AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Owk kawai tace ta mike ta nufi toilet, tana kammalawa ta fito ta iske maryam harta gama cin abincin tana shirrin kai kayan kitchen xama tayi tayi light makeup maryam ce ta dauko mata wata red din doguwar Riga ta sanya ta daura farin dan kwali ta juyo ta kallo maryam tayi mata farrr da idanu.

 

Maryam tace gsky kinyi kyau murmushi tayi tace na gd ta juya ta sanya turare ,maryam ce tace kinga muje kirakani karya dawo,har wajan motarta ta rakata sannan ta dawo ta xauna tana jiran dawowar sadeeq….

 

 

 

 

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:30 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written neenat saif ????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my mom she is only one i have she can do anything for me just to make me happy she care for me I love u so much mom????and i will always froud of u ????????????*

 

_Masoya na ina yawan ganin korafin ku akan cewar banayin typing da yawa, ya kamata kusan cewa mu marubuta muna kokari sosai akan ganin mun faranta muku kuma munajin dadin yabawarku garemu, game da typing da yawa kuma gsky ayyuka sunayimin yawa ne amma duk da haka ina kokarin ganin na yimuku typing kullum batare da nayi fashi ba, amma duk da haka xanyi kokari naga na kara yawan typing din domin ganin farin cikin ku, akoda yaushe ina tare daku masoya da makiya????????????_

 

 

*Page 18*

 

Ta dade a xaune amma shuru sadeeq bai dawoba har akayi sallah magrib akayi tashi tayi ta koma dakinta tayi sallah,

Tana idarwa ta tashi ta koma gaban madubi ta fara gyara kwalliyar ta, tsayuwar motar sadeeq tajiyo ta saki wani lallausan murmushi ta karasa gyara fuskar tata sanan ta mike ta fito.

A parlourn sama suka hadu tsayawa yayi yana kallonta tayi matukar kyau amma kuma tayi mugun ramewa sai uban fari data kara,

Kawai saiyaji tabashi tausayi a xuciyarsa yace kilama rashin lpy tayi shiyasa tayi wannan muguwar ramar amma ko sau daya banyi tunanin rashin lpy ne ya hanata ko fitowa parlour ba.

Karasowa inda yake tayi tana murmushi tace yaya sannu da xuwa amma yau ka dade a office din ko aikine yayi maka yawa???

Uhm kawai yace mata ta mika hannu ta karbi briefcase din dake hannunsa tace muje na hada maka ruwa ka watsa saikayi sallah.

Da xai dakatar da ita ne amma kuma saiya fasa yace yau kuma barinaga wane sabon salon aka samo.

Tana shiga dakin ta wuce toilet ta hada masa ruwan wanka ta fito taga bai shigoba dan haka ta fito ta sameshi ya xauna akan kujerar dake parlourn yayi tagumi da alama tunani yake, karasawa tayi kusa dashi tayi ta mika hannunta ta cire hannun dayayi tagumin tace nafa gama kaje kayi wankan.

Bai bata amsaba kawai ya mike yashiga dakin, bin bayansa tayi tana galla masa wata uwar harara sannan tayi kwafa tana fadin mu xa’a gayawa miskilanci, karar wayarta tajiyo a dakinta ta Mike ta shiga dakin tana dubawa taga sunan maryam a screen din tayi murmushi sannan ta amsa wayar tana fadin sis kinje gida lpy????

 

Lpy qalau ftn dai mutumin ya dawo???

Eh yanxu ya shigo na hada masa ruwane ya shiga wanka

Yawwa haka nakeso na fada miki kisaki jiki dashi sosai a kwanakin nan kinji sis

Kema dai saikace kin mantani ai nasan yadda xanyi dashi

Yawwa barina kashe karya fito munata faman surutu

Owk ki gaidamin hjy kinji

Shikenan xan fada mata ta kashe wayar.

Mike wa khairat tayi ta sakko parlourn kasa ta shiga kitchen ta fara kwaso abincin tana jeresu a dining din sama saida ta kammala da komai sannan ta janyo kujera daya ta xauna.

Bata jima da xama ba ya fito sanye cikin kananan kaya yanata xuba kamshi, kallon sa tayi axuciyar ta tace gsky kayi kyau, gani tayi yana niyyar sakkowa kasa xai bar parlour din tayi sauri mikewa tasha gabansa tayi narai narai da idanu.

