HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 24

 Halin Girma      24

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

Sai da rana ta daga sosai sannan ta farka, da sauri ta mike tana mamakin dadewar da tayi tana bacci ita da ya kamata ta koma wajen su Mamma. Sakkowa tayi tana jin jikin ta da dama-dama, ta shiga takawa a hankali zuwa toilet din dakin,ta wanko fuskar ta, ta fito ta gyarata sannan ta cire jallabiyar tasa ta maida kayan ta, ta ajiye masa a gefen gadon ta fito zuwa falon. Tunanin yadda zata iya komawa wajen su Mamma take da kuma yadda zatayi da kunyar da take ji daga zuwa ta dawo sai kwana bayan ba haka ya kamata ba a ganinta. Abin takaicin ma bata dauko wayar ta ba balle ta kira, tana tsaye tana tunanin yadda zata fita taji maganganu a kofar part din,wajen window ta isa, ta daga curtains din tana son ganin komai. Gabanta ne ya fadi, tayi saurin cika window din a daidai lokacin da taji suna karasa maganar su. Kyakkyawa ce ajin farko, kana ganin ta kaga bafulatanar adamawa, yau ba kamar jiya da ta soma ganin ta ba, tana cikin shiga me kyau harda Alkyabba, tayi kyau fuskar ta fes alamun tana cikin farin ciki. Kokarin daidaita kanta tayi sanda taji an turo kofar an shigo, idonsu ya hadu lokaci daya, wani banzan kallo Lailan ta watsa mata tana karaso wa ciki a gadarance, ta samu saman daya daga cikin kujerun falon ta hakimce baiwar ta,ta gyara mata k’asan rigar sannan tace ta fita ta basu wuri. Tana fita ta kalli Iman irin kallon sama da k’asa kafin tace

“Barka da rana amaryarmu.”

“Sannu.” Kawai Iman din tace ta juya zata bar wajen amma sai ta dakatar da ita

“Nace ba, ya kika ji da kwanan bakin ciki? A ranar farkon ki a dakin mijinki?”

“Bakin ciki kuma? Na me kenan?” Ta tambaya Kai tsaye kamar bata gane me Lailan take nufi ba

“Na abinda kika gani mana, bakin gani, kinga true color din so called mijinki ko?.”

” Ohh, wannan wasan kwaikwayon wai? Yayi kyau sosai ya kuma tsaru yadda ya kamata, sai dai shi actor din be san kan wasan ba dan be ma san me yake faruwa ba, shine kawai matsalar film din amma yayi kyau.”

“Me kike nufi?” Tace a hasale tana mikewa tsaye

” Abinda kika sani shi nake nufi, kin dauka zan yarda da banzan plan dinki? I’m not an illiterate, I can tell when someone is lying, beside mijina ba zai taba aikata abinda kika ikirarin ya aikata, and i trust him yadda bakya tunani.”

“Wow! Wow!! Wow!!! Sannu da kokari, I love your confidence, amma wanne irin sani kikayi masa haka? Da har zaki bashi irin wannan yardar? Kinsan waye namiji kuwa?”

” It doesn’t matter yaushe na sanshi, all that matters now shine, miji na ne, kuma nayi trusting nashi, dari bisa dari.”

” Shikenan, sai muga yadda zakiyi depending mijin naki at this critical condition, let’s see how far you can go….”

” Kwana hudu kachal kike da, idan har baki samu way out ba. Ki shirya karba ta a matsayin kishiyar ki, sannan na fitar dake ta karfin gaske, dan baki da waje a gidan nan, captain nawa ne right from the start kuma he will always be mine.”

Murmushi Iman tayi mata, tana jin wani irin tsana da haushin Lailan, tana jin zata iya komai, idan tace komai tana nufin komai domin taga ta fitar da shi daga koma menene, akwai babban kalubale a gabanta, amma ba zata karaya ba, duk wanda ya rik’e Allah da addu’a ya gama, da ikon Allah sai tayi galaba akan duk wani makiyin su. Ta daina shiru, duk wanda yace mata kule! Zata ce masa chas! Ita kanta bata san tana da courage din da zata iya maida mata martani ba, sai gashi.

