Sarauniya Akisatul Sauwara ta durfafi wani bangare daban na cikin gidan sarautar tayi ta kutsawa ta cikin wani surkuki mai lunguna da yawa har saida suka yi tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar wani gida.Koda masu gadin gidan suka hango Sarauniya Akisatul Sauwara tare da Yarima Lubainu sun tunkaro inda suke sai sukayi sauri suka bude kofar gidan tun kafin su iso.Suna isowa kuwa masu gadin suka risina suka gaida sarauniya.Ita kuwa ko kallonsu batayi ba ta kunna kai cikin gidan Lubainu na take mata baya.Babu komai a cikin wannan daki face kayna tarihi iri iri na kasar musamman abinda ya danganci kayan yaki kamar takubba,masu,Garkuwa da sauransu,kai harda kayan kyale kyale dana kawa kala kala.Nanfa Yarima Lubainu ya zama dan kauye ya kama kalle kalle da waige waige.Saida suka iso tsakiyar gidan suka iske kwalbar sihiri wacce aka dorata akan wani zagayayyen tubalin gini.A cikin wannan kwalba ne aka sanya Allon Sihiri.Nan take Lubainu yayi arba da wannan Allon Sihiri,ya dubi kwalbar da kyau yaga babu wata kofa ko huda a jikinta wacce za’a iya zura hannu a ciki a dauko Allon.Da isowarsu gaban kwalbar sihirin sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace,kayi iya kokarinka da duk abinda kake takama dashi wajen fasa wannan kwalba don dauko wannan Allon sihirin mu ga abinda zai faru.Ai kuwa kafin ta gama rufe bakinta tuni Yarima Lubainu ya dauko wani katon barandami ya sari wannan kwalbar sihirin da dukkan karfinsa.Maimakon kwalbar ta dare ko ta tarwatse sai shi barandamin ya karye bal,ya rabe gida biyu.In banda tarwatsin wuta daya tashi akan Gilashin babu abida ya sameshi.Al’amarin dayai mutukar girziza Yarima Lubainu kenan yaja da baya a dan tsorace.Ita kuwa sarauniya Akisatul sauwara sai ya bushe da dariya ta sake duban Yarima Lubainu tace to ai saika jarraba Karfin sihirin tsafinka mu gani.Lubainu bai karaya ba sai ya matsa dafda kwalbar sihirin ya shiga karanta wadansu dalasimai na tsafi yana shafar kwalbar da tafin hannunsa.Kwatsam sai yaji wata irin iska mai karfi ta sureshi ta baya ta gwarashi a jikin bangi ya fado kasa a galabaice. Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a karo na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya kai Lubainu kamar yadda na gaya maka da farko babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya isa ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan kwalba face ni.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta shafeta da hannunta na hagu.Take kwalbar ta rabe gida biyu kamar an yanke lemon bawo.Kawai sai ta sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace dashi,zo kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa Allon idanun.Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake gida biyu.Kuma bazai taba karantuwa ba a haka face an jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi ajiyar numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun karayar zuciya yace,Ai wannan Allon dake hannunki bashi da wani amfani idan ba’a samo daya Allon bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara tayi murmushi tace to ina tabbatar maka da cewa idan ma an samo Allon na biyu an hada da nawan rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an hada dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar da Allon cikin wannan kwalbar.Take kwalbar ta koma ta manne tamkar bata taba rabewa ba biyu.Akisatul Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga cikin wannan gida Lubainu yabita da sauri.Nan dai suka yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima Lubainu sai ya tsaya.Akisatul Sauwara ta juyo tana mai yi masa wani kallo mai dauke da murmushi da ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma izuwa masaukinka ka sake hutawa,amma ina gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na bayan turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in yaso gobe da safe muyi haramar tafiya.Tana gama fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin turakarta kuyangi na gyara mata hanya.Yarima Lubainu ya juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi masaukinsa zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi ko kuma KAUNA.Kamar yadda Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada haka al’amarin ya kasance wato da yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa jini dake bayan turakarta.Yana isowa wajen sai ya iske sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar yaki rike da takobi.Yana isowa sai shima aka miko masa sulke takobi da garkuwa.Ba tare da gardamar komai ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki karbar garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai shawartarka daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya baka mamaki.Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke baki rike garkuwa ba a matsayinki na ‘ya mace nima ba zan rike ba.Akisatul Sauwara tace,shi ke nan muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura.Kafin Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka tsalle ta kawo masa wawan sara a kafada.In ba don Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin tsananin zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu.Nan fa suka kacame da azababben yaki ta rinka kai masa mugayen hare hare da wani irin azababben zafin nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi mamaki tun da yake haduwa da mazaje bai taba haduwa da mai kamar jarumtakarta ba.Bisa dole shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare haren nata amma sai yaga duk da haka tana neman kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi sakaki zata iya gamawa dashi.Nan fa shima ya fara maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama abin tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin azababben yakin dasu sarauniya ke yi.Saida suka dauki dogon lokaci a haka dayansu bai sami nasarar koda shafar jikin abokin gwaminsa ba.Al’amarin dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin shi kuwa ya fara haki.Koda ya fuskanci cewa lallai zaiji kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon fadan ya hada dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai ya shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa amma tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta guda tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi tsalle sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi wuf ya mike tsaye Zumbur.Yana mai gyara tsayuwa a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin tafiyar da zanyi tare dakai domin na gamsu cewar kai jarumi ne na kwarai.Koda jin wannan batu sai ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar jarumtakarsa.Amma sai ya boye fushin nasa bai nuna mata ba.A wannan lokaci duk sun jike Sharkaf da gumi don haka sai ta shawarce shi akan yaje yayi wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai gobe da safe yayin wannan tafiya.Nan take kuwa Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya bayar gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda itama ta fada cikin wasi wasi domin ta kasa tantance irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na gajiya?Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da zata kaita turakarta.Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin tafiya,kuma bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta ba.Su biyu rak suka fice daga birnin Rauhul Bagadar bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran gari. Prince Auwal Auwzab Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka sakarwa dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya basu yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin ko kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu wanda yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata mu yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu nake son na sanar dake hakan amma sai na kasa don kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai tun kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni da kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi kunnen doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a karo na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin sa’a kuwa sai suka hango wata fadama a can gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar akwai duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu suka kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance jakar guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin kafashi.Al’amarin dayai mutukar baiwa