JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 43

Jiddah ta sauke idonta daga kallonsa tana sake nanata sunansa a xuciyarta, Aliyu kenan yake nufi, Ali shi ma ai Aliyu ne… muryarsa ya katse tunaninta, taji yace “Wani anguwan xa ki?” Sake kallonsa tayi sannan tace “Malali….” tana fadin haka ta bude jakar hannunta da sauri jin waya na vibrate, sai a sannan ta tuna ai wayar Maimoon na wajenta tun daxu da Yousuf ya kira suka yi magana, ta fiddo wayar tana kallon screen din taga Ya Aliyu… Ta d’an kallesa tace “Nayi mantuwa na taho da wayar yar uwata xan mayar mata cikin gida yanxu” Yace “Ohh ohk, take ur time, bari in ajiye ki bakin gate and i will wait u there okay?” Dai dai gate din gidan Aliyu ya tsaya ta bude motar ta sauka sannan ta shiga compound din tana tafiya a hankali, wayar har ya katse ya sake kira, kafin ta

shiga parlor ya sake katsewa, a nan gabanta ya hau faduwa tana tsoron kada ta sake ganin Aunty, da sauri ta wuce sama ta bude dakin da su Maimoon suke, duk suka juya suna kallonta, Maimoon tace “Kin fasa tafiyar kenan” karasawa tayi tace “Na mance na tafi da wayarki ashe a jakata, kuma ana ta kiranki amma dai ya katse..” Maimoon ta xaro ido tana kallon wayar da Jiddah ke mika mata tace “Lahh ashe wayar na gun ki na xata yana caji, wa ke kira?” Lkci daya mood din Maimoon ya canxa ganin me kiranta, cike da damuwa tace “Ni dai na shiga uku, wai ya Aliyu ke kirana, to me yasa?” Dagawa tayi ta kai kunne fuska daure, Kafin tace komai yace “Kuna ina?” Ta turo baki tace “Aa muna nan gidan amarya yaya…” Yace “Ke da wa da wa?” Tace “Ni, Aunty Safiyya, Aunty Ramlah, Nafisah, Aisha da Yusra

, sai Jiddah amma ita xata wuce gida ynxu, mu kuma muna son mu kwana ne” murya can kasa tace suna son su kwanan don bata san me xai ce ba, instead sai taji yace “Wacece xata tafi?” Ta kalli Jiddah da har ta nufi kofa ta fita, tace “Jiddah” Yace “Xata tafi ina?” Maimoon tace “Wai gida, tace ita baxata kwana ba” yace “Gidan da babu kowa?” Maimoon tace “Nima dai haka na gani… Amma Ummi na nan ai” Yace “Bata wayar” ta mike da sauri tace “Toh bari in kai mata ta fita yanxu” Yace “Do that quickly” cikin hanxari Maimoon ta fita dai dai second stairs taga Jiddah a tsaye tana

kallon parlor, Jiddah da bata ma san Maimoon ta fito daki ba, ta sauke idonta daga kallon da take ma 3 seater din parlon, ta ci gaba da sauka downstairs a hankali, Maimoon ta kwalo mata kira tace “Yaya xai maki magana” Daga haka ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar, amsa Jiddah tayi tana kallon screen din sannan ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace “Ina xa ki?” Tace “Gida” yace “Toh kar ki kuskura ki fita daga gidan nan ba tare da su Maimoon ba” shiru tayi ta ma rasa abinda xata ce, a

takaice yace “Bata wayar” Ta mika ma Maimoon wayar, daga daya bangaren yace “Nafisah dama xan yi ma magana kai mata wayar yanxu” Maimoon tace “Toh” daga haka ta juya ta tafi kai ma Nafisah waya a daki ranta fari tass bai ce su wuce gida ba duk da ta sanar da shi xa su kwana, Gaba daya mood din Jiddah ya canxa, ta ci gaba da sauka a hankali ta nufi kofar parlon ta fita, har sannan Ali na jiranta bakin gate, ta karasa kusa da motar don glass a sauke yake, cikin sanyin murya tace “Kayi hakuri don Allah brother dinmu yace mu kwana a nan kawai” Yace “Ohh really, to shkkn Jiddah, can i get ur digit plss?” Tace “Bana rike waya ae” ya xaro ido yana kallonta, yace “Saboda me?” Sincerely tace “Karatu nake yanxu”

kallonta yake yi da kyau, but come to think of her age kamar ynda ya kiyasta a ransa sae ya yrda da abinda tace, ya shafa lallausan gashin kansa yace “Then how will i be contacting u?” Tayi shiru, yace “Amma yar uwarki na da waya ita ai” Tace “Ehh ai ta girmeni” Yace “Ohh ok, gobe da karfe nawa xa ku bar nan?” Tace “Nima dai ban sani ba” Yace “Toh xanyi sallama da safe hope it’s okay?” Ta xaro ido tace “Aa idan yayanmu na nan fa” yace “Ohk sai yayi maki fada?” Ta gyada masa kai, shiru yayi, can yace “Okay then xan turo kanwata Khaleesat, she is just ur mate i guess, and kuna yanayi da ita sosai, ranan farko da na ganki a balcony daga nesa sai na ga kamar ita but i know i was mistaken coz tana boarding schl…

