BAKAR WASIKA 8

Page -7️⃣
Bayan Baba ya sauke wayar ya kalli Inna cikin yanayin damuwa yace.
“Bashiru ne yake mana maganar komawar mu can”
Inna ta girgiza kai.
“Babu inda zanje, ba a tserewa mutuwa a ko’ina take”
“Na san da haka amman dai ya kamata mu bar garin nan saboda ance akwai yiyuwar su dawo, kuma kina gani kullum mutane barin garin nan suke”
“Babu inda zanje Malam, na fi son mutuwata ta same ni a inda nake”
“Ai kaji matsalarki kenan, shi kansa abun da yake ta magana kenan a lallaba masa ke”
Inna bata sake cewa komai ba, har Baba ya ci ya shude. Duk abun da suke Aminatu na dama furar tana saurarensu, bayan ta gama ta kawo ma Inna ta zauna kusa da ita ta fara bata a hankali tana sha, Inna bata hana Aminatu shayar da ita ba, duk kuwa da kasancewar zata iya sha da kanta. Sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta rufe furar ta koma gurin girkin da take. Har ta girka ta gama bata cikin walwala da sakewar zuciya, ba na rashin yan’uwa ba, na tunanin kalaman da Inna tai mata? Ta ya zata rayu babu Inna? A hannu waye zata zauna ma? Ba ita kadai ba Baba ma ya zai ji idan suka wayi gari babu Inna? Ko da ace tana da aure rayuwa ba zata taba mata dadi babu uwa ba, balle kuma a yanzu da take tare da ita, Saurayinta Maniru ma yana cikin mutanen da yan bindigar suka kashe, bayan ta gama ta zubawa Baba nasa ta zubawa Isah a inda ake saka masa sannan ta kwashe sauran a Samira babba, ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta cire komai na jikinta sannan ta zauna saman dutsen da suke zama idan zasu yi wanka ta fashe da kuka.
Kuka tai sosai sannan tai wanka ta fito idonta a kumbure, ta dora alwala ta shiga dakinsu tai sallah, bayan ta gama ta d hannayenta sama tana rokon Allah.
“Ba ni da gata sai naka Allah, ka dauke yan’uwana a lokacin da ka so, ka sauya rayuwata zuwa yadda ka kaddara min, Allah ka yafe min ka jikan yan’uwana, ka ba mahaifiyata lafiya ka bar ni da ita Allah”
Ta karasa hawaye na sauko mata, sannan ta shafa addu’ar ta mike tsaye, ta fito waje, sai da ta zuba ma Inna ruwa a buta sannan ta rika ta, ta kaita bandaki bayan ta fito ta taimaka mata tai alwala sannan ta shimfida mata abun sallah.
“Allah ya miki albarka Auta”
Inna ta fada tana kokarin gyara zamanta, domin a zaune take sallah a yanzu. Aminatu ta kalleta kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta amsa.
“Ameen”
Ta mike tsaye.
“Bari naje na yi itace yamma ta yi”
Kai kawai Inna ta daga mata, ita kuma ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka ta ta dauki zaren da take daure itacen idan ta yi, sannan ta saka talkaminta ta fice, ba ita kadai ba kusan duk yan matan garin da ma matan aure suna zuwa daji ne su yi kara da yamma saboda dafa abinci, abu ne mai wahala ka ga gidan da ake siyen itace a yanki, yawanci duk a daji suke yin kara.
A da ta saba idan zata tafi yin kara akan biyo mata ko kuma ita ta biyawa wasu, sai dai tun bayan da aka tarwatsa rabin garin take tafiya ita kadai, saboda an tafi da wasu yan mata, wasu kuma sun yi gudun hijira, sauran da suka rage kadan ne. A gurin da ta saba tsayawa ta tsaya ta shimfida zanen sannan ta aje zaren a gefe, kana ta shiga tsintar karan, tana yi tana tuna yadda suke yi a da, ita da kawayenta, har tigengen suke cikin nishadi da walwala, sabanin yanzu da suka bar ta da kewa.
Sai da tai rabin sannan ta samu kanta da mugun faduwar gaba, marar misaltuwa, a take ta nade wanda ta tara a daure ta dauka ta nufo gida da gudunta, kowa sai kallonta yake, kamin ta iso har hawaye ya fara sauko mata, bakin kofa ta jefar da karan ta rugo da gudun gurin Inna da ke kwance tana bachi ta taba ta.
