AURAN WATA DAYA

Ayya dan uwa yi hkr ai kaga kai babba ne shiyasa na fara……sallamar sadeeq ce ta tsai da ita Momcy ce ta amsa tace barka da xuwa dana Ashe tare kuke??
Murmushi yayi sannan ya gaidata cikeda fara’a ta amsa tana fadin badai wannan shagwa babbiyar ce ta sanyaku fitowa yanxu ba???
Kallon ta yayi yaga tayi kasa da kanta ya juya wajan Momcy yace toh kinga ai saboda batada gsky ta kasa koda kallon mu, dagowa tayi tana fadin ka dai fadi gsky ni bb ruwana Momcy bani na takurasa masa ba ta fada tana cinno baki.
Uhm baga irin shagwa bar takiba ke dai har yanxu baxaki girma ba, da ace bansan halinki bane saina yadda bake kika matsa axoba.
Kallonsa tayi yayi mata murmushin mugunta ta bata rai tana fadin shikenan Momcy tunda kin nuna goyon bayansa kikeyi.
Sai a lokacin sageer dake ta fushin bashi aka fara yiwa magana ba ya juya ya gaida sadeeq cikin fara’a ya amsa sannan sageer yamike yana fadin Momcy ni xan shiga daki an bamu assignment inna gama xan fito, toh Allah ya taimaka mom ta fada sannan ya wuce ya tafi.
Sadeeq ne ya kalli rahama yace auta Bb magana ko kallonsa batayiba tace baxan kulakaba tunda baka kawomin ice cream ba,dariya yayi yace tuba nake ki bari inna samu tym xanxo ni da auntyn ki muje musha kinji.
Da sauri ta sakko tana murna ta tafi da gudu tana fadin barinaje na fadawa Yaya sageer, dariya sukayi gaba dayansu sannan suka taba fira ta yan mintuna daga baya sadeeq yace Momcy dady bai dawo bane?? Ya dawo ya fita yana da baki dasuka xo daga abuja shiyasa ya tafi sai anjima xai dawo,mikewa sadeeq yayi yana fadin toh Momcy nidai na wuce inya dawo a gaishe mana dashi,ya juya ya kalli khairat yace kekuma ina jiranki a mota, ya wuce gaba Momcy tana fadin toh saiki tashi ki bishi,bataraitayi tace Momcy nidai anan xan kwana,harara Momcy ta watsa mata tace banson shirme khairat bakiji dadin danaji ba ganin Ku danayi hk da alama bb wata matsala tsakaninki da sadeeq din koh???
Hadiye wani Abu dataji ya tokare mata a makoshi tayi ta kakalo murmushi tace lpy qalau muke Momcy addu’arki ta karbu komai ya sauya ba kamar yadda mu kayi tunani ba ta karasa maganar tana goge hawayen da yaxubo mata,rungume ta Momcy tayi tana cewa masha Allah amma naji dadi ke kuma ki rike biyayya a auranku duk da nasan halinki baxaki bamu kunya ba,gyada mata kai kawai tayi sannan Momcy ta dada yimata nasahi sannan ta tafi tana kuka ta fito ta bude kofar mortar ta shiga yana kallon yadda take kuka amma ya shareta ya tada motar mai gadi ya bude musu suka fita.
Tafiya suke a hanya Bb abinda khairat take sai kuka, da haushi tafara bashi amma dayayi wani tunani saiyaga batada laifi dan tayi kukan rabuwa da iyayan ta,yariga da ya fahimci ba kukan rabuwa da iyayan ta takeba tana kuka ne akan abinda xai faru gaba duk yadda akayi Momcy tayi mata wata magana data shafi auran su amma duk da baisan maganar dasukayi ba yasan cewar khairat baxata taba fadawa Momcy gskyr abinda ke tsakanin suba domin daxata fada mata da tun kafin auran su daya sanar mata xata fadawa Momcy ita kuma ta fadawa Dady shikenan magana ta lalace, wannan tunani daya yine yasan yashi jin tausayin ta shi gaba daya ma ya rasa dalilin dayasa a kwana kinnan yake jin tausayin ta a xuciyarsa,samun waje yayi yay parking din motar sannan ya juyo a hankali ya kira sunanta bata amsaba kuma bata dagoba ta kalleshi ba, shima baijira amsar taba yafara magana da ace nasan abinda xakiyi min Kenyan da ban tawo dakeba ko kuma nace da ban kawoki gidan kuba,ban fito da niyyar xuwa can ba amma sbd na faranta miki yasanya na kawoki kiga mahaifanki sbd koh bb komai nasan xakiji dadin hakan amadadin ace na daukeki na kaiki gidan iyayena batare da kinga nakiba sbd nasan kinyi kewarsu,duk da dai da nan din dacan duk daya ne, amma tunda abin yaxo da haka bari mu koma gida kawai karna kaiki can mom tayi tunanin wani abun nayi miki, daga haka ya juya da niyyar tada motar ya sauya hanya su koma gida.