Yarima Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba? Ai mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a wannan fannin.Sa’adda Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar yadda nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya ta ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi ‘yar guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba zai iya wulakantashi ya wuce abinsa.Ni yanzu na ajiye karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina daidai da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta biya mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba da bina har izuwa lokacin da burina zai cika?Ki tuna fa cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai zuwa goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin Allon Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi murmushi tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai zama gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi.Abida ya bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin bukatarsa ta biya?Abinda zuciyarsa keyi masa wasi wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan tafiya?A zahiri dai bai ga wani abu dazata amfana dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta ba.Nan dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya Akisatul Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya kwance jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka fara jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye masu shawagi a sama.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da sauri ta tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke shirin biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin mamaki Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma kin dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace naje na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara kokarin cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga cikin dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne yaji yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama ci.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji takun sawu a bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare takobinsa ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda ya tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye da wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce ta bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri da sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya taso a rayuwarsa bai taba ganin ‘ya mace haka ba a rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya danne zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da cikakkiyar lafiyar da zaiji wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk da cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta a hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi cikin murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya ta? Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi yake sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka sai Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa suka zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin dumin tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai ya mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan ya dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna daf da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar taku uku a tsakaninsu.Tsawon ‘yan dakiku dayansu bai ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi ya dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki kwanta kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin bacci? Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin daji.Tabbas ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan dalili ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda nake so dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta cikin alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya bazan iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani cewa babu wani ‘da namiji dazai ganki a cikin wannan yanayi bai rude ba ya kamu da sha’awarki da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba sanin ‘ya mace ba kuma wanda yake nisantarku dole ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda baka taba sanin ‘ya mace ba nima ban taba sanin wani ‘da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina mai tuna maka cewa samun yin barcina yana gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin tantin taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa Yarima Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga cikin tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina Akisatul Sauwara ke kwance ya kwanta.Yana kwanciya sai zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin gwagwarmayar dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa barci ya saceshi har yana munshari bai sani ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa sai ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda ke kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba akan shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan shimfidar wato an cireshi daga cikin kwalbar data lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije ya dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da mahaifinka ya baka kafin ka baro gida.Cin amana ne idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu zaka sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama aiyana hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji motsin taba.Al’amarin d yayi matukar bashi mamaki kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi gangancin barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai Yarima Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya wanke fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan abu dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe a cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya da daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye jarrabar tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun siffarta kuma ya kamu da matukar sha’awarta.Bisa mamaki sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar Yarima Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi kokarin guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin sa’adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin ya rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma yaji bata amsa ba.Al’amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi nemanta kuma azo a sace wannan Allon Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon Sihirin zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin da Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta juya da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi farauta ta harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa haba ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da kin sanar daniba. Koda ya hangota sai ya mike zumbur!Da sauri ya tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaya zaki tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba?Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka bari mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a saukake.Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara kokarin fisge wannan tsunstu data harbo.Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta ki don haka sai ya zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna suka kama cin nama tsuntsun.Tsawon yandakiku suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin da dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar dake kadawa.Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,idan baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin dayasa kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin ban kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki? Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da daria sannan tace,tabbas kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana sami nutsuwa.Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba hakurinka shin zaka kasance mai tsare mutuncina bisa alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juma a cikin wannan tafiya?Tabbas ka kiyaye wannan jarrabawa ka hayeta.Dalili na biyu kuma wanda yasa na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine domin na jarraba amanarka na gani shin zaka sace Allon Sihiri na ne ka gudu?Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka sace Allon Sihirin ba alhalin kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo shi.Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da sannu zamu kai ga wannan matsayi.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata idanu.Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar guzurinsa.Itama Sarauniya Akisatul Sauwara sai mike tsaye ta bishi izuwa cikin tantin ta shiga kimtsa na ta kayan.Har suka gama kimtsa komai basuce da junansu kala ba.Nan take suka hau dawakansu suka nausa cikin daji suna masu cigaba da tafiya.Sai da suka shafe sa’a hudu da rabi suna tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan Yarima Lubainu ya matso kusa da Sarauniya Akisatul Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta yace,waishin tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da muka nufa?Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa dadina dakai kenan ka cika zumudi da gaggawa.Ai idan kayi hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru bata kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa’a hudu suna tafiya.A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a bakin wani katon dutse.Anan suka kwana kashe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu riski wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu mugayen dabbobi ko kwaruka saidai kaga sun yi musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA!Kuma RUWA BA SA’AN KWANDO BANE.A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka Yarima Lubainu ya hango wani babban gari a gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu ya wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine ginen birnin cikin al’ajabi.Koda Sarauniya Akisatul sauwara ta lura da halin da yake ciki sai ta bushe da dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani kunya mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga cikin birnin tukunna.Koda jin wannan Batu sai Yarima Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin yanzu kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine Birnin Kimras inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara ta jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka sai abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi saboda Sarki Darmanu ba karamin shaidanin Mutum bane.A yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin wani abu domin ya cutar damu,don bani da tabbacin cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka zo masa da ita.Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da iya yaki KARE JINI BIRI JINI mukeyi.Sau tara muna fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki.Bisa sa’a ne kawai na samu na tsira daga sharrin tsafinsa sabodatsarin dana samu tun daga kakannina.Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta suna daf da shiga cikin birnin ne,Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a bayansa,shima zai shiga cikin birini.Cikin Ladabi Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu kallo ya lura cewa baki ne don haka saiya dubesu yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne a garin nan ko?Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin yanayi mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da gani kun fito daga babban gida kuma kun sami tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don kada ku fada cikin tarkon maketacin sarkinmu.Ina mai sanar daku cewa bisa al’adar wannan mugun sarki namu duk bakon daya shigo garin nan kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a kaishi kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a duniya sannan zai tsira da rayuwarsa.Yanzu zan taimake ku ba bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda zai ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso indan gari ya waje sai ku saje da ‘yan gari ku aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama fadin hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu yace,idan sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar ‘yar uwar taka saiya rabaka da ita har abada.Koda jin haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai jinjina al’amarin ba tare da yace kala ba.Nan dai tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai bin wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin.Su kuma suka ci gaba da jan limzamin dawakansu a hankali suna yin tafiyar san’da suna waige waige cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin da suka yi ‘yar doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin zai iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka turoshi ya yaudare mu ya cutar damu.Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da Yarima Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai ya tsaida nasa dokin suka kurawa tsohon idanu kawai yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace ‘ya’yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka kuka daina tafiya?Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon banza!bakin mayaudari na gane ko kai waye.Maza ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu tattauna bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da tsohon yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara saiya bushe da mahaukaciyar dariya cikin karfin murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza na take ya rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar shigar yaki.Sarki Darmanu ya kasance katon mutum mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma gashi kakkaura mai murdadden jiki gami da tarin kwanji da jijiyoyi.KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA.Wadansu bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe.Rigar dai Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon wando da dogayen takalma duka na bakin karfe.A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa ce wadda akayi ta da zallan dutsen lu’u lu’u mai nauyin gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya rabata da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya rike.Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro birnin ki naga duk abinda ya faru tsakaninki da Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa sa’adda kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin Allon Sihirin dake hannuna.Tabbas dake dashi kuma sami tabin hankali har da kuke tunanin zan karbeku hannun bibbiyu na yarda da bukatarku.Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan rana wacce zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki taho har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na gano yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar dakika adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu daga sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan hallaku na dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na biya tawa bukatar dashi.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama kamar an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk su biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk su biyun suka kaucewa saran suk fado kasa daga kan dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar tuffa.Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai takubban nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu suka ruguntsume da azababben Yaki. (Shegen kaya Uban mayaudara) ,ya zama cewa yana kai musu sara da suka cikin bakin zafin nama da jarumtaka ta ban al’ajabi.Duk da tsananin jarumtaka irin ta Lubainu data Sarauniya Akisatul sai gashi sun raina kansu domin basa iya maida martani saidai kokarin kare kansu daga mugayen hare haren da yake kai musu.Al’amarin dayai matukar firgita Sarauniya Akisatul Sauwara ke nan,kuma ya bata matukar mamaki domin ada can ta san cewa karfin damtsenta da iya yakinta yazo iri daya sak dana Sarki Darmanu,amma sai gashi yanzu labari ya sha bambam.Koda Sarki Darmanu yaga ya fisu zafin nama da jarumtaka sai ya kara zage dantse a kansu ya ci gaba da kuntatasu yana mai sauya salon fada,wato ya hada da kai musu naushi da hannu da kafa.Faruwar hakan keda wuya sai ya fara samun lagonsu.Nan da nan ya hada musu jini da majina.Idan ya naushe su a ciki sai cikinsu ya kulle sunyi ihu sun kife kasa.Idan kuma a fuska ya naushe su sai kaga har sama sukeyi suna fadowa kasa a galabaice.Maimakon yasa takobinsa yayi musu kisan gilla sai ya rinka yankarsu a sassan jikinsu jini na tsartuwa da feshi suna ihu da kururuwa sakamakon tsananin zafi da zogin da suke ji har saida suka sami sama da raunika biyar a jikinsu.A sannan ne suka zube kasa wanwar suna numfashi sama sama kamar zasu mutu suka kasa koda mikewa tsaye.Koda Sarki Darmanu yaga ya sami wannan gagarumar nasara sai ya tsaya cak! a kansu yana mai kyalkyala dariyar mugunta da farinciki.Daga can kuma sai ya nufi kan Sarauniya Akisatul Sauwara da nufin ya lalube jikinta ya dauke wannan Allon Sihirin nata.