AHUMAGGAH 3

Anan inda nake Kwana kuma 6.oopm na safiya ake buga musu workers alarm Daga jikin wata katuwar agogo dake Chan sama tsakiyar gidan dan haka kowa lokacin yake tashi ya shiga hidiman aikin sa
Yau Ina zaune akan sallaya Ammu adama ta tada ni nayi wanka na fito na saka wata riga da zani ruwan madara Da simple flat shoe na biyo ta.
Ni dai bakowa bace amma a yadda naga suke min nasan indai karamci ne to ana yimin.
Site din jahan Aarah muka nufa da shike babu hayaniya har muka shiga banga kowa ba Sai ita a Zaune Akan Beige rug Wanda yaji Floral patterns
Rusunawar Gaisuwa ammu tayi Bayan ammun ta mike Nima tuni sai Na bi sawon ta na rusuna.”Nace Allah ya taimake ki ina kwana?
Jahan tace lpya bahiyyah ko!.
Nace eh nice…sai dai bandago kai na ba
Yadda na gaishe Da Jahan din cikin ladabi da girmawa ya matukar burge Ammuh adaman barin Ma aje kan jahan Din dake sake min faffadan murmushin ta mai Saurin Tausasa yanayi
Daga ganin kalar biyayya ta,She’s now very sure that zan iya aikin da suka daura ni akai Duk dama tasan Task ne mai matikar wuya.
Gashi dama ban san cewa begham sahiba kafin ta tafi ranar Har ta fada mata na iya girki kala kala ba.
Im just a teenager but with lots of focus and energy ni bana son saibi bare sanyin jiki ayadda naga mahaifiyata na Kazar Kazar Akan aiki Nima haka na taso da spirit din.
Jahan Aarah tace ki saurare ni kiji abunda zan fada miki duk abunda baki gane ba call my attention ok?
Kaina a tsunkuye nace yess Jahan.
Tayi murmushi Tace’..aikin ki na farko karatu ne zaki zauna a koyar dake domin ki samu good secondry school cert,duk wanda kika gani agidan nan yana aiki toh yana da abun da zai nuna na matsayin matakin karatun sa, but yours is gonna be afternoon sessions a site din maids Thats in kin kammala duk wani aikin ki.
Game da ayyukan ki kuma Ya kamata kisan cewa.
Dana Shi kadai yake cin Break fast dinshi dan haka akan lokaci zaki na kasancewa a kitchen din dake section dinsa Wanda ke Kusa da dakin kwanan sa…
Adama tafada miki kitchen din nashi ne shi kadai ko?
A Dan Sanyaye Nace eh.
Tace good to Kar ki sake Kiyi masa abinci awani wajen inba A nashi kItchen din ba Doka ce
Cikin gamsuwa Nace yess maam
Tace By 7.30Am na Ko wani Safiya zaki shiga bedroom dinshi,do not wake him up kedai ki tabbata kin aje mishi fresh mint tea,and dont forget No Sugar honey Za kisa Masa 2teaspoon.
Zakiga oak side table anan zaki bari sannan sai ki fita
Inya tashi Zai fito karfe 8.00 Dai dai dan haka kiyi kokari Yana bada baya ki shiga dakin ki canza bedings Dinsa ki tsaftace dakin,kar ki manta zallan dakin baccin sa ne aikin ki,sauran part din san akwai masu kula dashi.
Sannan Karfe 9 zai taho dinning dinsa cin breakfast.
Sai ki tsaya ki yi serving dinshi ki Zuba mashi ko wani nauin abincin da akwai ba tare da kin tambaye shi mai yake so ba
Bayan kin kammala da nan sai ki koma ki hada mashi ruwan wanka akwai instrument so set it at exctly 39 degrees,yana wanka ke kuma kina tsaftace kitchen din sa.
Kar ki damu da serving dinshi abincin rana
a wajena yake ci.
sai dai Idan ya dawo zaki kawo abincin daren shi dining dinsa da misalin karfe 8.00,sauran lokacin da kike free zaki iya amfani da shi kiyi sauran ayyukan Daya dace
Nidai kallon bakin ta kawai nake,nace Ikon Allah!shikuma hakan rayuwar sa yake?Hmm tabb di.
“Baahi…adama ta dakatar da tunani na da kiran ta Afirgit na amsa da naam..
Tace Kinji abunda aka ce miki ko?
A dan birkice nace naji insha Allah zanyi Duka..
Nan Jahan ta sallame ni Fuskar Ta dauke da Wani irin Weak smiles.