“Inna…Inna…. Inn”
Bata karasa ba, Inna ta bude idonta da sauri tana kallonta.
“Lafiya Auta?”
Sai ta fashe da kuka, wanda hakan yasa Inna ta tashi zaune.
“Tsoro nake ji Inna, gabana faduwa yake”
“Tsoron me? Miya faru?”
“Ban san ni ba, bana son na yi nisa da ke”
“Auta kenan, kin isa ki tare min mutuwa ne? Da wani na tarewa wani mutuwa ai da na tarewa Yayana, kin san babu uwar da za a kashewa yaya a gabanta kuma ta kyale alhalin tana da ikon yin wani abu?”
Maganar da Inna tai ya isa ya tabbatar da cewar ta fi jin bakincikin kashe mata yaya da akai fiye da keta mata haddi da aka yi. Aminatu ta yi kasa da kanta tana kuka sosai.
“Kina kuka da wuri, ki adana kukanki saboda gaba”
Ta kalleta.
“Miyasa kike min fatan kuka Inna?”
“Saboda zaki yi kuka mai yawa Aminatu, dole zaki yi kuka, ranar da zaki bude ido babu ni, ranar da zaki ga wata uwar idan kika tuna da taki dole ki yi kuka, ranar da kika ga wasu yan’uwa kika tuna da naki dole ki yi kuka, ranar da kika nemi wani abu kika rasa dole ki yi kuka, ni na riga na gama tawa rayuwar har na yi jikoki kuma na yi Auta, ke kuma yanzu rayuwarki take kan ginuwa, ta fara miki a haka, me kika tsammani a gaba? Dadi? Dadin yana tafe bayan wuya amman, yanzu na fi tausayin rayuwarki fiye da ta kowa Aminatu”
Ta share hawayenta, ta kara matsawa kusa da Inna ta kwanta jikinta, ta lumshe ido, tana maida numfashi a hankali.
“Allah ga yata, Allah ka zame mata gata”
Inna ta fada a ranta hawaye na sauko mata, ba tana kalamai ba ne domin ta daga mata hankali, a a har ga Allah tana fadin abun da take jin ya kusa tabbatuwa a gareta ne, kuma tana jin nata mai kiran ya kusa kiranta, jikinta da mafarkanta suna bata haka, domin tana jin wani kalar yanayi na dabam a jikinta wanda bata taba jin irinsa ba, sai dai a kusa? Ko a nesa? Yau ko anjima? Shi ne abun da bata da tabbaci.
Bayan sallah Magariba, Baba da Isah suna daki sun saka Inna a gaba suna ta kokarin convinced din Inna akan ta amince da magabar Bashiru su ma su yi hijira su bar garin amman ta ki, Aminatu kam tana zaune waje sai kallon hadarin dake haduwa take, ita kanta bata san na yi ba, tafiyar ko zaman? Inna tana da gaskiya idan sun tafi ba za su tserewa mutuwa ba, sai dai barin garin zai taimaka Inna ta manta wata damuwar, domin a cikin abubuwan da suke bata mata rai har da zaman gidan da take ganin an kashe yayanta kuma tana ganin a kowa ne dare kamar za su shigo ne su yi mata sallama kamar yadda suka saba, yadda rayuwa take a baya.
Sai da akai kiran sallah isha’i sannan Baba da Isah suka fito waje, sukai alwala suka yi haramar zuwa masallacin.
TALBA POV.
Ya kusan minti ashirin a cikin motar sannan ta fito, kamin ta bude motar ta shiga ma wani aiki ne, ba karamin kufula shi tai ba, domin ya tsani jira ya tsani a bata matsa lokaci.
Sai dai ko kadan be nuna mata ransa ya bace ba, ya ja motar suka fita fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Mai gadin be yarda ya tsaya jiran sai Talba ya danna horn sannan ya bude masa ba, tun a lokacin da ya ga ya shiga motar yai hanzari bude gate din ya tsaya, be bar gurin ba har sai da motar Talba ta fice daga gidan.
Be kalli inda take ba, tukinsa kawai yake yana sauraren fm din dake gabatar da wani program, sai dai ita lokaci zuwa lokaci tana satar kallonsa, duk kuwa da kasancewar bata son su hada ido gudun kar ya ga tana kallonsa.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin titi, ya zata yi ta canja Talba? Shine tambayar da ta zo mata a rai, gata a mota daya da shi amman baya nuna mata wata alamar kauna, Baya ma son kallon inda take kamar ba masoyinta ba.