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji Yarima Lubainu ya gabza masa mahaukacin naushi a fuska.Saboda karfin naushin saida yai tsalle sama da baya yaje ya gwaru da wata bishiya ya fado kasa a matukar galabaice a lokacin da hancinsa da bakinsa ke yoyon jini.Kafin Sarki Darmanu ya yunkura ya mike tsaye tuni Lubainu ya dako tsalle a sama ya doki cikinsa da guiwar kafarsa ta dama.Take wani gudan jini yai fitar burgu dagacikin bakin Darmanu kawai sai ya koma kasa ya baje sumamme.Da kyar da jan ciki Yarima Lubainu ya karasa inda Sarauniya Akisatul Sauwara ke kwance ya rinka yagar rigar jikinsa yana daure sassan jikinta inda ta sami raunika don tsaida zubar jini.In ba don yayi hakan ba cikin gaggawa da tabbas zata iya rasa rayuwarta.Bayan ya gama ceton rayuwarsa sai ya fara kokarin daddaure nasa raunikan sannan ya sake jan ciki ya koma inda Sarki Darmanu ke kwance ya cire dukkan gurayen tsafin dake jikinsa ya mai dasu nasa jikin,kuma ya dauke takobin sarki Darmanu ya koma can inda Akisatul Sauwara ke kwance ya taimaka mata ta mike zaune ya jingina bayanta a bayan wata bishiya.Faruwar hakan ke da wuya sai Sarki Darmanu ya farfado daga dogon suman da yayi.Koda ya bude idanunsa yaga babu takobinsa a kusa dashi kuma ya shafa jikinsa yaji duk babu guraye da layunsa na tsafi,sai ya takarkare ya kwarara uban ihu na bakin ciki da takaici,amma sai Yarima Lubainu ya tari numfashinsa yana ma daka masa tsawa yace,yakai wannan sarki kayi sani cewa a halin yanzu duk tasirin tsafinka yana hannuna tunda na mallaki takobinka da dukkan gurayenka na tsafi.Abinda nake so dakai shine ka bamu hadin kai yanzu mu tafi izuwa fadarka ka kirawo likitocinka suyi mana magani a raunikan dake jikinmu,sannan kuma ka bamu hadin kai bisa abinda muka zo nema.Idan kaki bin umarnina koka nemi ka shammace mu kayi mana wani tuggun zan fille maka kai da takobinka sannan mu shiga har cikin fadar taka mu bincike ko ina da ina har mu gani inda ka boye Allon Sihirin naka mu daukeshi mu kara gaba.Lokacin da Yarima yazo nan a zancensa sai kwallar bakin ciki ta ciko a idanun Sarki Darmanu.Bisa dole ba don son ransa ba ya mike tsaye ya wuce gaba,shi kuma Yarima Lubainu sai ya goya Sarauniya Akisatul Sauwara a bayansa saboda ba zata iya takawa ba da kafafunta suka bi bayan Sarki Darmanu don shiga cikin Birnin Kimrasa.Maimakon Sarki Darmanu yabi hanyar kwarai ta zuwa gidan sarautar tasa sai yabi wannan barauniyar hanya saboda kada asirinsa ya tonu jama’ar gari su gane cewa yau fa AN CI SHI DA SHI.’Yar gajeriyar tafiya sukayi sai gasu sun bullo a wata kofa dake can bayan gidan sarautar.In banda Sarki Darmanu babu wani mahaluki wanda yake bi ta cikin wannan kofa.Shima yana amfani da kofar ne kawai idan zai gabatar da al’amuransa na sirri.Tun daga nesa Sarki Darmanu yayi kamar dawo ne cikin nasarar samo abokan gabarsa,domin yana tafiya ne cikin tunkaho da izza kamar yadda ya saba a duk sa’adda ya dawo daga rangadi.Nan dai ya wuce kai tsaye ta cikin wannan koda ta gaban dakarun dake gadi.Duk da cewa dakarun sun fahimci abinda ke faruwa sai da suka yi mamakin abu daya.Ba wani abu suka yi mamaki ba face ganin takobin sarki Darmanu a hannun bakon dazo dashi.Ita dai wannan takobi ta Sarki Darmanu ta kasance sihirtacciya,kuma itace sirrin dukkan karfinsa na damtse dana sihiri.Ma’ana karfin damtsensa na zahiri bai kai wanda takobin ke kara masa ba.A duniya babu abinda Sarki Darmanu ke so sama da wannan takobi,kuma babu abinda daya dogara dashi sai ita ita.Ganin raunika a jikin Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara ne yasa hankalon masu gadin ya kwanta suka ratsa suka basu hanya suka wuce.Koda suka fara tafiya a cikin wannan gidan sarautar sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tsaida Lubainu tace,ya kai Lubainu ka sani cewa kowa Prince Auwal Auwzab Auwzab a gidansa sarki ne,baka tunanin cewa wannan mutumin bazai iya yaudararmu yanzu a cikin gidan nan nasa ya cutar da mu?Koda jin wannan batu sai Lubainu yayi murmushi yace ki kwantar da hankalinki yake Akisatul Sauwara ai mun gama dashi tunda kema kin tabbatar dacewar wannan takobi itace tasirinsa,ai babu abinda zai iya yi mana.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi ajiyar numfashi tace hakane amma ka rike takobin hannu biyu komai rintsi kada ka bari ta subuce maka.ALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part B Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a karo na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya kai Lubainu kamar yadda na gaya maka da farko babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya isa ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan kwalba face ni. Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta shafeta da hannunta na hagu. Take kwalbar ta rabe gida biyu kamar an yanke lemon bawo. Kawai sai ta sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace dashi,zo kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa Allon idanun. Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake gida biyu.Kuma bazai taba karantuwa ba a haka face an jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi ajiyar numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun karayar zuciya yace, Ai wannan Allon dake hannunki bashi da wani amfani idan ba’a samo daya Allon bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara tayi murmushi tace to ina tabbatar maka da cewa idan ma an samo Allon na biyu an hada da nawan rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an hada dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar da Allon cikin wannan kwalbar. Take kwalbar ta koma ta manne tamkar bata taba rabewa ba biyu.Akisatul Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga cikin wannan gida Lubainu yabita da sauri. Nan dai suka yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima Lubainu sai ya tsaya. Akisatul Sauwara ta juyo tana mai yi masa wani kallo mai dauke da murmushi da ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma izuwa masaukinka ka sake hutawa, amma ina gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na bayan turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in yaso gobe da safe muyi haramar tafiya. Tana gama fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin turakarta kuyangi na gyara mata hanya. Yarima Lubainu ya juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi masaukinsa zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi ko kuma KAUNA. Kamar yadda Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada haka al’amarin ya kasance wato da yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa jini dake bayan turakarta. Yana isowa wajen sai ya iske sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar yaki rike da takobi. Yana isowa sai shima aka miko masa sulke takobi da garkuwa. Ba tare da gardamar komai ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki karbar garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai shawartarka daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya baka mamaki. Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke baki rike garkuwa ba a matsayinki na ‘ya mace nima ba zan rike ba. Akisatul Sauwara tace,shi ke nan muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura. Kafin Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka tsalle ta kawo masa wawan sara a kafada. In ba don Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin tsananin zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu. Nan fa suka kacame da azababben yaki ta rinka kai masa mugayen hare hare da wani irin azababben zafin nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi mamaki tun da yake haduwa da mazaje bai taba haduwa da mai kamar jarumtakarta ba. Bisa dole shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare haren nata amma sai yaga duk da haka tana neman kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi sakaki zata iya gamawa dashi. Nan fa shima ya fara maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama abin tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin azababben yakin dasu sarauniya ke yi. Saida suka dauki dogon lokaci a haka dayansu bai sami nasarar koda shafar jikin abokin gwaminsa ba. Al’amarin dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin shi kuwa ya fara haki Koda ya fuskanci cewa lallai zaiji kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon fadan ya hada dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai ya shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa amma tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta guda tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi tsalle sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi wuf ya mike tsaye Zumbur. Yana mai gyara tsayuwa a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin tafiyar da zanyi tare dakai domin na gamsu cewar kai jarumi ne na kwarai. Koda jin wannan batu sai ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar jarumtakarsa. Amma sai ya boye fushin nasa bai nuna mata ba. A wannan lokaci duk sun jike Sharkaf da gumi don haka sai ta shawarce shi akan yaje yayi wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai gobe da safe yayin wannan tafiya. Nan take kuwa Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya bayar gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda itama ta fada cikin wasi wasi domin ta kasa tantance irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na gajiya? Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da zata kaita turakarta. Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin tafiya,kuma bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta ba.Su biyu rak suka fice daga birnin Rauhul Bagadar bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran gari.ALLON SIHIRI Littfina na biyu(2) Part C Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka sakarwa dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya basu yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin ko kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu wanda yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata mu yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu nake son na sanar dake hakan amma sai na kasa don kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai tun kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni da kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi kunnen doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a karo na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin sa’a kuwa sai suka hango wata fadama a can gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar akwai duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu suka kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance jakar guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin kafashi. Al’amarin dayai mutukar baiwa Yarima Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba? Ai mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a wannan fannin.Sa’adda Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar yadda nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya ta ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi ‘yar guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba zai iya wulakantashi ya wuce abinsa. Ni yanzu na ajiye karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina daidai da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta biya mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba da bina har izuwa lokacin da burina zai cika? Ki tuna fa cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai zuwa goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin Allon Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi murmushi tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai zama gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi. Abinda ya bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin bukatarsa ta biya? Abinda zuciyarsa keyi masa wasi wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan tafiya?. A zahiri dai bai ga wani abu dazata amfana dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta ba.Nan dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya Akisatul Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya kwance jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka fara jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye masu shawagi a sama.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da sauri ta tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke shirin biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin mamaki Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma kin dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace naje na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara kokarin cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga cikin dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne yaji yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama ci.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji takun sawu a bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare takobinsa ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda ya tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye da wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce ta bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri da sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya taso a rayuwarsa bai taba ganin ‘ya mace haka ba a rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya danne zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da cikakkiyar lafiyar da zaiji wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk da cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta a hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi cikin murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya ta? Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi yake sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka sai Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa suka zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin dumin tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai ya mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan ya dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna daf da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar taku uku a tsakaninsu.Tsawon ‘yan dakiku dayansu bai ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi ya dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki kwanta kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin bacci? Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin daji.Tabbas ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan dalili ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda nake so dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta cikin alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya bazan iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani cewa babu wani ‘da namiji dazai ganki a cikin wannan yanayi bai rude ba ya kamu da sha’awarki da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba sanin ‘ya mace ba kuma wanda yake nisantarku dole ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda baka taba sanin ‘ya mace ba nima ban taba sanin wani ‘da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina mai tuna maka cewa samun yin barcina yana gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin tantin taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa Yarima Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga cikin tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina Akisatul Sauwara ke kwance ya kwanta. Yana kwanciya sai zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin gwagwarmayar dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa barci ya saceshi har yana munshari bai sani ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa sai ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda ke kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba akan shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan shimfidar wato an cireshi daga cikin kwalbar data lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije ya dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da mahaifinka ya baka kafin ka baro gida.Cin amana ne idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu zaka sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama aiyana hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji motsin taba.Al’amarin d yayi matukar bashi mamaki kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi gangancin barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai Yarima Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya wanke fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan abu dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe a cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya da daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye jarrabar tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun siffarta kuma ya kamu da matukar sha’awarta.Bisa mamaki sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar Yarima Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi kokarin guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin sa’adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin ya rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma yaji bata amsa ba.Al’amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi nemanta kuma azo a sace wannan Allon Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon Sihirin zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin da Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta juya da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi farauta ta harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa haba ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da kin sanar daniba.ALLON SIHIRI Littafi na daya(2) Part D Koda ya hangota sai ya mike zumbur! Da sauri ya tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaa zaki tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba? Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka bari mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a saukake. Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara kokarin fisge wannan tsunstu data harbo. Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta ki don haka sai ya zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna suka kama cin nama tsuntsun. Tsawon yandakiku suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin da dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar dake kadawa. Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,idan baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin dayasa kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin ban kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki? Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da daria sannan tace,tabbas kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana sami nutsuwa. Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba hakurinka shin zaka kasance mai tsare mutuncina bisa alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juna a cikin wannan tafiya? Tabbas ka kiyaye wannan jarrabawa ka hayeta. Dalili na biyu kuma wanda yasa na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine domin na jarraba amanarka na gani shin zaka sace Allon Sihiri na ne ka gudu? Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka sace Allon Sihirin ba alhalin kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo shi. Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da sannu zamu kai ga wannan matsayi. Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata idanu. Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar guzurinsa. Itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta bishi izuwa cikin tantin ta shiga kimtsa na ta kayan. Har suka gama kimtsa komai basuce da junansu kala ba. Nan take suka hau dawakansu suka nausa cikin daji suna masu cigaba da tafiya.Sai da suka shafe sa’a hudu da rabi suna tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan Yarima Lubainu ya matso kusa da Sarauniya Akisatul Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta yace,waishin tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da muka nufa? Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa dadina dakai kenan ka cika zumudi da gaggawa. Ai idan kayi hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru bata kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa’a hudu suna tafiya. A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a bakin wani katon dutse. Anan suka kwana washe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu riski wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu mugayen dabbobi ko kwaruka saidai kaga sun yi musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA! Kuma RUWA BA SA’AN KWANDO BANE. A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka Yarima Lubainu ya hango wani babban gari a gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu ya wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine ginen birnin cikin al’ajabi.Koda Sarauniya Akisatul sauwara ta lura da halin da yake ciki sai ta bushe da dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani kunya mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga cikin birnin tukunna. Koda jin wannan Batu sai Yarima Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin yanzu kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine Birnin Kimras inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara ta jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka sai abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi saboda Sarki Darmanu ba karamin 2shaidanin Mutum bane.A yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin wani abu domin ya cutar damu,don bani da tabbacin cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka zo masa da ita. Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da iya yaki KARE JINI BIRI JINI mukeyi. Sau tara muna fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki. Bisa sa’a ne kawai na samu na tsira daga sharrin tsafinsa saboda tsarin dana samu tun daga kakannina. Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta suna daf da shiga cikin birnin ne, Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a bayansa,shima zai shiga cikin birnin.Cikin Ladabi Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu kallo ya lura cewa baki ne don haka saiya dubesu yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne a garin nan ko? Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin yanayi mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da gani kun fito daga babban gida kuma kun sami tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don kada ku fada cikin tarkon maketacin sarkinmu.Ina mai sanar daku cewa bisa al’adar wannan mugun sarki namu duk bakon daya shigo garin nan kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a kaishi kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a duniya sannan zai tsira da rayuwarsa. Yanzu zan taimake ku zna bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda zai ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso indan gari ya waje sai ku saje da ‘yan gari ku aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama fadin hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu yace,idan sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar ‘yar uwar taka saiya rabaka da ita har abada. Koda jin haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai jinjina al’amarin ba tare da yace kala ba. Nan dai tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai bin wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin. Su kuma suka ci gaba da jan limzamin dawakansu a hankali suna yin tafiyar san’da suna waige waige cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin da suka yi ‘yar doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin zai iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka turoshi ya yaudare mu ya cutar damu. Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da Yarima Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai ya tsaida nasa dokin suka kurawa tsohon idanu kawai yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace ‘ya’yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka kuka daina tafiya? Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon banza!bakin mayaudari na gane ko kai waye.Maza ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu tattauna bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da tsohon yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara saiya bushe da mahaukaciyar dariya cikin karfin murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza nan take ya rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar shigar yaki. Sarki Darmanu ya kasance katon mutum mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma gashi kakkaura mai murdadden jiki gami da tarin kwanji da jijiyoyi. KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA. Wadansu bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe. Rigar dai Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon wando da dogayen takalma duka na bakin karfe. A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa ce wadda akayi ta da zallan dutsen lu’u lu’u mai nauyin gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya rabata da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya rike. Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro birnin ki naga duk abinda ya faru tsakaninki da Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa sa’adda kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin Allon Sihirin dake hannuna. Tabbas dake dashi kuma sami tabin hankali har da kuke tunanin zan karbeku hannun bibbiyu na yarda da bukatarku. Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan rana wacce zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki taho har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na gano yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar dakika adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu daga sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan hallaku na dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na biya tawa bukatar dashi. Koda gama fadin hakan sai Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama kamar an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk su biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk su biyun suka kaucewa saran suka fado kasa daga kan dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar tuffa. Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai takubban nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu suka runtsume da azababben Yaki. Shegen kaya Uban mayaudara Sarki Darmanu. 6 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part E Sannan su dauke mu mu ci gaba da tunkarar gidan Boka Darbusa.Yanzu ga dawakai nan guda biyu dana tanadar muku sai ku hau mu kara gaba.Ba tare da gardamar komai ba kuwa Lubainu da sarauniya Akisatul Sauwara suka hau wadannan dawakai suka bi bayan Sarki Darmanu suka fice daga cikin birnin gaba daya.Nan dai suka nausa cikin daji suka yi ta tafiya ba sassauci har suka shafe sa’a goma sha biyu ba tare da sun hadu da wani mugun abu ba.Duk wata muguwar dabba idan ta hangosu daga nesa sak kaga ta ratsa ta sauya hanya,haka ma mugayen aljanu.Yan fashi kuwa da zarar sun hango Sarki Darmanu tare dasu Lubainu sai kaga sunyi ta kansu saboda sun san cewa Bakin Rijiya ba wajen wasan yaro bane.Adaidai wannan lokaci ne magriba ta riskesu kuma a sannan ne suka shigo farkon dajin da wadannan tsuntsaye na sarki Darmanu suke.Da shigarsu cikin dajin sai Sarki Darmanu ya daga kansa sama yana mai karanta wadansu dalasimai na tsafi.Faruwar hakan keda wuya sai Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka ji wata irin iska mai karfin daga sama ta fara kadawa.Kwatsam sai ga wadansu jibga jibgan tsuntsaye guda uku sun bayyana suna masu saukowa kasa.Duk su ukun a gaban sarki Darmanu suka sauka suna masu dukar da kawunansu alamar cewa sun kwashi gaisuwa.Nan take sarki Darmanu ya shafa kawunan wadannan tsuntsaye yayi magana dasu a cikin yaren tsafi.Faruwar hakan ke da wuya sai tsuntsayen suka bude fukafukansu suka sake tashi sama suka luluka a cikin gajimare har suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba.A sannan ne Sarki Darmanu ya dubi Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara yace,anan zamu yada zango mu dan huta nan da cikar kamar sa’a uku wadannan tsuntsaye zasu dawo su daukemu mu ci gaba da tafiya.Nan take suka kafa tanti suka fidda abincinsu na guzuri suka kama ci suna hira.kafin Yarima Lubainu yayi wani abu da hannunsa tuni Sarauniya Akisatul Sauwara ta miko masa,ya zamana cewa tana kyautata masa,bata son taga ya yi wani abu na wahala da kansa face ta taimaka masa.Bayan sun gama cin abincin ne Akisatul Sauwara ya mike tsaye ta dubesu tace,tana son ta zagaya bayan wata katuwar bishiya dake can gabansu tayi bawali.Tana gama fadin hakan sai ta juya ta nufi inda wannan bishiyar take.Tana isa kuwa ta zagaya bayan bishiyar ta bace musu da gani.A wannan lokaci ne Sarki Darmanu ya dubi Lubainu cikin murmushi yace,na fuskanci cewar Akisatul Sauwara ta kamu da matukar sonka.Koda jin haka sai mamaki ya kama Lubainu ya dubeshi yace,wacce irin magana kake yi haka?Ai wannan bayani naka daidai yake da tatsuniya a cikin kunne na,domin babu yadda za’a yi sarauniya Akisatul Sauwara ta so ni saboda kwararan dalilai guda uku.Dalili na farko shine a rayuwarta bata tabayin soyayya ba don babu wani ‘da namiji daya taba burgeta.Dalili na biyu shine ta san cewa ni ba cikakken namiji bane,kaga kuwa bazata so ta auri wanda baya haihuwa ba tazo ta rasa magaji.Dalili na uku shine ta fini kyau,ta fini mulki,kuma kasan su mata sun fi son su auri wanda yafi su komai.Koda Yarima yazo nan a zancensa sai Sarki Darmanu ya bushe da dariya sannan dubi Lubainu cikin nustuwa yace,Lubainu kai saurayi ne matashi wanda har yanzu yake daukar darasi a cikin karatun duniya,sabanin magidancin mutum kamata wanda yake da matan aure ashirin da hudu.Babu irin soyayyar daban yi ba a rayuwata,dukkanin alamomin SO da KAUNA sun bayyana akan fuskar Sarauniya Akisatul Sauwara a gareka da kuma alamomin kauna a zahiri.Idan ma baka yarda da abinda nake gaya maka ba yanzu nan gaba zaka gani a lokacin da Kura takai bango.Ka bar ganin cewar tasan kana da mata a gida mai jiran ka koma gareta.Hakan ba zai hana taso ka ba saboda shi SO bashi da hijabi kuma babu abinda yake iya tareshi idan har ya yunkuro.Har Lubainu ya bude baki zaice wani abu sai ga Sarauniya Akisatul Sauwara ta dawo,don haka sai yai shiru baice komai ba yana ta nazarin abinda Sarki Darmanu ya gaya masa.Haka dai Akisatul Sauwara tazo ta zauna tare dasu aka ci gaba da hira,inda Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu tace,yanzu kai a ganinka ta yaya zamu jewa boka Darbusa?Shin zamuje masa ne cikin lumana da nasiha ko kuwa zamuje masa ne ta tsiya tsiya? Koda jin wannan tambaya sai Sarki Darmanu yayi murmushi cikin ajiyar zuciya sannan yace,ni ta yaya kuka zo mini keda Lubainu?Sarauniya Akisatul Sauwara tace ai kai baka bari mun iso fadarka ba tun a daji ka taremu kana mai badda kama kazo mana a siffar tsoho don ka yaudaremu ka cutar damu.Dajin haka sai Sarki Darmanu yayi dariya kuma ya hade fuska yace,to kiyi zaton yaudara da tarkon tuggu ninki wanda nayi muku daga Boka Darbusa tunda kin san cewa ya ninka ni sau dari A komai.Koda jin wannan batu sai hankalin Sarauniya Akisatul Sauwara dana Yarima Lubainu ya tashi domin sun fuskanci cewar hadarin dake gabansu na fuskantar Boka Darbusa ba kadan bane.Kodai su sha wahala ko kuma su rasa rayuwarsu gaba daya.Haka dai suka ci gaba da hira har lokaci ya cika sai ga wadannan manyan tsuntsaye guda uku na Sarki Darmanu sun dawo suna masu saukowa kasa daga can kololuwar sama.Cikin gaggawa su ukun suka mike tsaye suka hada nasu i nasu su,kowannensu ya hau kan tsuntsu guda.Sarki Darmanu ne akan gaba,Sarauniya Akisatul Sauwara a tsakiya sannan Yarima Lubainu.Lokaci guda tsuntsayen uku suka bude fuka fukansu suka tashi sama suka luluka izuwa can sama suna masu giftwa ta gaban Rana wacce ke shirin faduwa ta zama ja jawur.Abin gwanin ban sha’awa ga dukkan halittar da take kallo daga kasan Turba.Kamar yadda Sarki Darmanu ya fada haka al’amarin ya kasance wato saida suka shafe kwana hudu da yini daya suna tafiya a sararin samaniya bisa wadannan manyan tsuntsaye sannan suka hango gidan boka Darbusa a nesa kadan dasu.ALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part F Sannan suka hango Gidan Boka Darbusa a nesa kadan dasu.Babban abinda ya baiwa Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara a cikin wannan tafiya shine a tsawon duk kwanakin da akayi ko sau daya tsuntsayen dake dauke dasu basu gajiya ba,kuma ba a sauko kasa an yada zango ba.Haka kuma duk su ukun babu wanda wata bukata ta kamashi ta bawali ko bayan gari saidai kawai idan sun gaji da zama akan tsuntsayen su kwanta suyita sharar barci abinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba.Da yammaci ne sakaliya suka hango wannan gida na Boka Darbusa wanda saidai a kirashi da aljannar duniya saboda ginuwarsa da kawatuwarsa.Tunda Yarima Lubainu yazo duniya ko a bakin masana tarihi bai taba jin labarin gida mai kyan na Boka Darbusa ba.Saidai babban abin takaice shine a tsakiyar dokar daji aka zo aka gina wannan gida wanda aka bata miliyoyin dinare wajen ginashi.Kai da gani kasan cewa in ba rikakken Boka ba wanda ya cika hatsabibin gaske babu wanda zai iya gina irin wannan gida a dokar daji haka ya zauna a cikinsa.Da saukar tsuntsayen uku kusa da kofar gidan da tazarar kamar taku ashirin sai kawai suka ga an bude kofar gidan wacce ta kasance katuwar gaske.Kofar na budewa sai