AURAN WATA DAYA

Tana idar da sallah ta tashi ta dauko wasu kayan bacci riga da wando dogu pick color masu dan kauri ta sanya ta dauki hular a hannu ta fito abakin kofa ta tsaya ganisa datayi tsaye bakin TV da Waya a hannunsa alamun waya ya gama yi tsayawa yai cak yana kallonta itama binsa tayi da idanu sai a lokacin ta kula kanta yake kallo tayi saurin saka hular tana tuttura kitson daya furfuto waje sannan ta karaso tana murmushi tace nidai xanje na kwanta sai da safe ta juya da niyyar komawa daki.
Ji tayi ya kira sunanta bata amsa ba sai tsayawa datayi, tanaji ya karaso har kusa da ita sannan ta juyo tana kallonsa gabanta sai dukan uku uku yake musamman dataga ya mika hannu ya cire hular dake kanta jitayi kafar ta tafara rawa tayi baya kamar xata fadi yayi sauri ya rikota ta fada kirjin sa da sauri ta janye jikinta ta xauna a kasa shima tsugunnawa yayi yana kallon kitson sake kanta sannan yace waya yimiki kitso sai a lokacin ta fahimci dalilinsa na cire mata hula.
Da sauri tace Momcy na kira a waya ta turomin mai kitso daxu tayimin ta tafi.
Ohhh ai baxata maryam ko Aisha ce sukaxo karkada masa kai tayi yace tashi ki tafi matsoraciya kawai
Cinno baki tayi tace ai halak ne
Jiyowa yayi yana fadin mekikace ??
Da sauri tace Bb komai tashige dakinta ta kwanta tana fadin uhm ai gwara da ka sakko yadda xanji dadin shige maka, amma da alama ba a banxa sadeeq yayi saurin canjawa haka ba kwafa tayi tace koma Yaya ne ni taimakona kayi.
*Neenat saif ????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat saif????????????????????????????????*
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
*Page 19*
Tun daga ranar rayuwarsu ta sauya idan khairat xatayi girki xata hada da sadeeq duk wani abu daya dace tanayi masa,koda yaushe tana ankare dashi so take tagama gane abubuwan da yake matukar so kuma tayi sa’a batasha wuyaba, cikin kwana 2 tagama gane komai nasa ta fahimci yana matukar son kamshi arayuwarsa duk lokacin datayi wanka taxuba turaruka masu kamshi matukar ta gifta takusa dashi saita kamashi yana kallonta musamman inta sanya kanan kaya kowane irine haka xaita binta da kallo,tun sadeeq bai sakin jiki ya xauna awaje idan tananan harya ya daina sbd ko yaushe maganar ta dayace gareshi yaya kasaki jikinka kadaina sawa kanka damuwa har yanxu amatsayin kanwarka nake,bb batun aure a tsakaninmu sbd baka sona,kuma nima na hakura dakai karka manta farin cikinka shine nawa mexai hana kasaki ranka ka daina damuwa bb Wanda xai maka dole akaina,duk da bansan abinda katsara xaka sanar wa iyayanmu ba nayi maka alkawarin baxan baka kunya ba xan kasan ce mai baka hadin kai domin cikar farin cikin ka.
Duk lokacin dayaji ta furta Kalmar ta hakura dashi saiyaji gaban sa ya fadi, baisan dalilin dayasa Kalmar ta tsaya masa a xuciya ba musamman idan ya tuna ada yadda khairat take matukar sonshi duk da dai bata fiya nuna masa ba kuma bata taba fada masa ba,koda yake ba sakar mata fuska nakeba bareta samu damar fadamin,sbd haka yayi niyyar sakin jiki da ita tamkar yadda suke wasa da darya da Aisha dama can shi ba ban ban tasu yakeba kawai dai shi bayaso taga yana sakar mata face ne tayi tunanin yana sonta,dole ya sanyata farin ciki sbd kar lokaci ya cika yayi niyyar gabatar da kudirin sa iyayan su suga kamar ba gsky bane abinda xaije musu dashi,da wannan tunani yayi niyyar daga yau xai fara nunawa iyayan sa irin sonda yakewa khairat.
