Uncategorized

WAYAFI SONTA 17


Page 17

“”””Batare data kallesaba tace namanta nima! Ok shikenan tunda kin manta Zaki iya tafiya”to Amma…amma what?”pls you can go! nadawo agajiye Zaki sani surutu” bejira cewar zainab d’in ba”yakoma bed room nasa… zainab ta tab’e baki had’e da tashi ta fice dg parlourn”

Waiting parlour ta nufo” cike da d’oki sukayi clash da hjy ta fito dg kitchen”ah ah zainab yanzun Nike cewa kina Ina?”naje wani gurine!zaro Ido hjy tayi had’e da cewa Masha ALLAH !Kai alhmdllh” ja’irah shine sai yanzun nikikayi mun mgn? Murmushi zainab tayi had’e da rungume hjy tace ah ah wlh banfi 40 minit dabara mgn ba!dalilin yankewa da wuk’a”tafad’a tana nunawa hjy ciwon dataji..

   Subahanallahi kice jin ciwo yyi dad’i” inafatan nice farkon jin maganar ki zainab?”

Murmushi zainab tayi tace ah ah hjy” Yaya haidar ne….tsab cikin kunnen faruq ,Wanda shogowarsa kenan yadawo dg office! Azuciyarsa yace itama tanson Yaya kenan ,tunda gashi tace shine yafara jin maganar ta”

Congrat! zainab ALLAH ya kyauta gaba!juyowa tayi tana murmushi tace ameen “saidai murmushin yatsaya sbd ganin yadda faruq yyimata,sbd tasaba Yana sakar Mata fuska ,Yana Mata murmushi dakuma kalaman soyayya masu dad’i to meke faruwa Kota Masa wani abune??” Gsky kije gun mamana taji kin fara mgn Kota sanine?” Cewar hjy tana nufar kicin” da sauri zainab tadawo tunaninta tace ah ah bata saniba bara naje to…

Fad’in farin cikin da anty mariya da Baffa sule sukayi b’ata lokacine…atake anty mariya ta Kira mama…mama wacce ke tsakar gd”tana tuka tuwon dare”tacewa khalifa yamik’o Mata wayarta”

Da sallama mama tafara!anty mariya tace albishirinki!mamana!! ZAINAB! mama tafad’a da k’arfi had’e da saka handsfree” da sauri baba da goggo haule suka fito jin an ambaci zainab”mama Kinga ikon ubangiji ko?” ni zainab Ina mgn da bakina !mama tashare hawayen farin ciki tace eh zainab y’an bakin ciki saidai su mutu! ALLAH yyiwa rayuwarki albarka yatsaremunke kinji aduk inda Zaki shiga!ameen mamana “Ina baba dasu yah Ahmed da khalifa?”Ahmed baya nan khalifa gashinan ,babankima…. zainabbbbbbb! Cewar baba Yana matsawa kusada mama ya karb’i wayar…. sum sum goggo haule ta koma d’akin ta” yyinda baba da mama da khalifa sukayita waya da zainab..har kud’in anty mariya suka k’are….

     Mama da kanta tasaka hijab taje gdnsu (marigayi Umar) tasanarwa Inna da Maryam wannan labarin farincikn”kafin mama ta Kira anty mariya , zainab sukayi mgn da Inna dasu Maryam….nanma Saida kud’in mama yak’are tukum suka hak’ura da wayar…akan cewa insha ALLAH k’arshen wata zainab zatazo ganin gd….

 

 

     Zainab kuwa kwanan farin ciki tayi,sunraba dare  itada elham suna fira”kafin su kwanta!