Da sauri khairat tace yi hkr dan Allah muje wajan Mom din na daina kukan, bai cemata komai ba sai wani kyalle daya dauko ya mika mata ta amsa sannan yaja motar suka fara tafi.
Suna isa kofar gidan yayi horn mai gadi ya leko yaga waye, kasan cewar Dady yadawo,yana ganin motar sadeeq yayi saurin bude musu suka shiga, tare suka fito suka nufi cikin gidan suna xuwa bakin kofar parlour din sadeeq ya dakatar da khairat ta hanyar riqe hannunta kallon sa tayi yayi mata murmushi sannan ya kara hade hannunsa ya sanya daya hannun ya bude kofar suka shiga hannun su sagale da juna,mom dake xaune a kujera ce ta dago idanunta ta kallesu tare da fadada murmushin ta tun kafin su karaso ta mike ta karaso inda suke ta riko hannun khairat tana fadin barka da xuwa my daughter, murmushi kawai khairat tayi ta gaishe da mom, da fara’a mom ta amsa shima sadeeq ya gaishe da ita ta amsa a lokacin ne Dady ya sakko daga part dinsa yana fara’a yana fadin kace yau ya’yan nawane suka kawomin xiyara,nan dai suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ftn dai suna lpy suka bashi amsa da lpy qalau suke, Aisha dake fitowa daga daki ce ta karaso da sauri ta rungume khairat nan dai sukaita fira har saida sadeeq ya tashi Aisha takawo musu abinci sbd daxu Momcy tace akwo musu sukace sun koshi yanxu kuma cikin su yadan ragu,nan Aisha takawo musu abinci sukaci suka koshi aka xauna akaita faman hira daga baya mom da dady sukayi musu nasiha sosai sbd sunji dadin ganin yaran nasu Bb wata matsala, musamman ma mom sbd a tuna ninta sadeeq yaji nasihar ta,sai wajan karfe goma da rabi suka tafi gida,suna isa khairat ta kwanata a kujera domin jinta take duk ta gaji, sadeeq ne ya kalleta yace y dai???
Wlh nagaji tabashi amsa tana cire mayafin datayi rolling, binta yayi da idanu a xuciyarsa yana fadin kai wannan yarinyar komai nata mai kyau ne gsky duk wanda ya samu khairat matsayin mata ya dace yarinyar ga kyau Uwa uba ga ilimi da son addini, uhm amma duk wadan nan abubu wa dake tare dake baxan iya rayuwa dake ba sbd wani dalili bayan hakama bana jin sonta araina yanxu nema kawai nake danjin tausayin ki( uhm sadeeq kenan ya manta cewar tausayin yana daya daga cikin rukunnan soyayya,haka xalika duk soyayyar data fara da tausayi tafi dorewa musamman shida baisan cewar damacan yanason abarsaba????)
Ganin kallon dayake matane yasanyata mikewa tana wata irin mika alamun gajiya,bin jikin ta yayi da kallo ganin yadda take wani kakkarya gabban jikinta da sauri ya kauda idonsa a kanta domin inyaci gaba da kallonta xai iya kwabsawa kansa, ganin yadda ya juyane tayi murmushi ta juyo ta rike hannunsa da sauri ya juyo ta kalleshi tace Yaya xanje na kwanta, kamar mai koyon magana yace toh Allah ya tashemu lpy,ameen yaya ta fada sannan ta juya harta kai bakin kofar sai ta tuna da wata muguntar da sauri ta dawo ta tsaya gaban sa amma takasa magana ganin batada niyyar magana ne ya sanya yace ya dai naga kin dawo???
Cikin kinkina ce uhm…..dama….rigar nan CE…zip din yake bani wahalar..cirewa daxuma da kyar na sanya.wani kallo yabita dashi xaiyi magana tayi saurin kara tsayi ta sanya dan yatsanta daya ta rufe masa baki, sannan tace karka manta har yanxu matsayin matarka nake ba’ayi sakin ba don haka ba haramun bane koka manta ni kanwarka CE??