AHUMAGGAH 5

Sai dai har yanzu ba damuwa ta bace Nasan me muka zoyi gashi tunda muka zo ban ma ganshi ba.
Ina sharo kwana kuwa Cikin sa’a muka gamu da nana A tana haurowa site dina.
Na dada gaishe ta,itama jawo ni tayi muka shiga wani shashi mai girma sosai.
“…Ashe ma a private part nake ban sani ba maybe ko dan anan shima ya sauka so babu hayaniya.
‘Da muka fito sarari yanzu ne nake ganin asalin mutanen dake gidan…
Its actually one of his mums personal houses, ita ma idan tazo wani abun a ibadan anan take zama duk dama gaba daya estate din da sunan shi tayi signing.
Anan ba kowa sai nanah A da sauran ma’aikatan gida tsawon lokaci suna lura da komai
“He is here for an important 100 billion dolla national security meeting wanda za’ayi shi gobe da safe karfe 10 tare da taron duka wersten kings, obas and govenors of nigeria.
Muna sauka daga part dinshi nanah A tayi da ni kitchen a wani sashi,Kamar wanda take kallon hanjin ciki na
Tace am sure ure hungry”na gyada kai na asaukake.
Sai Tayi murmushi ta bude wani katafaren food store iya kallon idanu na
Tace here!!
sai dai ki tabbata ko wani abinci zaici awaje kina wajen,ki fara tabawa kici kiji, kar kiyi kuskuren sakewa har wani ya saka masa poison.
Na gwalo ido Nace ehm?Saura kadan nayi blurting out loud but i kept shut,so idan ma poising din ne nina fara mutuwa kenan ko?….
Chaii this ppl are funy.
Ban dai ce komai ba har ta gama shimfida min dokoki kusan iri daya ne da normal aikin dana saba mashi a chan gida kano
So i can quickly memorise everthing.
Kafin na daura girki muka koma ciki,
Anan ta gwada min dakin shi da sauran part din kafin ta kyale ni tayi gaba
I stood there staring ina ta kalle kalle kamar wata fatalwa,dakin Bai dai kai na chan gida a kano girma ba amma yana da girman shima sosai.
“katoton Kingsize bed ne da tufted head boards crown molding over walls tare da white ceilings sai wasu golden drapery curtains da tarin stylish funirtures.
Tabe baki na nayi na fito na shiga hade masa abinci kodan na samu nima naci ko naji dai dai ajiki na.
I did evrything accodingly babu wani matsala dan gidan sam babu hayaniya.
Its seems like Yana busy dan haka daya kammala cin abincin ya shiga daki ban sake jin shi ba.
Washe gari da sassafe nana A ta shigo daki nah,
Bayan mun gaisa take cemin
Nayi sauri na hada mashi abincin safe ta dada jadadda min karfe 10 ne meeting din shi,
Ta kuma cewa Khaldun ya bada umarni in goge floor din dake kofar dakin shi
Nasha mamakin wanan oder, dan nasan bana irin wannan aiki .
Amma sai nana A tace min ai anan gidan babu mai shiga shashen sa sai ita,yanzu kuma nine dan haka ni zan je na goge.
Nace mata babu komai Ban wani daga hankali ma ba na saka rigar material ja da baki nafito kitchen na shiga na fara hada masa break fast
Bayan nayi serving dinshi ban tsaya ba ya sallame ni sai na je hada mashi ruwan wanka
Anan sai na lura bai sha tea dinsa na safe ba,..
Nayi sauri dai na kimtsa na fito still banganshi akan dinning din ba na duba naga anan ma ko taba abincin baiyi ba..
Strange! Zuciyata tace ina faman tattara abincin zuwa kitchen.
A hanya muka ci karo dashi duk da ma nayi saurin rusunawa adaddafe bai hanashi daura min wata muguwar harara ba.
Drop it and come Yace ya wuce
Nayi sauri nakai kwanukan kitchen na dawo zan shigo dakin san sai naji a kulle yake gam gam
Dan wulakanci haka nayi ta knocking yana ciki yana ji har sanda na share mintina talatin ina tsaye kafin ya bani izini na shigo
A gaban wato sharbaben full size mirror na ganshi
Combin kansa yake da soft hair brush
Dan Baiko bani daman daidaita tsayuwa ta ba naji yace min
Almond cakes and orange juice
Daga nan bai kara cemin uffan ba yayi shiru.
Wani rau da idanu nayi I was like New breakfast oder kenan?hmmm kirjina ne ya biga
Ayayin da na ja kafata nayi hanyar kitchen na masa exact abunda yake so.
