AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

_Dukkan yabo da godiya ya tabbata ga Allah S.W.A wanda ya kagi sammai da kassai yakuma sanya soyayya shugabanmu annabi Muhammad S.A.W acikin xukatammu wanda yabani ikon fara rubuta wannan littafi ya Allah kabani ikon rubuta abinda al’ummu xasuyi farin ciki dani????????_

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis aisha????*

 

 

*Page 1*

 

”Kwance take kan makeken gadon dake cikin dakin tayi kur tana kallon fankar dake manne a saman dakin tana juyawa, hawaye ne kebin kuncinta amma kotakansu batabi ba dasunan gogewa, tashi tsaye tayi tafata xagaye dakin tana nemawa kanta mafuta akan matsalar dake tunkarota, momcy ce tashigo dakin sallamarta uku amma kwata kwata diyar tata bataki ko daya daga ciki ba, hakan ne yasa tamatsa kusa da ita ta dafa kafadarta hadi da kiran sunanta a hankali.

Khairat make damunki haka harna shigo dakinki ina sallama baliji ba kina tunani gashi kuma kuka naga kukama kike?

Fadawa tayi jikin mahaifiyar tata tana wani marayan kuku hakan ne yasa momcy tariko hannunta suka xauna bakin gadon tafara goge mata hawayen tana rarrashinta Sannan tace toh fadamin meke damunki kiji diyata idan baki fafaminba waxaki fadawa?

Shuru khairat tayi tana tunanin anya nafadawa hajiya cewar sadeeq auran wata daya yakeso muyi kuwa anya baridai kawai naboye mata wannan domin nasan ruwa na ballowa kaina gashi Allah yajarb ceni dason sadeeq gwara naxauna dashi kona 1 month din……..

Muryar momcy ce ta katseta ” khairat kenake wa maganafa amma kinyi shuru wai meke faruwa ne?

Cikin kuka tasoma magana ” mom wai meyasa yaya sadeeq baya kaunata ko kadan baya Tausaya min duk da na kasance yar uwa agareshi tun ina daukin auransa harna fara yanke shawarar fasawa mom wlh nafara gajiya takuma fashewa da wani Sabon kukan.
Kwantar da hankalinki kinji khairat komai me wacewane bb yanda muka iya tunda kinasonsa addu’a xakici gaba dayi kina mika kukanki ga ubangiji sannu a hankali xakiga komai na xuwa miki da sauki, ki daina damuwa munan dake sai sadeeq yayimiki soyayyar daxaiji kamar ya hadiyeki insha Allah kidage da addu’a kawai itace makarin mumini.

Kallon mom kawai tayi tace anya kuwa mom yaya sadeeq xai soni?

Haba khairat wace tambaya ce wannan yanxu ke ba Allah ne ya sanya mi soyayyar saba ko ra’ayin kankine haka?

A’a momcy da ra’ayina ne ai datini nadade dacireshi araina.

Murmushi mom tayi ta dafa kafadarta tace ” ki kwantar da hamkalinki ki abinda nace kici gaba da shirye shiryenku kinga yanxu saura kwana 10 amma akwanakinnan kidage da addu’a kinji nasanki akwai kokari ta nan bangaran.

Toh mom ngd

Nan ta dada kwantar mata da hankali Sannan tatashi ta xata tafi.

Har takai bakin kofa ta juyo tace au kinga harkin mantar dani abinda yakawo ni, dama sako xaki karbomin wajan hajiya rabi munyi waya da ita nace yanxu xakixo.

Toh momcy barina shiga toilet na gyara fuskaya saina tafi

Owk inkin dawo ina sama sbd bacci xanyi jiya bansamu bacci sosaiba ta fada lokacin datake rufe mata kofar.

Tashi khairat tayi tashige toilet din…..

 

 

 

 

 

Neenat saif????????
[12/18, 7:26 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*
????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 2*

 

 

Tana dawowa daga gidan hajiya rabi kai tsaye tawuce gidan babbar aminiyar tata marya

Tun ahanya ta kirata awaya tasanar mata tana hanyar gidansu.

Tana isa gidan tayi parking ta fito daga motar dan ko direba dama bataxo dashiba.

A parlour ta iske hajiya sakina mahaifiyar maryam tana kallo tayi sallama hajiya ta amsa cikin sakin fusaka tana cewa amarya amarya anji mutuniyar shuru aka biyo ta kenan?