Washe gari “kasan cewar week end zainab tare da hjy suka had’a break fast! Amma zainab bata yarda tayi break tareda Yan gdn ba”tunda suka gaisa da Alh yyimata murna ,ta wuce dakinsu ,ko faruq bata ganiba…

Da misalin k’arfe 9:am sanye take da yunifoam dark brown na islamiyya tana tafiya zata islamiyya…  hango haidar tayi za’a bud’e Masa mota” da k’ananun Kaya ajikinsa..sauri ta k’ara..har anbud’e k’ofar motar zai shiga , zainab nakawowa” Yaya haidar!fasa shiga motar yyi”Sarai yagane zainab ce “Amma sai yajuyo Yana cewa wacece?”

 Sunkuyadda Kai tayi had’e da cewa Ina kwana?”lfy qlau meye dalilin ki na tsayar Dani?” Yafad’a in a serious tone! Gabanta yafad’i kadafa yamata wata fassarar!

Dakewa tayi itama fuska bbu walwala tace natuna abinda kamun yasaka na harareka”uhum inajinki to?”to dama….dama bakai bane kagayamun bak’ar mgn aranar da zamuje India!

Shiyasa ki harara na?” Eh “uhum ba bak’ar mgn bace “shawara ce nabaki ,koki yarda da hakan ko karki yarda agurina fine! Zaki iya tafiya…baka hakura ba?”eh…. azuciyarta tace bazan koma baka hakuriba!saime inbaki koma bani hakurin ba?”

    Zaro Ido zainab tayi sbd tasan itadai azuciyarta tayi mgn ,Amma  gashi yaji…wani lallausan murmushi yasaki”har fararen hakoransa suka bayyana ,yace uhum yarinya kenan!kije islamiyya karki latti ,kinzo kin wani tsayardani kina sani mgn…insha ALLAH bazan koma tsayar dakaiba har nasaka  ka yawan mgn dg k’arshe nagode k’warai ALLAH yasaka da alkhairi akan taimakon dakamun akan lafiya ta….kirike godiyar ki,banaso nayine Dan ALLAH….bejira cewar taba yashige mota,ita Kuma ta wuce warta…*****************

 

Agajiye yadawo gdn ga yunwa sbd ko break fast beyiba!saidai kallo d’aya zaka Masa kasan Yana cikin farinciki sbd ayaune case d’in sa da Alh buba yazo k’arshe”yanzun haka anyankewa alh buba d’aurin Rai da Rai agdn yari…. awaiting parlour yaji tsit bbu kowa”.hakan yasa  yatsaya yad’an kwanta kan 3 seeter ya lumshe Ido Yana maida numfashi ahankali” ko takalmi becireba suna ak’afarsa!agefensa Kuma jakarsace ta zuwa office!

    Cike da nishad’i zainab ta fito dg kitchen “hannunta guda rik’e da d’ankwalinta”d’ayan hannun rik’e da plate d’in indomie taji serdine  sai k’amshi ketashi”tanata turiri….. atsorace taja da baya tana raba Ido! Sbd arba datayi da DSP haidar dake kallon ta tak’asan Ido… wannan ne karon farko dayagan ta bbu hijab ko d’ankwali”innalillahi! Tafad’a tana waige waige sbd ita ko motsin shogowarsa bataji ba”Kuma batayi zaton acikin shida faruq wani zai dawo yanzun ba , sbd tasan sai 6:da wasu mintina suke dawowa dg office!gashi dududu 4:43 pm” yanxun…datasan hakan    zaifaru dabata tsayaba gashi hjy tanagun barkan haihuwa” elham Kuma tana bacci ” ita d’aya ce….keeeeeeeee! Da sauri zainab ta ajiye plate din k’asa ta yafa d’ankwalinta” batare data kallesaba tace sunana ZAINAB!

     Tab’e baki yyi had’e da cewa bantambayeki ,dake nagadamar kiranki! Ina hjy?” Fuska d’aure tace taje gun barka! Ok me kuka dafa agdn?”

