AURAN WATA DAYA

*AURAN WATA DAYA*
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat saif????????????????????????????????*
*Dedicated my lovely fans???? ina matukar godiya da irin kaunar da kuke nunamin inajin dadin addu’arku gareni, makiya kuma ina mugu mugun yinku irin totally dinnan???? ina dada mika godiyata a gareku baki daya masoya da makiya????????*
*Page 16*
Bin bayanta kawai sadeeq yayi a xuciyarsa yana fadin bariya tafi xakiga abinda xan miki dama iskancine ya sanyaki fitowa a hk kuma kinyi kinji dadi xamu gauraya ne letter.
Abdul ne ya tabashi yace Malam ta dade da tafiya fa naga kabi hanyar databi tun daxu kana kallo, idan ancen kana sonta kacewa mutane karya ne bayan…
Kaga malam dakata haka abar maganar haka ka manta da maganar dakayi ne?
Ban manta ba kuma shawarace nace baxan sake baka ita akan khairat ba kuma abinda na fada maka dole ya faru wlh wlh wlh kaji rantsu guda 3 danayi maka bb babu kagfara acikinta nan da wasu kwanaki xaka gane gskyr danake fada maka kuma saikayi dakasani.
Toh Malam naji Allah ya kara basira irin wannan fasahar xance da hangen nesa gsky kayi kokari.
Uhm sadeeq kasan….
Cikin xafin rai sadeeq ya daga masa hannu ya isa haka nace ngd???????? da shawarar ka arufe maganar haka.
Kallonsa kawai Abdul yake axuciyarsa yace yaro bakasan wutaba sannan yace
Toh shikenan dama tafiya xanyi ni.
Toh Allah y kiyaye hanya ka gaida min hajjiya najima banshiga gidan ba.
Shikenan xataji ya wuce yayi tafitarsa ko bakin mota sadeeq bai rakashiba.
Tunda ta hau saman kai tsaye dakinta ta shige ta fada gado tana sakin wani irin kuka mai tsuma xuciya tana danasanin sauka kasan datayi harta jiyowa kanta bakar Kalmar da harta koma ga mahaliccinta baxata taba manta taba, bana sonta kuma kafi kowa sanin bana sonta kalaman sadeeq keta mai maita kansu a cikin kunnanta da sauri ta toshe kunnenta tana karanto Addi’oi domin jitake kamar xuciyarta xata fashe’a fili ta furta yaya sadeeq bansan cewar tsanar dakakemin harta kai hakaba insha Allah daga yau ko ganinama kadainayi ko fita parlour indai kana gidannan baxan sake kuskuran yin hakaba har xuwa lokacin daka diba min yacika domin nasan wata rana ido da ido xaka kalleni ka furta baka sona…..
Wayarta taji tana kara kamar baxata daukaba sbd kar wani ya fahimci kuka tayi, harta katse aka sake kira shima harya kusa katsewa sai tayi tunanin ya kamata taga wayake kiranta, mika hannu tayi saman gadon data ajje wayar tana dubawa taga mom din sadeeq ce sauri tayi ta sai saita kanta ta amsa wayar hadida sallama mom ta amsa suka gaisa sannan mom tace
Khairat yanaji muyarki haka meke faruwa?
Sauri tayi tayi murmushi tana fadin mom mura nakeyi yau kwana biyu kenan tama dan ragu sbd inashan magani.
Ayya toh Allah yabaki lpy har yanxu khairat baxaki daina shan kayan ssnyi ba kenan?
A’a mom aina rage
Toh Allah yasa da gsk kike.
Ameen mom ina aisha ne?
Wlh tunda ta tafi school bata dawoba ina tunanin sai magriba sbd da rana ta tafi.
Owk ina dady fah?
Yanxu kikasan da dady din kenan uhm khairat nima tunda akasa ranar ku da sadeeq kika daina xuwa gadan iyayan naki koda aka kaiki baki kirani ba sai yanxu dana kiraki.
Rufe fuskarta tayi da hannu tace wlh mom ni kunyarku nakeji keda dady.
Salati mom tayi tace kaniyarki khairat mu kikejin kunya ai mu iyayanki ne ba surukaiba don haka ki daina kinji
Toh mom
Nan dai taware sukasha fira rabi nasihace mom tayi mata sbd tasan halin dan nata sannan tace daxar kinga yayi mimi wani abun bacin rai ki fadamin sbd nasan halin sadeeq
Toh kawai tace sukayi sallama ta kashe wayar.