Juyawa tayi ta koma bedroom din dan ba zata cigaba da bata lokaci akan wadda bata tunanin tana da hankali ko kad’an. Wayarta ta gani ajiye a saman chest of drawers ta dauka ta kira Mamma da k’yar, sukayi magana ta ajiye ta zauna tana lissafin rayuwar da zatayi a irin wannan gida, tuna sanda ake mata fad’a irin na bankwana tayi, wata Babar su Abba tana ta jaddada mata hakuri da kuma shirya wa duk wani kalubale na gidan sarauta, karta bari a takata kar kuma ta cuci kowa, akwai makirci sosai wanda zata gamu dashi amma idan ta nutsu tayi hakuri da karfin addu’a Allah zai bud’e mata komai.

   Bata jima a zaune ba taji ana mata knocking, ta tashi ta bud’e ta fito, russunawa tayi har k’asa da sauri ta gaishe ta, kunya ta kama Iman din ganin Matar da zata yi kusan sa’ar Mama tana gaishe ta a haka. Kaya ta mika mata cikin girmamawa tace ta chanja zata rakata bangaren Fulani (Ammi) juyawa tayi ciki, dan dama kayan jikin ta sun dame ta sosai. Sai da ta shirya tsaf  sannan ta fito, ta lura Laila ta jima da barin falon sai dai mayen kamshin da take yana nan a falon. Kai tsaye shashen Ammi suka wuce wanda sai a sannan ne ta sake karewa fadar gani sosai. Anan suka tarar da su Mamma da wasu mutanen wanda da yawan su kana kallo zaka gane alakar su da gidan saboda yanayi na kama da suke da juna. Shigowar su ya saka kowa maida hankali kanta kowa na son ganin amarya, tunda jiya babu wanda ya samu ganin ta saboda dare. Kanta a k’asa taki yarda ta dago saboda yadda take jin kamar ta nutse, a tunanin ta duk sun san daga in da ta taho, bata san Mamma bata fad’a ba sun dai barshi a zuwan sun barota ne tana shiryawa. Sai da duk suka lafa ne aka zazzauna sannan ta gaida Mamma da take kallon ta da murmushi, murmushin da ita kadai ta san ma’anar sa, hakan ya sake saka Iman din cikin jin kunya. 

  Sanda ta shigo Ammi bata falon, tana zaune suna magana da Amaani ta dawo, da sauri Iman din ta zamo daga kujerar ta gaishe ta, ta rik’e ta, ta mik’ar da ita tsaye tana amsawa a sake sosai, sannan ta saka a raka Iman din part din Kilishi.

   Hannun ta cikin na Amaani suka shiga, babu kowa a falon farko sai wata baiwa guda tana goge-goge,wadda ta rako su ce tace su zauna sannan ta nufi kofar ciki don sanar da zuwan su. Jim kad’an ta dawo ta tsaya a gefe, zuwa wani lokaci Kilishin ta fito, fuskar ta kadaran kadahan ba zaka gane komai ba, Iman bata kalle ta ba, ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa a yatsine bata ma zauna ba.

“Hari wannan din itace sirikar tamu?”

“Itace ranki ya dade.”

“Lallai sannu yarinya, shi ko Muhammad ya rasa wa zai dauko mana sai yar karamar yarinya haka? Ko da yake ra’ayin sa ne ai, ba kuma a san ya akayi ba dai, ko da yake dama dai yaran talakawa sai a hankali, idon su idon me arziki sai in da karfin su ya kare, sannu kinji? Allah ya bada zaman lafiya.”

Sai ta juya

” Hari naga amarya, ki gaida uwar dakin naki.” 

Wani abu ne ya tokare wa Iman a makogwaro, idan har ta fahimci maganganun matar tana nufin asiri tayi ta aure shi kenan, a fakaice ta ci mata mutunci babu gaira babu dalili, bayan bata san ta ba, idan banda jiya sai yau ne karo na biyu da ta taba ganin ta. Ajiye ta tayi a daidai mazaunin da da ajiye Laila, ta kuma kuduri aniyar zama dasu daidai da yadda suka zaba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button