sukaga wadansu kyawawan kuyangi su goma sha biyu sun fito daga cikin gidan a jere a layi.Shida a hannun dama ragowar shidan a hannun hagu.Dukkaninsu suna dauke da wani dan karamin kwando wanda akayi shi da karfen jauhar.Kowanne gwando an cikashi da wani irin jan fure mai tsananin kamshi.Gaba dayan wadannan kuyangin suna sanye ne da dogayen riguna masu launin kore wadanda akayi su da Miski.Babbar cikin kuyangin ce kadai take da riga kala dabam mai ruwan kwai wacce akayi mata dinki mai siffar dawisu.Tsananin kyawun wannan kuyanga gami da kyawun shigar datayi dole ne ya rudi kowanne lafiyayyen ‘da namiji.Cikin tafiyar kasaita da karairaya tamkar macijin gona haka wannan kuyanga da sauran yan uwanta suka iso daf da su sarki Darmanu suka risina sukayi gaisuwa gami da yimusu barkda da zuwa.A sannan ne shugabar kuyangin ta dago kai ta dubi su Lubainu tace lale marhaban da manyan baki na musamma,lallai mai girma Darbusa yana farin ciki da zuwanku kuma yace nayi muku jagora izuwa cikin fadarsa.Koda jin wannan batu sai Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka sauki daha kan wadannan tsuntsayen.Suna sauka sai tsuntsayen suka sake bude fuka fukansu suka tashi sama.Kafin kiftwar ido sun kule a cikin sararin samaniya.Koda ganin haka sai mamaki ya kama Lubainu da Akisatul Sauwara suke a cikin zuciyarsu,Wai shin su wadannan tsuntsaue wane iri nesu?Gashi sunyi tafiyar kwanda hudu da yini daya basu yada zango ba,kuma da saukarsu yanzun nan sun sake tashi sama ko hutawa basuyi ba bare su nemi ruwan sha ko abinci.Anya kuwa wadannan tsuntsaye ba sihirtattu bane?.Amsar da suka kasa baiwa kansu kenan.Ba tare da fargabar komai ba kuwa su Sarki Darmanu suka bi wannan shugabar kuyangin a baya suka nufi cikin gidan.Su kuwa sauran kuyangin tuni suna kan gaba suna zubar da wannan Jan fure mai kamshi a kasa su Lubainu na bi ta kansa.Da shigarsu cikin gidan sai duk su ukun suka kama kalle kalle da waige waige domin sun zama cikakkun yan kauye duk da cewar dukkaninsu sarakai ne masu tarin abin duniya.Ba komai ne yasa suka zama yan kauye ba face ganin kayan kawar da idanunsu basu taba gani ba da abubuwan al’ajibi wanda ko a mafarki da hasashe basu taba zaton wanzuwarsu ba.A cikin wannan gida ne suka ga wani katon Lambu wanda girmansa yafi na wani dan karamin garin kuma kyawawan bishiyoyin dake cikinsa da furanni tamkar halittarsu akayi a ciki ba shukasu akayi ba sai kayi zaton idan kayi musu magana zasu amsa.Barewa,tsuntsaye da kwaron nan mai suna malan buda mana littafi kuwa gasu nan birjik a cikin Lambun kala kala,launi launi bazasu kirgu ba.Kai idan mutum yana kallon wadannan Lambu da abubuwan dake cikinsa sai ya manta da duk wani bakin cikin duniya kuma sai yaji kamar shine sarkin duniyar gaba daya saboda farin ciki.Saida akayi tafiya dasu kusan ta rabin sa’a sannan aka iso dasu fadar Boka Darbusa.Wangamemiyar fada ce wadda girmanta yakai a sanya gidan sarautar Sarauniya Akisatul Sauwara guda uku a ciki.Wannan karon sai da su Lubainu suka rinka yin tuntube suna faduwa kasa saboda kalle kalle da waige waige bisa ganin kayan kawar da yafi wanda suka gani a baya,amma kuma duk wannan kawa sai ta zama ta banza domin kuwa ba karamar razana da firgita sukayi ba sakamakon ganin irin fadawan da suke cikin fadar.Babu bil’adama ko guda daya a cikin dubbun fadawan Boka Darbusa face wadansu irin halittu wadanda mutum bazai iya tantancewa ba yace Aljanu ne ko Dodonni.Wasun su rabin jikinsu na mutum ne rabi na Aljan,wasu rabi dabbobi,rabi dodanni,wasu kuwa rabinsu na Aljan ne da wuta.Sun ksance manya manya,girda girda saidai a kwatanta girmansu da siffofin maridai ko mutanen farko.Dukkaninsu suna da matukar muni,kwarjini da ban tsoro,kuma suna dauke da mugayen makaman yaki iri iri barkatai.Wani kalar makamin ma ko a tarihi mutum bai taba kin irinsa ba.Wadannan dakaru sun cika fadar gaba dayanta sai yar siririyar hanua suka bari a tsakiyar fadar wacce fadinta bai wuce kamu uku ba,kuma itace hanyar dazata kai mutum har izuwa inda karagar mulkin Boka Darbusa take.Koda Boka Darbusa ya kyallara ido yaga kuyanginsa sun shigo cikin fadar tare dasu Sarki Darmanu sai ya mike tsaye daga kan karagar cikin tsananin farin ciki ya bushe da mahaukaciyar dariya yayita dariyar kamar wanda aka bashi komai na duniya.Al’amarin daya kara razana su Yarima Lubainu kenan sukaji a jikinsu cewar lallai Boka Darbusa yaudarsu yayi daya turo aka karbesu hannu biyu,lallai yunkurin cutar dasu zaiyi yanzu.Bayan Boka Darbusa yayi dariyar mugunta har ta ishe shi sai ya murtuke fuskarsa a lokacin da wadannan kyawawan kuyangi goma sha biyu suka rikide suka zama aljanun haske rike da zabga zabgan takubba kuma suka yiwa su Yarima Lubainu kawanya.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu ma suka zare takubbansu suka jingina da bayansu su ukun suna jiran suga ta inda za a kawo musu hari.Koda gani haka sai Boka Darbusa ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi su Yarima Lubainu yace,kunyi hauka kuma kunyi babban kuskure harda kuke yin tunanin cewa zakuzi wajena neman Allon Sihiri na kuma na baku alhalin yau sama da shekara bakwai kenan ina son ku kawo kanku nan fadata kun ki.Ai abinda kuka fada gaskiya ne cewar kowa a gidansa sarki ne.Ina mai tabbatar muku da cewa tunda har kuka shigo nan cikin fadata to tabbas babu dayanku dazai fita daga nan a raye,kuma shi kun shigo dauke da Allunan Sihiri guda biyu.Ku sani cewa tuni nayi bincike na gano hanyar dazan iya cire Allunan Sihirinku daga cikin kwalaben Sihirin da kuka sasu.Ina cirosu zan hada su da nawa.Hakan na faruwa shike na na zama SARKIN DUNIYAr nan gaba daya.Duk wata halitta dake bisa doron kasa walau mutum ko aljan,dabba,tsunstu ko kwaro sai ya dawo karkashin mulkina da ikona.Yanzu zan barku da wadannan Aljanun haske da suka yi muku kawanya na ga iyakar shirin ku dakuke dashi don karbar Allon Sihirina.Koda gama fadin haka sai Boka Darbusa ya yiwa Aljanun izinin su hallaka su Darmanu.Nan take kuwa Aljanun suka afka musu aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa Aljanun suna kai musu sara da suka cikin tsananin zafin nama dabasu taba gani ba.Duk sa’adda takobin Aljanun ta hadu da tasu saidai kaga tarwatsin wuta na tashi kuma takobin Lubainu data Akisatul Sauwara suka rinka dakushewa,ta Sarki Darmanu ce kawai batayi komai ba.Haka kuma duk sa’adda su Lubainu suka sami nasarar sara ko sukar jikin Aljanun saidai suji kamar iska suka soka.Bugu da kari da kyar su Lubainu suke iya tare harin Aljanun saboda karfin saransu,jinsa suke kamar katon dutse ake bugawa a kan takubbansu wanda sai kato arba”in sun tare zasu iya daukarsa.A duk sa’adda takobin Aljanun ta shafi jikinsu Lubainu koda kuwa dan lakatarsu tayi saidai kaji sun kwalla ihi saboda tsananin zafi da zogon da suka ji,a lokacin da jini je tsartuwa gami da feshi daga jikin nasu.Koda Boka Darbusa yaga yana samun wannan gagarumar nasara saiya cigaba da kyalkyalewa da dariyar mugunta saboda ya tabbatar da cewar hakansa ya kusa cimma ruwa.Al’amarin su Yarima Lubainu kuwa suna wannan yaki ne cikin nadama da takaici domin sun gane cewa lallau tsautsayi ne yasa suka biyo Boka Darbusa har gidansa domin karbar Allon Sihiri.Banda Tsautsayi kuma zasu iya cewa Ajali ne ya kirasu,domin sun san cewa babu wata dabara dazasu iya yi a yanzu su ceci rayuwarsu daga hannun wadannan Aljanu na haske. SHIN SU YARIMA LUBAINU ZASU KUBUTA DAGA HANNUN WADANNAN MUGAYEN ALJANU NA BOKA DARBUSA HAR SU KARFI ALLON SIHIRIN HANNUNSA? IDAN HAR HAKAN TA KASANCE YAUSHE NE ZASU ISA KOGON BAHAR IMFAL YARIMA LUBAINU YA SAMO MAGANIN DA YA FITO NEMA? YAYA SOYAYYAR SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DA YARIMA LUBAINU ZATA KASANCE?SHIN ZATA BAYYANA MASA SIRRIN ZUCIYARTA NE KUMA YAYA ZAI KARBI TAYIN NATA? A WANE HALI YAZARINA TAKE YANZU A CAN BIRNIN ZAMRAL BISA BAKIN CIKIN RABUWA DA MASOYINTA YARIMA LUBAINU? INA LABARIN YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA SARKI ALKAS WADANDA SUKA KOMA CAN BIRNINSU A CIKIN BAKIN CIKI NA SABANI? SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIRE SON YAZARINA DAGA CIKIN ZUCIYARSA GABA DAYA A MATSAYINSA NA WANDA YA ZAMO MASAKI MAI HANNU DAYA? WANE MATAKI ZAI DAUKA AKAN MAHAIFINSA SARKI ALKASA WANDA YACE YA CIRESHI DAGA SAHUN ‘YA’YANSA?SHIN YANA TUNANIN DAUKAR FANSA NE AKAN YARIMA LUBAINU KO KUWA YA RUNGUMI KADDARA? YAUSHE NE YARIMA LUBAINU ZAI DAWO BIRNIN ZAMRAL HAR YA SAKE SADUWA DA MASOYIYARSA YAZARINA ‘YAR BABBAN ATTAJIRI NA NAHIYAR? Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI 3(kashi Na Uku) don jin ci gaban wannan kayataccen Kasaitaccen Labari. Post navigation [ad_2]