AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Jiyowa tayi tadan saki fuska tace sadeeq jiya nakira khairat muryar ta kawai naji nasan da akwai matsala na tambayeta tace batada lpy, amma banyyarda ba nabiye matane kawai, sadeeq inaso kasan cewar khairat amana ce awajamka kuma kobabu komai kasan yar uwar kace batada ban banci da Aisha awajanka karka manta hakan kuma inka cuceta sai Allah ya saka mata karkaga Bb Wanda yake kallonku kasan Allah naganin duk wani Abu daxaka aikata afili ko a boye inaso ka rike wannan aranka.

Jiyayi jikinsa yayi sanyi yace shikenan hajiya karki damu insha Allah xanyi kokari naga na sauke duk wani hakki nata da yake kaina.

Toh Allah ya taimaka mom tace sannan tada yimasa nasiha sannan ya tafi, a hanya ya tsaya yayi takeaway sannan ya nufi gida.

*Neenat saif ????????*
[12/18, 7:30 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 17*

 

 

Yana isa gida kai tsaye dakinsa ya wuce yayi wanka sannan ya fito yaci abinci yayi xamansa a parlour, harya gama xamansa baiga khairat ba abin yabashi mamaki amma kuma saiya basar,har akayi magrib akayi ishsha amma baiji motsinta ba haka ya karaci xamansa ya koma daki ya kwanta.

 

Saida sukayi 2 days a haka kwata kwata sadeeq ya daina ganin khairat haka kawai sai yake jin Bb dadi a xuciyarsa musamman inya tuna nasihar da mom tayi masa akan amanar khairat sau tari yakanyi kokari ya nufi dakinta da niyyar ya shiga amma kuma saiya kasa duk abun duniya ya isheshi ya rasa yadda xaiyi kobabu komai yanxu hakkin khairat ya ratayene a wuyansa shiyasa abin yake damunsa.

 

Ta bangaran khairat kuwa duk abin duniya ya isheta ko abinci bata iyaci, kwanan ta 2 bb lpy amma ko sau daya batasha maganiba,wayar tama gaba daya ta kashe ta takan kunnata ne idan xata kira Momcy da dady ko kumaa mom dinsu sadeeq domin yanxu tana kiranta har su gaisa da alhjin su sadeeq, ko maryam bata kira a waya ita kawai tana jiran kwanakinta su cika ne sadeeq ya kawo mata takardar ta wuce ta koma gida, ko parlour bata fitowa sitaji yunwa ta isheta ne take xuwa ta dauko hollandia ta dansha baba mai gadi kuwa ta sanar mai yaringa siyan abinci batajin dadi ne kwana 2.

 

Yau kwanan khairat uku rabonta da ganin Sadeeq shima haka domin ta haram tawa kanta ganinsa.

Kwance take a daki ta idar da sallah ko tashi batayi ba daga wajan datayi sallar, sallama taji anayi a parlourn kasa shuru tayi jin kamar muryar maryam takeji, kin amsawa tayi domin tafi bukatar maryam ta taho har saman.

Maryam dataji ba’a amsa sallamar tataba ne yasanya ta fara hawa steps din tana isa kofar dakin maryam ta tura kofar hadi da sallama tsayawa tayi cak tana kallon khairat wacce ta juyo tana yimata murmushi.

Bakida lpy ne khairat????

Maryam ta fada tana karasawa kusa da khairat, khairat bata bata amsa ba sai mikewa datayi ta cire hijjab dinta ta ninke shi ta ajje sannan ta juyo wajan maryam.

Kallonta kawai maryam keyi ganin yadda duk ta rame amma kuma tayi fari fat kamar Bb jini a jikinta duk ta dashe.

 

Khairat ce ta dubeta tace lpy kike maryam naga duk kin wani xuba min idanu kamar yau kika fara ganina???

Mikewa maryam tayi ta kama hannun khairat suka xauna bakin gado sannan ta dubi khairat tace baki bani amsa taba na tambayeki rashin lpy kikayi ne???? Naganki kin wani rame sai wani fari da kikayi?

Murmushi khairat tayi tace uhm kwana na 3 banida lpy yaune na tashi jikin da dan sauki.