Fresh orange juice with spicy almond pan cakes na hada mashi da cool raspbery desert.
A tsanake yake ci yau kam ya taba duk abunda na ajiye masa.
Ina tsaye daga gefe ya ajiye food napkin din ya gama goge bakin shi ya kalle phatek philp din sa ya dubi time.
Kinyi aikin dana saka ki?
Da sauri
Nace ah’a
Sai Ya dan tabe baki
Yace 9,45am u wll get my dresses..
Kafin na gama amsa shi yayi gaba ya haura dakin sa.
Da sauri na kimtsa komai banma iya neman wanda zasu ci abincin daya bari ba sai na juye a wani warmer na jika ruwa a mopping duck na taho inda yace na goge din
Daf da kofar dakin shi ne infact za’a iya ce ma wajen hall way ne daya ke bi in zai shiga daki..
Anan na baje ina goge tiles din da basuyi kama da sunyi datti ba Allah kadai yasan meya sa yace agoge mashi.
Ina cikin aikin sai ga sallama
Wani mutum nagani mai kama da delivery man wearing a strip army uniform baiya ko murmushI shima
box din dake hannun shi ya mika min ya juya abunshi.
Duk dama Nasan kayan sakawan shin ne but I have to open it And check Kamar Dai yadda nanah A tace inayi dan na tabbatar da komai intact.
Sai na aje mopper ta agefe Ban lurada ruwa yana tsiyaya A kasa Ba nan na bude box din cikin rawar jiki.
Wasu haddadun uniforma naci karo dasu God Knows Its amazing,Hannu nasa akan Materials din Ina shafawa Basai an gaya min tsadaddu bane kyaun su a ido da laushin su ya isa ya sanar min..
Farin rigan uniform kal ce da royal blue army trousers da cap an nade su tsaf kamar ba mutum ne zaisa ba.
Sai dai wannnan
Karon wayo na ya carke min A hanya bansan ma unifom din na soja bane ko na mai tukan jirgi”
,dan Ban ko iya karanta Ma’anan Abun da aka rubuta akan silver plated insignia da aka manna agaban white shirt din ba (wato milltary badge dinsa) dake gaban rigar ba .
Naga dai An rubuta wasu abubuwan a dakile kafin naga wata kalma kamar sunan shi reading BG SA’OOD HAMOOD MC.
Nan na Shiga tunani ina nazari,ni dai naji ana ta Ce masa khaldun amma bashi nagani ajikin rigar ba toh what does that mean?
Ko dai ba sunan shi bane?To sunan waye kenan?
Wasa wasa na tsunduma kaina cikin nazarin da baida amfani ban hankara ba naji an bude kofa daga baya na Ina juyawa kuwa muka hade ido tsaban gaba na yayi rasss sai nayi saurin fizgewa na kame
Nasan Shi din ne ya fito yayi tsaye yana jefo min mugayen kallo hannun shi rike da door handle dinsa
A sadade na shiga kokarin rufe box din ina kokarin mikewa na kalle shi na mika masa kayan sa,ai kuwa Ina daga kafa ta sai gashi tsantsi ya debo ni nayo zutttt na zame akasa Kayan sun zube duka acikin ruwan bleach din dake kasa wanda ya zubo daga mooper duck din.
A take na shiga ganin waje ldishi dishi Duk da zafin buguwan da nayi bai hanani karkarwan tsoro ba
Kokarin mikewa naki sai naji na kasa daga kafa Sau dari ina kashe kaina mentally.
Yau Na shiga uku na furta ina kokarin jan kafata da karfi dan Na mike nasan bazan iya Ma kallon Idanun shi ba.
Im very sorrry sir!!! Dan Allah kayi hakuri…
Baki na ne ya shiga furta su involuntarily
Baice min uffan ba
Hawayen tashin hankali bazata suka wanke min fuska ta ina famar tsamo kayan daga cikin ruwan bleach din dik sun baci sunyi rawaya
Bai min tsawa ba but yadda yake kallo na in a disqusiting way nasan tawa ta kare min.
Wrist dinsa ya daga ya dubo time a Agogon shi ya ce min
I have A Multi billion dollar meeting in 20 minutes.
Ki kawo min kayan da zansa na baki minti goma,ko dago kaina banyi ba wuff ya juya ya koma dakin sa ya barni da Jikakken kayan sa a hannu na.
Follow
#SURAYYAHMS
COMMENT and SHARE WITH OTHERS❤❤