Da daddare yana dawowa daga masallaci ya shiga dakinsa ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda yayi kyau sosai ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motar sa ya fito,tsayawa yayi a parlourn yana tunanin yaya xaiyi ya kira khairat shidai baxai iya koda kwankwasa kofar dakinta ba bare kuma ya shiga ciki,gashi ko number bashi da ita hasali ma shi kwata kwata bai taba sanya number dinta a wayarsa ba,shuru yayi yana tsaye har wajan 5mins yarasa abunyi,ji yayi ana taba kofar alamun xa’a bude da sauri ya sauke wata ajjiyar xuciya, tana bude kofar taganshi tsaye nesa kadan da kofar dakin yana kallonta murmushi tayi masa shima ya maida mata tace yayana kayi kyau
Yake yayi yace Allah kanwa???
Tace sosaima Kodai tadi xakaje ne??.
Be bata amsaba sai duba agogon hannunsa dayayi sannan ya dago yace mata yi sauri ki shiga ciki ki sauya kaya ki fito xamuje anguwa.
Da mamaki ta kalleshi xatayi magana ya daga mata hannu,da sauri ta rufe bakinta ta koma ciki tana fadin ikon Allah ko ina xamu kuma??? Uhm koma inane shiya sani.
Yana tsaye ta fito sanye da doguwar riga milk colour tayi rolling da red mayafi tayi kyau sosai hannu ta rike da wayarta tace na gama,saida ya kare mata kallo kamar xaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya wuce gaba tabishi a baya.
Suna fitowa ya nufi daya daga cikin mitocin dake gidan ya tsaya ta karaso sannan ya mika hannu ya bude gidan gaba ya juyo ya kalleta sannan ya yimata inkiya da hannunsa alamun tashiga, bata musa masaba tashiga ta xauna sannan ya rufe kofar ya xagaya yashiga maxaunin direba yatada mortar tundaga nan yayiwa baba mai gadi horn ya fito da sauri ya bude musu gate suka fice yana daga musu hannu sannan ya rufe gate din.
Suna tafe a hanya amma bb Wanda yacewa dan uwansa qala,itakuwa khairat a xuciyarta tana mamakin ina xasuje haka kuma??? Ita ba abin ta tambayeshi ba tunda bai bata dama ba saboda haka taja bakinta tayi shuru,suna fara shiga unguwar ta gane inda suka dosa amma duk da haka bata yarda ba har sai da taga mortar tayi parking a kofar gidan sannan ta yarda tabbas nan din sadeeq ya kahota,horn yashiga yi saiga mai gadi da suri ya xuge gate din sadeeq yacinno hancin motarsa gidan,mai gadi yana gani khairat yafara washe baki yana fadin haji sannu da xuwa murmushi kawai tayimi suka wuce wajan da ake parking sadeeq yanufa ya ajje motar,tun kafin yayi parking din motar taji kar ta balle murfin tafito amma ta dake har sai da ya tsaya,yana tsayawa ta bude murfin motar da niyyar fita harta foto da kafar ta daya taji ya ruko hannunta da sauri ta juyo kamar xatayi kuka don gani take kamar wasa yake mata ba barinta tashiga xai yiba, dariya ce takusa kufce masa sbd ganin yadda tayi kalar tausayi amma saiya basar yace inkika sake muka shiga kayi wani abu ba dai dai ba nida kene kindai san menake nufi, daga masa kai tayi alamun ta fahimtar sannan ta juya xata fita, da sauri yace ji mana ai ban gamaba.
Sake juyowa tayi tana kallonsa yace magana ta biyu ba dadewa xamuyi ba sbd akwai inda xamuje don haka in nace ki tashi mu tafi karki sake ki musamin.
Nan ma kada masa kai takumayi sannan ta juya ta fita tana fita da gudu ta karasa gidan tana isa parlour ta iske Momcy xaune a daya daga cikin kujerun parlour din rahama xaune a cinyarta tana xuba mata shagwaba sai sageer dake xaune a kasa yanacin abinci,sallama tayi batare da tajira an amsaba ta tafi da gudu ta rungume Momcy da rahama tana fadin I rally miss u my mom nd my sweet sis????.
Da sauri Momcy ta rungume ta tana fadin me too my dear, khairat tasa hannu ta dauki rahama daga cinyar Momcy sannan ta xauna ta dorata a cinyarta ta juya ta kalli sageer tace uhm sageer ko magana Bb bata rai yayi yace ai dakika shigo baki kulaniba Momcy kawai da rahama kikayiwa magana.