Kallonta yayi yace ya dai???

Kamar xatayi kuka tace haba yaya sadeeq tun daxufa nake xaune ina jiranka amma kuma ka fito ko kulani bakayi ba xaka tafi abunka ta karasa fada tana dada cinno dan karamin bakinta kamar xatayi kuka.

Baisan sanda yayi mata murmushi ba sbd tayi matukar burgeshi ji yayi kamar ya rungume ta ya tsotse lips din nata dayasha light pink din lipstick wanda tunda tafara magana shi yake kallo,ganin tana shirin kwafsawa Kansa ne ya sanya yayi saurin basar wa yace ai ba fita xanyi yiba xan koma parlourn kasa ne.

 

Owk amma daka xo mun fara cin abincin tukunna saika koma can

Wani irin kallo yabita dashi yana fadin abinci kuma???

 

Kashe mai ido daya tayi tace eh mana

Saida ya kauda kansa tukunna yace banaci

Tsaki tayi axuciyar ta tace karkaci din

Amma a fili sai tayi kalar tausayi tace haba Yaya kar kayimin haka saboda kaifa na bata lokaci na shiga kitchen nayi maka girki amma kace bakaci.

Daure fuskar sa yayi cikin fada fada yace amma idan ban manta ba tun washe garin ranar da aka kawoki gidannan nayi miki kashedin karki sake idan xakiyi girkin ki karki sake kiyi daniba???

Hakane yaya amma ya kamata ace mun daina irin wannan rayuwar me xai hana mu xauna a gidannan a matsayin da muke tun ainihi har a yanxu kanwa nake gareka iyayan mu ne kawai da jama’ar Anguwa suke tunanin mu ma’aurata ne, amma nida kai munsan ba haka bane tunda nanda 20 days ne xaka sallameni nikuma na koma gidanmu a lokacin nasan ka fahimtar dasu baxasu gane cewar ka bijirewa umarninsu bane.

Sbd haka mudaina rayuwa cikin kunci ai ba aibu bane danna girka maka abinci kaci koka manta cewar kai yayana ne???

Sai da yatafi tunanin a xuciyarsa yace ammafa yarinyar nan tayi tunani irin wanda ya dace sbd matukar ban faranta mataba nasan cewar nima baxan samu cikar nawa burinba sbd a lokacin dana kaiwa iyayena dalilin dayasa xan saki khairat nasan dolane su kirata suji ta bakinta don hk dolane na lallaba ta sbd itama tabani hadin kai.

Jiyowa yayi yaganta tsaye tana jiran amsar daxai bata don haka ya sakar mata murmushi yace shikenan muje.

Kai tsaye suka karasa wajan ta janyo masa kujera sannan tafara xuba masa abincin duka biyun ta xuba masa hadi da juice din dasukayi,tunda ta bude flaks din kamshi ya daki hancinsa nan danan yafara hadiyar yau, tana kammalawa tace masa bismillah sannan itama ta xuba nata tajanyo kujera ta xauna tafara ci.

Sai dayaga tafara ci sannan ya diba shima yakai bakinsa tana kallonsa ta gefen ido taga yawani lumshe ido alamun dadin abincin ya ratsashi murmushin mugunta tayi kawai ta karkada kai.

 

Suna kammalawa ta fara kwashe kwanunkan muryarsa kawai taji a sama yana fadin barina tayaki kwashewa abin yabata mamaki amma saita basar tace a’a na hutassheka.

Bai kulataba kawai ya kwashi ragowar ya nufi kitchen dasi binsa tayi abaya tana shirin shiga shi kuma yana fitowa garin matsawa ya wuce kafarta ta goce tayi baya kamar xata fadi yayi saurin rikota har saida takusa fadawa kirjinsa tayi saurin gocewa tanayin kasa da kanta kallonta kawai yayi ya tsuna ya diba kayan data xubar ya juya ya ajje su sannan ya raba ta gefenta ya futa.

 

Karasawa tayi ta ajje sauran kwanukan ta wankesu ta gyara wajan ta fito ta wuce sama tana shirin shiga dakinta ta ganshi yana fitowa daga dakinsa tsayawa tayi tana kallonsa ya karaso yace xan tafi masallaci ko amsarta baijira ba yayi gaba itama bude kofa tayi tashige daki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button