Dana fice Adama ce ta matso cikin saukar da kai tace ranki shi dade jahan.
kiyi hakuri da shisshigi na amma sai naga kamar daman Da kika bata yayi yawa khaldun sa’ood bazai so ace…..
Bata karasa ba jahan ta daga mata hannu..Tace
Karki damu Da wannan adama
Nina haife shi kuma Nasan menakeyi sarai
Shin ya kike ganin hankalin yarinyar a yanzu?ko akwai abunda kika gano game da ita wanda zan iya sani ne?
Nidai Nayi nazarin Mai zurfi Akan tarihin rayuwar Ta dana jiyo Muddin Yarinyar nan ta wuce wannan jarabawar dana dora ta to ba shakka zan kaita wani matsayi mai kyau arayuwa…
Ajiyan zuciya adama ta saki tace a’ah babu komai Jahan she’s perfect sai dai bamusan nn gaba ba…nidai Ki barmin komai A hannu na ni zan kula ..Adaman tace.
Jahan tace Toh kiyi kokari…
Daga nan sukayi sallama kowa ya shiga hidiman rayuwan sa.
washe gari da safe Ammu adama ta taso ni agaba tace min Yau fa zaki fara aikin ki bahiiyyah
gaba naKe Yawan faduwa sabida gani nake kamar Bazan Saba ba
cikin nitsuwa da jan kunne Ammuh adama ta Zaunar dani tace kina ji na?
Nace eh
Tace to kar ki sake ki shiga bangaren shi Gatsau,bare Kuma dakinshi in har ba akan aikin ki ba
and most impotantly babu ruwan ki dayi masa magana inba shi yayi miki ba
Ki nitsu ki ji duk abunda zaice miki batare da kin sa ido kina kallon nashi idanun ba,in yana tsaye kar ki zauna domin shi ba mutum bane mai son raini zakiyi hankali dashi sosai.
Cikin nazarin abun Na kuma cewa toh naji Ammuh
Tace Tashi muje na kaiki sabon dakin ki Zaman ki anan ya kare ..da sauri na dago nace sabon daki Na kuma?Tare zamu kuma kenan ko ammuh? Dan Allah kar ki rabu dani ..
Ammuh Adama tayi murmushi cikin son kwantar min da hankali tace Bahiyyah kenan,
Daga nan dai batace uffan ba,Hannu ta mika min na taso jiki a sanyaye na fara biyo ta.
Bamu tsaya ba sai a cikin wani sashi Ta cikin gidan Mai kamar four duplex apartment Amma bashi din bane design Ne kawai
Sai da ta nuna min Wani zigzag stairs da zan bi ya Sada ni da wajen aiki na kafin muka sauko Wani daki sai ta bude min
Muka shiga ciki Tare.
Its a very Exotic sleek style bedroom So simple and elegant.
gadaje Yan madaidaita har guda biyu aka bar min Ga brass lanterns Masu fararen haske,komina design din Sa fari ne kar gwanin sha’awa.
This is ur personal room.
AmmU tafada tana Bude Min wardrob dan na ga kayan sawaN da aka aje Min,tace Min
zaki iya muamala da kowa amma aikin ki baya bukatar ki sake da sauran ma’aikatan gidan nan If posible Just stay alone shi
Zai Fi miki.
Tace babuu wanda jahan ta karramashi da wannan matsayi saike dan haka kar ki bani kunya bahiyya.
Sai na dan kalle ta dan Sosai na kejin wani iri araina,sai naji na Bi na damu tsoro na neman shiga ta sosai..all this rules..oohh ya rabbi
Haka har adama tayi min sallama ta fice,tin daga ranar kuma ban sake ganin ta ba.
Nikuwa Ba jira Da safassafe na tashi na haura site din sa,i think A rana na farko i was a bit early sabida danaje kitchen din shin sai da nayi tsayuwan minti talatin ina jiran lokaci ya daidaita kafin na hado Masa steamy mint tea na dora akan italian tea sets farare kal
Na fito dasu
A hankali nake bin ta hallway da yakai ni har bakin kofar dakin shi,cikin kula natura kofar tsoro na kar na dago shi a bacci
Dama A raina na bari cewa He must be a demigod tunda kula da shi ma yazama abun aiki
Irin haka.
Dana shigo Fully na kare ma ko ina kallo Sai naga Dakin yafi karfin Ma ace dashi normal daki don yana da girma sosai its like an apartment on its own Har da palours.
