Sai ta cigaba Da cewa
Mijina ya fadamin komai Game dake,dan haka Zaki zauna anan gidan tare dani kafin nan ya kammala sauran jinyar shi ya dawo.
Fatan kin fahimce ni?
Da sauri na gyada kai na tari numfashin fargaba dake neman shake min wuya na da beam smiles
Shigowar su begham kenan jahan Aarah,tayi nuni da Matar da ta shigo Damu mai suna adama Wanda kowa A gidan yake kiran da Sunah ammuh,Anan Jahan tace Mim wannan zata nuna miki duk abunda ya kamata ki sani.
Wani kawataccen box naga ta sa adaman ta dauko mata,ba bata lokaci naga ta miko shi ma begham
Ita kuma ta rusuna tana godiya
…a haka har tayi mana sallama ta bar gidan mu uku aka barmu a faloun
Inda Nan din gidan sarauta ne Da zan iya Cewa Adama ce jakadiyar jahan Aarah but no.
data dan dube ni sai Tace Ranki shi dade fatan zamu iya tafiya Ko akwai wani bayani Ne?
Kawai sai naga matar ta min hannu Alaman na matso,murmushin data keyi yasa na dada tahowa a sanyaye na tsaya daf da ita.
She knew im nervous and soo scared,hannu na ta fara kamawa sai tace godiya ta tabbata ga yarinya mai jin kai irin ki.
Karki razana da mu babu abunda zamu miki,kwance tashi ai baya hana ruwan rijiya sabawa da guga ko!just relax
..u will get use to this place Its ur home now.
A hankali na dago na dube ta naga murmushi ma takeyi still,Kirjina ne ya shiga bugawa Amma dana samu na kauce ma hasken idanun ta da kyar na iya furta mata nagode.
Tace zaki iya aiki agidan nan?
Nace eh na kuma na gyada kai a ladabce
Tace toh adama gata nan Zan gaya miki Sauran details din aikin ta anjima.
I think she will fit in best ma aikin dana zabar mata.
Hannun matar Naji A kafadata Ta dafa ni sai na dago kai Amma Nakasa hade ido da ita,But i can feel it while smiling at me tace Daga yanzu Zaki zama mai kula Min da dana shima yana nan agidan nan
..Yadda tayi maganan nasan This statement is neva a request Bare na samu filin MUhawwara da zuciya Ta akan ina so ko bana so
Nidai Wani irin faduwar gaba naji tun kafin ma na ce Komai,naji ammuh Adama ta yi korafi tanacewa amma ranki shi dade,anya bata kasa a matsayin personal maid din khaldun ba?
Dan karamin miskilallan murmushi matar tayi tace mata a’ah,
I think shes 15 ko?Ta dube ni Sama da kasa in a quick body inspection
nikuwa nayi saurin sauke kai na kasa Nayi Shiru.
Sai Tace zata iya mana,beside a matsayin alfarman da tayi mana ta wuce wanda zan bata aikin kula da dawainiyar dana.
Adama
Da saurii adama tadan rusuna kai tace yes jahan
Just Do one thing,teach her everything and everywhere.
Idan kuka kammala nida kaina zan gaya mata dokokin aikin ta
Adama ta dube ni tace kinji ko?
Cikin barin baki mai dada bayyana innocent heart dina na amsa da eh naji.
Nagode
Nan Jahan din tayi murmushi ta sallame mu hannu na adama ta kama muka nufi wani site.
Nidai bin ta kawai nake yi amma
Bansan cewa jahan din tafada ma adama akan Gwajin hali ta daura ni Shiyasa tabani wannan aikin ba.
Chan da yamma Bayan waje yayi liff ana ta shirin himman kirayen sallahr magriba
Matar ce a kwance akan wata sculpted black tuned soffa a wani purple tinted mini palour Har ta sauya Kayanta zuwa royal orange arabian jallabiya.
waje yayi shiru sosai don kuwa nan waje ne da ta saba amsa wayar mijin ta wato retired,navy admiral 5 stared army general,a reknwn political beurocrat,and the 39th chief security adviser to the united states legis.
Rtr adm gen alhj hamood mufaddal clive sunan shi..
Shi mutum ne karfaffa mai tsayi da jiki curently in his late 70s.
Duk da wayannan matsayin na shi
He Is still a son from an ancient royal palace of iran anan ma wata sarauniyace ce ta haife shi.
Da tarihin Zuria yabi zuria a nan asalin tarihin sa ya bayyana cewa ajinsin dawlat khatun ya fito karkashin jinin wasu bi-Queens of the persian empire paticularly jinin sarauniya badi’atul jamal waccce ta fara kafa tarihi nadaban a labarin sarki sayful maluku tun a lokacin kasar iran yana amsa sunan sa na land of aryans a duniya.