Tagumi takumayi hawaye nabin fuskarka addu’a taci gaba dayi jin yanda xuciyarta har yanxu take mata wani mugun xafi ya ilahi kabani hakuri da juriyar da xan cinye wannan jarabawar taka ya Allah kaga xuciyata bani na tursasa iyayan mu suka hada wannan aureba r’ayinsu ne a haka ya Allah ka yayemin soyayyar wannan bawa naka acikin xuciyarta ya Allah……
Wani Sabon kukan ne yaci karfinta ita yanxu tausayin kanta takeyi tana cikin damuwa amma babu Wanda xai jata jikinsa ya rarrasheta ya ilahi wannan wace irin rayuwa ce, haka ta xauna tanata Abu daya har magriba tayi tashi tayi taje tayi alwala taxo tayi sallah ta dade tanata addu’oi har akayi issha’i bata tashi daga wajan ba tanayin sallah ta tashi yau ko wanka batayi ba bare kuma ta sauya kayan bacci kawai ta kwanta.
Tunda Abdul ya tafi sadeeq keta jiran sauko warta shi adole saiya koya mata hankali akan fitowar datayi da wannan kayan harda xuwa gaban Abdul din yadda xaifi kare mata kallo, jinta dayayi shiru ne yasa ya tuna tace xata hada masa ruwan wanka tashi yayi yanufi dakinsa kai tsaye toilet yanufa ya bude yaganshi Bb ruwanda ta hada amma kuma bayin sai kamshi yake gyaran datayi daxu, lumshe idonsa yayi shi dai yana matukar son kamshi arayuwarsa,shiga yayi ya hada ruwan wankan yayi wankansa yana fitowa yaji ana kiraye kirayen sallah komawa yayi yayi alwala sannan yafito yayi sallah, shiryawa yayi ya dauki key din motarsa ya fice daga gidan.
Sai wajan karfe 9:00 ya dawo gidan ya rufe ko ina duba parlour yayi yaga alamar tun tafiyarsa khairat bata sakko ba kenan hakan yana nufin ko abinci bataci ciba, a fili ya furta wannan yarinyar yar matsalace wlh salon wani abin yasameta tajamin salalan tsaya dama daxu mom takirani tanata fada ko maita gaya mata oho????????
Kai tsaye ya wuce dakinsa ya sanya kayan bacci ya kwanta lumshe idonsa yayi sbd wani sihirtaccen kamshi dayaji yana tashi a gadon sai a lokacin ya kula har xanin gadon da rigar filo ta sauya kuma su suketa xuba wannan kamshin, jinsa yayi kawai xuciyarsa tai wasai rufe idanunsa yayi hangota yayi adaxu data sanya wani lallausan kyalle mai kamshi tana share masa fuska tana wani fari hadi da hura masa iska a face dinsa, jin wani shock yayi ajikinsa kamar a lokacin hakan ta faru jiyayi gaba daya yanayinsa ya sauya, juyi yayi hadi da tsaki ya rufe idanunsa yana fadin aikin kawai da ace macen danakeso na aura da yanxu haka bata faru daniba(ni dai kallonsa kawai nayi domin khairat CE macen dayakeso amma yakasa ganewa????)
Washe gari yana tashi yayi shirin tafiya office yana fitowa ya duba yaga khairat bata fitoba xama yayi a parlourn sama har wajan karfe 8:00 amma baiji motsintaba gajiya yayi ya tashi yayi tafiyarsa.
Yau gaba daya tashi tayi batajin dadi gashi da daddre bata samu bacciba sai tashi kawai tayi ta jero nafilfili har xuwa asuba sannan tasamu bacci.
Da kyar tashiga bayi tayi wanka ta kintsa kanta cikin wata doguwar riga mara nauyi irin roba dinnan, da kwanciya xata koma tayi sbd kwata kwata batajin cin abincin tunawa tayi da baba mai gadi ta mike tashiga kitchen ta hada mai tea da soyayyar indomie da kawai ta xuba mai ta mika mai sannan ta dawo ta koma dakinta ta kwanta.
Wajan karfe 3:00 yabar office kai tsaye gidan su ya wuce, mom naganinsa ta watsa masa harara murmushi yayi yana Sosa kyeya ya gaisheta.
Ko kallonsa batayiba ta amsa aisha dake gefe ta gaisheshi ya amsa sannan ta tashi tabar musu parlourn dan taga alamar yau lefi yaayan nata yayiwa mom.
Xuwa yayi kusada mom ya xauna yace mom wai menayi naga kinata fushi dani? tun jiya da dakika kirani naji kinata fada nasan nayi laifi.