NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 9

Nikuma Khaldun bai ce min komai ba sai na aje Juice da pancake din akan ottoman
Bench kusa da ruwan pool na dawo na tsaya nida big sis.

Kana ganin fuskn ta kasan She is worried for shahrul dan naga fuskan nata dauke yake da damuwa 

.ita kanta ta gane cewa shahrul baice komai ba ne sabida baya son khaldun ya dau abun da zafi

But It neva worked don kuwa ana fara sabon game din khaldun sai da ya nemi dai dai setin bakin saadat ya zuba mashi gwiwan hannu dagangan sai da yayi tumble din bazata yasa ihu.

Kowa yasan khal baya bada hakuri ahaka ma riirike shi shahruul yayi cikin harshen larabaci ya na dan masa masifa cewa meye haka?

Subaya tuni ta dago mijin ta a birkice tana dubasa,tsaban haushin da zafin da bakin sa yake sai yana tutture hannun ta ajikin shi

Bata ji dadi ba sam ta dago ta kalle khaldun daya tsime,shahrul ne kawai yake ce ma sadat yayi hakuri is a mistake.

Sabida ni sadaat ya waske yace musu bakomai besides ai shima yayi mistake din dazu.

Haka aka bar magana Kamar da gaske sun fahimce juna Aka sake komawa sai dai dukan su da abunda ke ransu.

Subaya tace ma saddat su koma daki ita kam game over kawai muje gida bai amsa ta ba

Nan khaldun ya min ido akan na kawo drink ma shahrul,
banyi kasa a gwiwa ba na dauko farantin ina tafe

Ina daf dasu na daga kafa ta kenan naji kwal abu mai karfi ya ture ni tsundum na fada acikin ruwan pool  

Sadaat ne ya sake ball ya gangaro bazata naci karo dashi kowa yaha hakan
Amma dukan su basu motsa ba

Big sis subaya zata zo ta cire ni sadat ya finciko ta,yace bazakije ba yanayi yana kallon khaldun alaman tunda sunfi kusa dani to su cire ni mana

 Nikuwa inata wutsil wutsil cikin ruwa

Hankalin subaya ya tashi tana ta kira na tana ce musu su taimake.

Sadaat Haka yaki ya sake ta,khaldun ma ya dauke kansa ya hade rai.

Shahrul hankalin sa ya mugun tashi da irin wasan banzan da ke wakana tsakanin sadaat da khaldun sai kallon su yake yi cike da mamaki.

 Haka aka barni
A cikin ruwa ina kokarin fitowa the pool its too big dan haka da kyar nake diving.

Daga karshe Shahrul din ne yayi tsaki ya tashi zai zo ya taimaka min

A fusace khaldun ya riko sa yace please let go in,wai kai ka jefa ta ne?

“Khaldun..subaya ta tsawatar.. amma ko ya kula ta sai  Ya ma ja hannun shahrul dagske
Zasu bar wajen

Abun ya dada ba sadat haushi A fusace ya juya yace ma big sis And you too.. Ai bake kadai bace ya agidan nan,that girl is both your sister right?,idan wani banza is weak and wicked enough yana azabtar da ita so be it Get in doors.. Ya mata nuni da hanya Subaya zata yi magana..ya tsare ta rai a bace ya ce NOw..

Da sauri ta shiga gida ta barsu su ukun. 

Zai motsa kenan
Khaldun ya tsare sa yace” i hope i dnt hear you calling me weak and wicked?

Shahrul dhe tsaye na kallon su yace  sa’ood pls stop it.
 Please let me help the girl dan Allah ku bari 

Shikuwa Sadaat abunda yake so kenan yaga dai ya bata ma khaldun rai kamar yadda yagani yanzu,baisan tsawar daya yi ma yar uwansan bane ya shake sa 

Lets go..shahrul y dada jansa amma yaki motsawa

sadat kaima ka shiga gida mana the game is over Comn dudes  

Wani fizga khaldun yayi cikin bacin rai yace ma shahrul baza a cire ta ba,shi da baiya azabtar da itan sai ya cire ta.

Sadaat yace yess i will… zan cire ta mana,am just waiting for you to go..am human i dont enslave girls Im not like you..

Ran khaldun ya dada baci sosai Da kyar shahrul ya rike sa .

Sai ya fara tunanin meye ruwan sadat da aikin da nakeyi mashi, da chan shi yace ina masa aikin ne harda wani zai masa wannan zagin?

Bacin ransa sam babu kyan gani Wani fixge jikin shi yayi ya taho bakin pool din ya kalle ni”get out”… ya daka min tsawar da sai da na firgice na fito a ruwan batare da na sani

 Go inside now..

A tsorace na wuce shi da gudu I went inside cryng my balls out.

 ….gaba daya tausayi na ya kama shahrul sosaii

 Haka suka watse kowa yayi hanyar sa
 Ziciyar sadaat kuwa kamar zai fashe dan baiso hakan ba

A daki na big sis Subaya ce tayi ta bani hakuri har nayi bacci.

Dana je serving dinsu dinner yau kam shahrul bai sake fuskan sa ba.
Duka sunyi shiru sun basar da juna
Alaman wani abun ya shiga tsakanin su kowa sai shan qamshi yake.

Little did i know that,saboda ni shahrul yayi masifa sosai ma khaldun dazu 
Ba wai don ina masa aiki ba shi kin accepting dina dayayi a matsayin yar uwan sa ne ya dame sa.

Ai kuwa Ko uffan baice masa ba,Taurin kan khaldun ya wuce misali dan shika dai yasan meyasa yake yin haka 

a duk korafin da shahrul yayi har washe garin ranan bai masa dai dai da ya amsa shi ba.

Da safe dana zo serving dinsu shahrul sai ya ce min zai tafi,yace na dinga hakuri and he enjoyed my cooking sosai, cewar sa wata rana zai sa akawo ni oman na na zauna dashi ko dan na dafa mashi daddan abincii shida mum dinsa.

 Duk dama nasan hakan bazai yuwa ba amma naji dadi sosai,nace masa nagode’..ban ma kar a dora wani kalma ba Na ci karo da wani banzan kallon da khaldun yake mana,don kuwa hararar da khaldun din ya watsa min kadai ya hana ni amsa shi musamman maganan zuwa oman da shahrul yayi.

Today i notice a little bit of jelousy a yanayin sa sai kawai nayi shiru.

Duk dama fushi nake da shi da naga ya nuna alaman kishi na aransa a Take naji zuciyata ta yafe mashi komai.
#follow
#Surayyahms
Pls sai monday????????
.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button