A yanzu inda ta kwanta babu abunda take Tunani kamar maganan da su kayi da mijin ta akaina tun kafin nazo,shiru tayi cikin wani nazarin daya sake jefa ta cikin jimamin abunda ya faru da shi a cikin kwanakin nan yare da lunshe idanun ta ta sauke wani sassayan ajiyan zuciya.
Asalin sunan ta Aarah,amma ana kiran ta da Jahan Aarah itace matar sa na farko,duk dama ita ba daga dangin shi bane amma Soyayya sosai su kayi kafin sukayi aure
…rtr hamood ya kasance Shine hasken zuciyan ta cikar burin ranta,farin cikin ta da duk wani sadaukar wan ta,sai dai inta Tuno cewa badon yarinyar nan bahiyya ba da babu shi a duniyan yau
Sai taji kamar ta sa a kira mata bahiyan tayi declaring dinta yar cikin ta kawai dan nuna godiyan su,.
Da dai Sun tsara hakan tun a farkon jin labarin ta,sun fahimci cewa ita abun a tausayawa ne, yarinya karama Marar uwa da uba ne a duniyan nan.
Sai dai she can’t Do That just yet,bazasu iya aikata haka agagauce ba domin kuwa su manyan mutane ne wanda rayuwar su ke tafiya da tsari da dokoki wanda dole ne su bishi ko dan samun tabbatcen tsira daga makiyan su.
Bayan mutuwan iyaye,ayanzu abu mafi daraja arayuwan jahan Aara shine Mjin ta
Daga shi kuma sai yayan ta Guda biyu mace da namiji
Gashi Haka kawai Bahiyyar ta shiga ranta,har ta Kuma furta hakan ma gen hamood M tun ma bata ganta ba
Toh Lokacin ne suka hadu sukayi nazarin rayuwa Mai zurfi akaina harda hadun bakin yar uwan sa begahm sahiba
acewar su tunda an tabbata bani da kowa a duniya toh Kafin su maida ni official adopted child zan zauna a matsayin mai aiki da hidama da dansu
Wanda Duk cikin zuria suke ganin kamar babu irinsa a wajen wahalar zama,shi mutum ne mai murdadden yanayi,muddin har na iya zama dashi to babu tantama zan iya zama da kowa.
Kuma Ahakan suke saran sanin wacece ni kuma da Wacce irin zuciya nazo Musu dashi.
Cikin su jahan tafi kowa Fatan na Kasance ta gari Inda zatayi saurin yanta ni ta dawo da ni tamkar yar cikin ta domin ita mace ce mai tsananin tausayin nakasa da ita Ga son maida Ladan alheri akan lokaci..tunda ta ganni yau take faman tausayi na aranta.
She is already thinking of so many ways to repay my kindness.
Ni kuwa tun Ranar da muka fita a shashin jahan Aarahn ba a sake bada izinin dawowa dani ba
Achan wani sashi muke Jibge,tare da sauran dattijan mata Su hudu wanda suka kasance manyan masu lura da ma’aikatan gidan kowa dana shi fannin Daya kware.
Ammuh adama itace general Chief maid Na gidan,Sai mami fatima tana kula da harkokin siyayya Da harkokin Kowani irin store Inde nagidan ne, Mami hafsa Itace mai Lura da duk wani shige da ficen kowa dan haka tana da Masifa Sosai.
…Mami jamila Kuma Itace kunne da idon gidan babu karya Wajen Aikin ta na gano munafukai da warware matsala Tsakanin Mutane.
Sam basu da matsala domin kuwa akwai wadatacciyar arzikin da komin Salalan Tsiyar mutum dole zaiji shi ajikin sa.
Yanayin Tsarin dokan da aka shimfide ake bi da ma’aikatan gidan Shi yake nuna sakewar su da dattako da girmamawan su wajen Aiwatar da dutyn su.
Kwanaki goma sha biyu kacal Ammuh adama ta dauka tana saita ni
Farko sai da ta zagaya dani kowani sashi lungu Da sako na gidan kafin muka dawo muka fara daga kan koyar salon magana
girmama Nagaba
kwajin tsafta,iya tafiya,Kayan Amfani da girki,hatta yadda ake serving da yanayin gyaran gadon su duk ta nuna min
hazaka da kaifin basirah ta yasa yanzu zaka sha mamakin yadda adama ta sake dani,dan sau daya zata fadi abu na dauka,daga ta koyar dani tofa za taga nayi dai dai koma fiye Da hakan, kuma bana da saurin mantuwa.
Ammuh Dai ta dawo min kamar wata uwar daki don kuwa tun zuwa na ba wanda ya taba daure min fuskan sa Agidan..
Yanzi har na Saba a gidan Karfe 7.00 Na kowani rana ake bude gate Din waje gaba dayan ta sannan babu mai fita agidan har sai karfe 9.