Ba’ayi girkiba”sai zuwa dare….kamar ya?” Mene can yake turiri abayanki?” Indomie ce! Kikace Kuma bakuyi girkiba?”eh yanzun nadafa!nikuma yunwa nakeji saikiyi Yaya Dani?”gabanta taji yafad’i ga wani tsoro yakamata kasancewar taga sukad’aine apart d’in”ko anty mariya tana nasu part d’in…

      Kallonsa tayi taga yatashi zaune Yana cire takalminsa”ke kiyi Dani yunwafa nace Miki inaji!” Zakaci indomie d’in ?” Kawo nagani inba jagwalgwalo kikayiba! Juyawa tayi ta d’akko tazo agabansa ta aje!jeki kamun fork”da ruwa…

Juice da swan harda cup takamasa “had’e da  fork d’in….bayan ta aje Masa tajuya! Kije ki sake dafa wata Mana! Ah ah nafasa ai” kekika sani” juyowa tayi ta maka Masa harara tayi wucewarta”

Girgiza Kai yyi sbd taganta” yacigaba da cin indomie d’in,data Masa mugun dad’i sosai dukda dai tayi yaji “Amma tas yacinye ” yatashi da niyar wucewa part d’in su,hjy ta shigo” da mamaki tace yau kadawo da gurine?”

Murmushi yyi yace eh hjy wlh munsami nassara akotu” yanxun dai alh buba anyanke Masa hukuncin d’aurin Rai da Rai agdn yari…ah ah Masha ALLAH ALLAH ya taimaka yatsare munku…ameen hjy ta! Bara naje nawatsa ruwa! Ina zainab?” Nagadai tafita! Yafad’a atak’aice” waya ajiye maka wad’an nan kayan?” Tafad’a tana nuna plate d cup had’e da juice din da zainab ta kamasa….

     Sosa Kai yyi had’e da cewa itace ta kamun ,tace bakuyi girkiba,Wai saizuwa dare” haba hjy pls kirik’a girki Koda yaushe mana !banji dad’i ba wlh nadawo da yunwa ,saidai indomie naci… ALLAH ko?” To ingirkin kakeso akai akai sai kayi aure…bece komaiba yawuce…Da dare Gurin k’arfe 8:45 pm haidar ne yashiga bedroom d’in hjy da sallama”

Hjy nazaune tana lazimi kan prayer mat” Zama yyi gefen gado” kafin yace nashiga kicin naga bbu ruwan zafi inason nasha cofee” gashi injin din gdn nan baya d’aukar heater!

Sai ayi Yaya yanxun?” Nidai bani zuwa kitchen yanxun tunda ba aikin mijina bane “wayama zanyi da Alh k’ila gobe yadawo…tashi tsaye yyi Yana latsa waya yace bani number d’in yarinyar nan nakirata ta azamun! Wake nan?” Sarai hjy tasan zainab yake nufi!

Yarinyar nan zainab” batada waya wlh dama inaso ko Kai ko faruq wani yasiya Mata waya Dan ALLAH” yarinyar nan nada kirki inajin dad’in zama da ita”

     Za’a siya Mata insha ALLAH! To shikenan kaje d’akin su itada elham ” saikace ta aza maka…tamakar yyi mgn saikuma yyi shiru kawai ya wuce”

Jiyake tamkar yahak’ura da Shan coffee d’in!

Clash yyi da zainab d’in da hijab ajikinta da alama dg wani guri take” tana ganinsa ta rusuna tace Ina wuni Yaya haidar? Kasancewar tunda yyimata taimakon biyan kud’i tasami lfy ” taji k’imarsa ta nunku aranta..”cikin cool voice yace lfylau”Ina kikaje?”batare data kallesaba tace dg part d’insu anty nike ! Ok kije kitchen yanzun kidafamun ruwan zafi tafashashshe…to! Tafad’a tana wucewa hanyar kicin d’in”

     Yabita da kallo ,shidai yarinyar ta na birgesa Gurin ladabi da girmama manya da alama tasami tarbiyya me kyau” dukda wani lokacin yalura tanada tsiwa!