Dari tayi tana cewa eh wlh hajiya ina wuni

Lpy lau ta amsa mata suka dan gaisa tace maryam din ai tana ciki.

Mikewa tayi ta nufi dakin maryam tana isa ta isketa xaune abakin gado tana game a waya.

Tanajin shigowar khairat ta dago tana fadin amarsu, harara ta watsa mata tana fadin duba tym kigani karfe 2:00 yanxu amma kokixo gida kinsan kuma ina nemanki

Yi hkr sis yau kai nane natashi yanamin ciwo

Owk Allah yabaki lpy ta fada tana xama akusa da ita

Ameen sis

Shuru khairat tayi tana duba yatsun kafarta amma tskasa magana idanu maryam tabita dashi tana karantar yanayinta domin tasan cewar tabbas akwai matsala.

Ajje wayar hannunta tayi tajuyo ta fuskanci khairat ta kama Hanna yenta ta rike cikin nata Sannan tafara magana.

Besty yanayinki ne kawai yasar min akwai matsala banason ganinki cikin damuwa ki taimaka ki fadamin abinda yafaru banason kifara wannan kukan dan nasan matsalar baxa wuce ta yaya sadeeq ba.

Hawaye ne suka fara bin kuncinta shiiiiiiii maryam ta fada hajiya tana parlour banaso taji mu tunda naganki a haka nasan ko momcy baki fadawa ba don haka fadamin kawai musan abinyi amma kitsaida kukan kar hajiya tajimu.

Share hawayen khairat tayi takalli maryam tace ” maryam sadeeq baya sona dagaske fah da na dauki abin na dan lokaci ne amma yanxu na fuskanci kawai yanamin hakuri amatsayina na yar uwar sane amma yanxu dayaga maganar auren mu da gsk ne bb fashi hankalinsa duk yatashi tsantsar kiyaya kawai nake gani yanxu a tattre dashi.

Nasan da haka maryam ta fada yanxu ni sonake naji yaya kukayi dashi?

Hawaye tafara Sannan tace jiya da daddare sadeeq yaxo amma abinda yaxomin da shine yahanani kwanciyar hankali nayi niyyar fadawa momcy amma kuma saina tuna kafin yatafi ya fadamin cewar idan har ikirarin ina sonshi da nakeyi har cikin xuciyata ne toh karna sake iyayenmu suji wannan magana domin bayaso iyayansa suyi fushi dashi, kuma tabbasa indai harna bari suka sani kuma yaga wani sauyi a tartare dasu xai dauki alhakin komai ya dora akaina nice silar rabashi da farin ciki sa kuma dama ba kaunar sa nakeba………..

Kukane yaci jarfinta maganar ta tsaya anan tanajin wani irin xafi a xuciyarta.

Rarrashinta maryam tayi Sannan tace wace maganace wannan ya fada miki?

Saida ta tsaida kukanta tajuyo ta kalli maryam Sannan tace

”Yaya sadeeq yace auran wata daya xuyi tsakanina dashi.

Wata daya kuma maryam tafada tane xare ido????

Yanda na fada miki haka ya fadamin khairat ta fada tana kallon maryam da mamaki ya gama kasheta a xaune.

Dakyar ta tattaro nutsuwarta ta kalli khairat tace yanxu dai kina nufin xa’ayi auranku amma kuma bayan wata daya xai sakeki?

Eh haka yace sbd wai baya sona kuma idan yaki auena iyayenmu xasuyi fushi dashi akan yaki musu biyayya amma inya aureni yasan abinda xaiyi wanda xai rabu dani cikin wata daya batare da ansamu matsala ba.

Shuru maryam tayi Sannan daga baya ta dago ta kalli khairat tace wannan ba matsala bace kawai mu dora inda aka tsaya muci gaba da shirye shiryenmu kawai????????‍♀

Kamar yaya so kike yi nayi aure nan da wata daya nafito marayam?

Dariya maryam ta sheke da ita, kallon mamaki khairat tabi maryam dashi harda bude baki.

Saida ta gama dry ta Sannan ta kalli khairat tace karki damu xanyi miki bayani kuma xaki gane me nake nufi amma ba yanxuba kawai sonake ke kwantar da hankalinki ayi abinnan cikin kwanciyar hankali daga ranar saga ranar da aka daura muku aure xa’a fara wasan.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button