A kusa da tsakiyar dakin aka kafe Wani sharbaben king sized royal bed,mutum ne a kwance fuskan sa gaba daya a rufe Take da duvet Ba Aganin komai daga siffar sa
Ban tsaya kalle kalle ba na aje tea din akan oak Oriented table na juya na fita kamar yadda aka fada min
Dinning hall Nayi da sauri naje na shiga jera mashi warmers din abincin shi Akan dinning table.
Haka na dinga bin lokacin aikina daki daki har naci nasaran gyara mashi daki na sauya bedsheet na jejjera pillows komai akan tsari
Saura minti kadan lokacin cin abincin shi yayi dan haka na fita naje dinning area din nayi tsaye ina jiran shi ya dawo Daga inda yaje don nayi serving dinshi
..But ganin 9 yayi dot bai shigo ba nayi himma na shiga serving
Duk abincin dake wajen yadda aka koya min.
Ina gamawa nayi sauri na koma dakin shi
Nan na shiga dayan kofar da nake tunanin bayan gidan sa ne,to tunda nike da alhakin hada mashi ruwan wanka that means tsaftace bayin sa ma aiki na ne.
Haka na gama kare ma wajen kallo,Kirji na ne ya biga ganin girman complicated bathrum din da ko a mafarki ma babu kaman sa,
na dan dafe kaina na taho domin fara abun daya kawoni
A cikin bayin Wata katoton mirror ce mai dauke da handler na kayan duniya.
Gefe dashi akwai bath tub wanda ajikin shi drawers ne masu yawa da Wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower Tana wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu dauke hankali
Komai Dai a bayin Royal purple And black ne girmanshi mutane fiye da talatin zasu iya shiga ciki
Nidai Tabe baki nayi kawai na shiga hada mashi ruwan wanka at exctly 39 degres din”,wai shin wani dan adam ne a duniya Wanda har yake da specific tempureture na ruwan wankan sa?
rike da themometar dake bayin a hannu na nake wannan tunani ina tabe baki.
Finally i did whats right minti sha biyar kawai na dauka na fito daga dakin walking quietly Down stairs zuwa dining area dan naga ko ya taho
Luckly enough Bayan shi kawai na hango alaman yana cin abincin amma Koda wasa banga ya kammanin shi yake ba,leke nake ina daddafa pillar Ko zanci sa’a sai dai ko 1scnd ban yi ba naga ya mike alaman zai tashi,wani uban tsoro yasa Ni back turn da gudu na yi hanyar kitchen na dauko food dismisal tray Kafin na Dawo Nan ban ganshi ba
Kallo nabi abincin dashi wanda yake kamar ma ba ataba shi Ba,i was like did he even touched It?
Sai ido na yafada kan half stained spoon wanda ya isar min da amsa ta
haka Kawai na Shiga tattara Komai nakai kitchen na Kuma tsaftace su
Haka Najira har ya fita kafin na je loundry dan ance mani za’a dinga bada gogaggun kayan shi ina aje masa a closet dinsa.
Tun Daga ranar Haka nake yi kullum babu abunda ya sauya, Nakan dai gaida jahan dik lokacin da naga sarari dan ba ko yaushe ake ganin ta ba
Tun ina dar dar da gidan har na sake na jajirce na shiga bin dokokin aiki na tsaff inayin shi
Sai dai fa har yau ban taba ganin fuskan sa da kyau ba Idan na kawo mint tea yawanci fuskan sa a arufe yake cikin comfoters ko ma ya juya fuskan sa gefe
Ko da ina serving dinshi baya zuwa har sai na kammala na tafi, bare ma nace nagan sa
Rana daya dana ci sa’a ya zauna ina zuba mashi abincin idanun sa da dukan hankalin sa nakan wayar sa.
kyakkwar motsin nunfashin sa banaji bare naga ya kamannin sa yake.
All i know is he is fair,fari ne tass irin caribean white din nan
kalar jikin shi kamar ana goge shi da madara kullum, shi baiyi dau ba amma sheqin dayake yi ya wuce misali
yana da tsayi da ginannen jiki da duk da namijin da ya mallaka zaiyi tinkaho da shi Domin Kuwa babu maraban tsarin sa dana Indian actor john abraham..
Yau sati biyu kenan amma sau daya na taba jin muryan shi ranar dana ce muku na yana latsa Waya hakan ma Cemin Yayi
“leave”
Muryan nashi ko akwai dadi,Its husky,deep yet very appealing domin kuwa har yau ban mance sautin shi A kunne na ba.