Bayan sun tafasa ta juye a flus ta samesa a waiting parlour ta mik’a Masa” thanks yafurta can k’asan mak’oshi…washe gari zainab na dining area tana k’ara jajjera komai…. k’amshin turaren sa yadaki hancin ta,tana d’agowa suka had’a ido! sunkuyadda Kai tayi”tace Ina kwana?” Kintashi lfy?”bejira cewar ta ba”yanufi parlourn hjy Dan Mata sallama…hakanan kawai ta tsintsi kanta da had’a Masa tea”tafara shek’awa…yafito zai wuce!Yaya bazaka yi break fast ba?” Juyowa yyi fuska asake yace anajirana ne zainab! Pls ko tea ne kazo kasha gashima Ina shek’a maka”kallonta yakeyi bbu ko kiftawa”itakuwa saitaji kunya”jiyayi bazai iya yarfataba”dawowa yyi yaja kujera yazauna”yyinda zainab ke tsaye ta mik’a Masa cup d’in zata wuce….kizauna kijira nagama Mana cewar DSP Yana kurb’an tea d’in…ata kure ta zauna kanta d’uk’e”askul wane mataki kk?”NCE….gab dazai shanye hjy ta fito dg parlourn ta”da mamaki take dubarsu”amma Bata nunaba saima ta wuce abinta…tashi yyi batare da yakalli zainab dinba yace natafi! Allah yatsare…ameen yafad’a fuska asake…hjy dake kitchen duk tanajinsu cike da mamaki” tana wani murmushi…

 

 

*****************

 

Kwance tashi bbu wuya agurin Allah yau zainab kusan watanta guda kenan da dawowa India” yyinda ahankali ahankali suka Saba da DSP ,har fira intakama sunayi Kota Masa tambaya gameda aikinsa”ga yawan damuwa datayi sosai dashi,danma bata nunawa,shima anasa b’angaren hakane”har mamakin kansa yake akan damuwar dayakeyi akan zainab”yyinda faruq kuwa dg gaisuwa ko abinda yashafi y’arsa Babu abinda ke had’a shi da zainab….

Ayau yakama week end bbu aiki” su hjy da zainab na parlou suna kallo…wayar hjy tayi ringing” d’agawa tayi tana murmushi tace mutanan kaduna yakuke?” Kedai bari wlh to ai autar taki ta yadani” Allah sarki yaushe zatazo ne?” To gobe kenan Allah yakaimu yakawota lfy ” Yana nan lfy to zaa gayamasa….nan sukayi sallama…. zainab dake saurarensu hakanan  taji faduwar gaba”suna nan zaune haidar da faruq suka fito tare da alama wani guri zasuje…haidar yace hjy sannunku da hutawa!yauwa ,yanZun kuwa mukayi waya da antynku maimuna( k’anwar hjy ce ubansu guda) auta na nan tafe hutu ” tace insanar maka kaje Tasha kadaukota” kicin kicin haidar yyi da fuska yace haba hjy kinsan bansan shirme aikinnawazan Bari naje na d’aukota ! Ni wlh dama baninan zatazo banason takura….kirjin zainab yabuga sbd kalaman haidar to meyake nufi?” Ko budurwarce yarinyar….kana nufin bazakaje daukartaba ?” Cewar hjy!inkince naje Dole naje sbd bazan iya musu dakeba….hjy tace nasan haka Allah yyimuku albarka”dama nima banbada goyon bayan kajeba driver zaije insha ALLAH goben yad’auko ta… faruq Yana dariya yace to miye aciki Yaya Dan ka dauko babynk…..harara haidar yabankomasa,yasaci kallon zainab da tun d’azun yakeson suhad’a Ido Taki yarda….

Cikin sa’a suka had’a ido yyimata hararar Wasa da Mata nuni da hannu sun b’ata….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button