Kar kiyimin karya khairat kinsani bb wani abu da xaki iya boyemin nasan akwai abunda yake faruwa, karki manta tun kafin kiyi aure ban sanki da kina kashe waya ba amma kuma abin mamaki sai gashi yanxu dakikayi aure wai ana kiran wayarki ba’a samu, haba khairat kwana na 3 ina kiran wayarki amma kuma koda yaushe a kashe daxuma saida na kira amma ban samu ba gashi kema kin daina kirana shiyasa na shirya na taho domin nasan a kawai matsala.

 

Hawaye khairat ta fara yi maryam ta daga mata hannu tace no khairat karmuyi haka dake.

 

Goge hawayan khairat tayi tabawa maryam lbrn abun daya faru, shuru maryam tayi tana jin tausayin kawar tata kallonta tayi ta saki wani murmushi sannan tace ai ina ganin wannan ba matsala bace,

Wani kallo khairat tabita dashi amma takasa magana dariya maryam tayi tace khairat ki nutsu muyi magana dake ida banyi batan lissafi ba yau kwana 10 da auranku da sadeeq kenan???

Gyada mata kai kawai khairat tayi murmushi maryam takumayi sannan tace karki damu da kalam da sadeeq yayi sbd ai bake yake fadwa ba kuma sannan baima san kina wajan ba,kuma karki manta bai taba furta miki baya sonkiba a lokacin dayake gaki gashi ba don haka karki damu amma xamu sake shiri yan xunnan a wannan karon saimun danawa sadeeq tarko cikin kwana ki kalilin.

Kwafa khairat tayi tace nifa na hakura da sadeeq kawai ki kyaleshi

 

Dariya maryam tayi tace naji ai nima bance auranku xa’a gyara ba kawai inasone shima sadeeq ya wahala akan soyyarki kamar yadda kema kikasha wahalarsa dubi yadda kika koma fa ta fada tana nuna ta.

Kallon kanta tayi sannan tace shi yace miki yana sona toh da har xai samu Matsala a kaina????

 

Kallonta maryam tayi tace ko daya amma jiya munyi waya da waya da Abdul kinsan tun da akayi bikinku wasu lokutan yakan kirana.

Kodai ya kyasa ne khairat ta fada tana xolayar maryam

 

Murmushi maryam tayi tace nima alamun danake gani kenan amma kuma bai furta ba….uhm kings mu ajje wannan maganar xuwa wani lokacin yanxu ta sadeeq muke ina fada miki jiya da mukayi Waya da Abdul yake bani labarin sadeeq ayanda na fahimta sadeeq yana sonki amma nakasa gane meyasa yake karyata hakan, na tambayi Abdul yace min shima bai saniba, amma yanxu mu xamusashi ya yarda da hakan.

 

Kwafa khairat tayi tace uhm kawai dai xan biye mikine amma badan na yarda da wannan magana ba.

Naji karki yarda yanxu ya kamata mufara shirye shiryen mu

Kallonta khairat tayi tace kamar ya????

 

Itama binta tayi da idanu batare da ta bata amsaba, idanunta ta saike kan khairat tace bani kayan kitso nayi miki kitso yanxun nan.

Mikewa khairat tayi ta kwaso kayan kitson takawowa maryam nan suka fara amma ba kanana ba, kitso tayi mata irin Wanda akeyin na baya sannan ayi wani a tsakiya kamar shiku,

Suna kammalawa maryam tace mu huce kitchen kinsan yau har gogan naki xa’ayiwa girki.

Bude baki khairat tayi tace kin manta kashe din dayayimin ne?

Uhm tunawa da hakanne yasanya xamuyi dashi

Kai tsaye suka wuce kitchen suka fara shirya lafiyayyen abinci har kala 2 saida suka kusa kammalawa ne khairat ta fito tabar maryam ta karasa ita kuma ta fara gyara gidan tundaga dakin sadeeq xuwa parlourn sama dana kasa duka saida ta gyara ko ina kamshi ne kawai yake tashi a gidan.

maryam na kammalawa tajuye kamai a flask ta rufe ta fito tsayawa tayi tana kallon khairat tace gsky mutuniyar kin iya gyara

Dry khairat tayi tace muje muyi sallah karfe 5:00 ya salam maryam ta furta, suka wuce dakin khairat.

Suna idar da sallah maryam tace tashi ki shiga wanka ki barina xuba abinci naci sannan na tafi sbd banaso sadeeq yaxo ya sameni nafiso yayi tunanin ke kadai kikayi komai ba hada baki mukayiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button