An Kai Wadanda Suka Kashe Karuwar Da Ta Ajiye Kur’ani A Dakinta Kotu
Wani mazaunin kasuwar da bai so a ambaci sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya afku ne tun a cikin watan Afrilun da ya gabata.
Ya ce wani mutum ne ya je dakin karuwar bayan ya yi lalata da ita kamar yadda ya saba ya biyata kudinta Naira dubu daya, da ya fita ne sai karuwar mai suna Hannatu Salihu ta duba ba ta ga kudinta Naira 5000 da ta ajiye a dakin ba, nan take ta fita neman mutumin.
“Nan take abokin harkallar nata ya taho tare da abokinsa da kuma karuwar suka shiga dakin nata don su binciki inda kudinta Naira 5,000 suka shiga.
“Suna cikin bincikawa ce sai suka gano ta ajiye Alkur’ani Mai girma a karkashin katifarta wacce ake kwanciya a kai a yi lalata da ita, wannan ne ya sa suka fusata suka kai maganar ga shugabannin kasuwar, amma suka yi watsi da ita.
Hakan ne ya sa suka dauki doka a hannunsu, bayan sun yi mata dukan kawo wuka suka kone gawarta,” inji majiyar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rundunar ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
[ad_2]