She is available now sun yi hutu, and i want u two to be frnds…” Tayi murmushin karfin hali tace “Toh” Yace “Let me not keep u standing in sha Allah xata shigo da safe sai ta baki waya mu yi magana okay?” a hankali tace “Allah ya kai mu” murmushinsa me kyau yyi mata ta juya ta shiga compound din gidan, a parlor ta ci karo da Aunty da kawayen Aneesah rike da warmer din abinci iri iri sun fito daga kitchen, Da mamaki Aunty ta tsaya tana kallon Jiddah, can ta ajiye babban warmer din hannunta tana kallon hanyar stairs ta nufota, Jiddah ta fara komawa baya gabanta na

faduwa, Aunty na nunata da yatsa tace “Wai ke wacce irin natattciya ce mayya? Ban koreki daga gidan nan ba kika kara dawowa don ubanki, kin ga wani bare a nan banda ke? Duk fa babu bare a gidan nan wllh, Me kika sake dawowa yi banda rashin xuciya don Allah, idan muna abu na family me yasa xaki dinga cusa kanki, wllh tunda nake ban ta6a ganin me naci mara xuciya irinki ba.. ke a wa xaki biyo jama’a xuwa gidan nan idan ba kin yada xuciyarki kare ya lashe ba, bamu hada komai dake ba fa, babu dangin iya balle na baba, yar talakawa dake ma idan ba kaddara ba da kuma Aliyu da ya ja mana wannan masifa da fitina me xai shigo dake irin wannan family din, ke kin ma samu waje ko waiwayon kauyanku baki yi kin shigo birni

ko…” Jiddah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, duk kawayen Aneesah na tsaye parlon suna kallonsu da alamar abun ya masu dadi, Aunty ta bude kofa ta hankadata waje a fusace tace “Fita ki bar gidan nan don uwarki, wllh kika sake dawowa sai na kwara maki tafasasshen ruwan xafi sai dai duk abinda xai faru ya faru” Juyawa Jiddah tayi ta fara tafiya, taji xuciyarta yayi mata rauni sosai, tun da aka fara shirin kai amarya dama tace ita baxata ba amma Hajja tayi ta fada wai ita ma xata fara koyon

mugun hali irin nasu Aisha da Maimoon, xata fara yi ma mutane musu da taurin kai, haka ne yasa bata sake cewa komai ba aka shirya da ita aka tafi kai Aneesah, banda wannan bata tashi da intention din bin yan kai amarya ba don karatu ma tayi niyyar yi idan an tafi, da gefen hannunta ta share hawayen da ya gangaro fuskarta me xafi, tana fitowa kofar gida ta nufi titi da kafa, ta fi minti goma a tsaye tana jiran adaidaita sahu kafin ta samu daga karshe, har suka isa gida hankalinta baya jikinta, ta sauka ta basa kudi, snn ta juya xata shiga gate dai dai fitowar Aliyu

daga gate din rike da makullin motarsa, kana ganin fuskarta kasan tayi kuka duk da ba me yawa ba, daga sama har kasa yake kallonta, yace “Tafi wajen motata ki jirani” cikin sanyin murya tace “Me xanyi a can? Don Allah ka barni in shiga gida” Yace “Are u questioning me?” Juyawa tayi ta nufi motar walking slowly, har ta isa gun motar ta tsaya, sai a sannan ya nufi motar ya bude back seat yana kallonta, hawaye ya kawo idonta tana kokarin ganin bai xubo ba cikin rawan murya tace “Don Allah ni baxan

shiga ba, ka barni in je inyi sallah” Ya dinga kallonta, sai kuma ta juya masa baya ta fara kukan dake cin ta, sai a lkcn maganganun Aunty ke mata xafi sosai a xuciyarta, taji she really wants to go back to Hansai, don ita kadai ce idan tayi mata bata kuka kuma bata Jin xafi a ranta tunda a ko da yaushe kallon mahaifiyarta take mata, ita ta taso ta gani a matsayin baabarta, kuma ita take ma kallon baabarta, Kallonta Abuturrab ya dinga yi cause kana jin yanda take kukan kasan she is hurt, bin wajen yayi da kallo sannan ya kama hannunta ya shigar da ita motar, ta hade kanta da gwiwa tana rera kuka, ya xauna gefenta ya kulle motar yana

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button