AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Bai bata amsaba haka itama batayi tunanin xata samu ba don haka tacire hannunta daga bakinsa ta juya masa baya, sai da ya jima sannan ya sanya hannu ya fara xuge zip din,tun a farko daya sanya hannunsa yafara xugwa dan yatsansa ya taba fatar bayansa da sauri ya xaune hannunsa sbd wani shock dayaji,dry khairat taso tayi amma ta basar,maida hannunsa yayi ya karasa xuge mata mutuwar tsaye sadeeq yayi sbd gaba daya yana ganin shape din bayanta wani Abu yaji ya tsarga masa tundaga kansa har tsintsiyar kasa mutsi yayi,shurun da khairat tajine yasan tayi dryr mugunta sannan ta juyo tana juyowa suka hada ido ta kashe mai ido daya sannan tace tnx tawuce gaba tashige daki na dariya.

 

Saida yajima awajan a tsaye sannan ya juya yanufi dakinsa yana fadin yarinyar nan ta gama dani nasan yau kwata kwata baxan iya bacci ba kamar yayi kuka ya bude kofar dakinsa ya shige ya rufe kofa..

 

 

 

*Neenat saif ????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 20*

 

 

Kasan cewar yau weekend ne ya sanya da khairat ta tashi tayi sallah asuba ta koma baccinta, sai wajan 8:00am ya tashi ta sauko kasa, kai tsaye kitchen tafa nufa tafara hada break fast, saida ta tabbatar tagama hada komai sanan ta fito tafar gyara gidan kafin ya karasa,tana gama gyara parlourn ta wuce kitchen ta sauke ta xuba a flaks ta xuba xubawa baba mai gadi ta kaima sa nasa , sannan ta dawo taci gaba da aykinta,saida ta tabbatar tagama gyara ko ina har dakinta dakin sadeeq ne kawai ya rage,sannan ta tashi tashiga wanka,tana kammalawa ta shirya cikin wana rantsatsiyar atamfa da dinkinta ya amshi jikinta kai kace ajikinta akayi dinkin,tana kammalawa ta fito sai xuba kamshi take,kitchen ta nufa ta dauko abincin taxo ta jeresu a dining sannan ta nemin kujera ta xauna,ji tayi kawai tana kewar Momcy ta daga idonta ta kalli agogo taga 10:30 wayata ta dako takira Momcy suka gaisa hardasu rahama da sadeeq, rahama ce mai tambayar ta yaushe xasuxo da Yaya sadeeq aje shan ice cream din??? dariya khairat tayi tace yanxu bacci yake bariya tashi saina tambayar miki shi,nan dai sukayi sallama da Momcy ta kashe wayar tanajin dadin yadda taji mahaifiyar tata cikin farin ciki,tausayin mahaifiyar tata taji sbd tasan Momcy tana farin cikine sbd yanda tagansu jiya xatayi tunanin Bb wata matsala,kamshin tura ransa dataji ya mamaye wajan ne ya tabbatar mata da isowar sa a hankali ta dago ta kalleshi,gani tayi yayi matukar yimata kyau sanye yake cikin kananan kaya blue din jins ne ajikinsa sai White din riga wacce tai dai dai da jikinsa yayi matukar kyau gashinnan nasa yayi luf sai kyalli yake da alama yaci kudi,fuskar sa ta karewa kallo ganin yadda yaketa kallonta idanunsa ta kalla taga yadda suka kankance da alama bai samu ishashen bacci ba,tmby kanta take wane irin kallo sadeeq yake mata sbd har yanxu yaki dauke idonsa a kanta sai itace tayi saurin yin kasa da kanta.

Shiko sadeeq tunda ya fito yake kallonta har ga Allah tayi matukar yimasa kyau domin shi yanxu ya daina mamakin irin wannan kyau na khairat kullum gani yake kamar sauya ta ake,a xahirnace ba kyawun datayi bane yasanya ya dade yana kallonta hakaba kawai yana kallo tane yana fasalta irin hukuncin da xai mata sbd jiya tana sane tayi abinda tasan xata tada masa hankali dadin dadawa ma harda sanya shi yayi abinda tasan tababas in yayi saiyaga surar jikinta,tunawa yayi da yadda jiya kwata kwata baiyi bacci ba ga wani axababan ciwon mara dayayi a daran,tmby kansa yayi toh wai kodai khairat ta fahimci yadda nakeda saurin sha’awa ne tabbas tunyana gida haka yake abu kadan ketada masa hankali, amma baisan yadda akayi wannan muguwar ta fahimtar ba,koda yake Bb wani hukkunci da xan mata xulamata ce tajawomin sannan nida nake so na lallabata ai fushi ba nawa bane.

Karasawa yayi inda take ya xugun na gabda ita ya sanya hannu ya dago habarta a hankali suka hada ido jiyayi gaban sa yayi wani irin faduwa,da sauri yayi kasa da kansa da kyar ya dake yaseke kallonta yace kanwa yau ko gaisuwa babu????

Batarai tayi cikeda shagwaba tace toh ba kaibane tun daxu na kammala break fast amma baka fitoba.

Yanda tayi maganar ba karamin burgeshi tayi ba a rayuwar shi yana matukar son Mace mai shagwaba yarinyar ta hada duk abin da yakeso, murmushi yayi ya rike hannunta yace ayyah sorry yar kanwata tashi muje muci abincin,tashi tayi tabishi ya xauna a kujera itakuma ta xuba musu abincin suka soma cin abincin.

Bayan sun kammala ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke sannan ta dawo parlour din,xaune ta ganshi yana kallo ta samu guri kusa dashi ta xauna,har tsawon yan mintuna suna xaune bb wanda yayiwa wani magana,bacci khairat taji yana dan fuxgarta sbd batayi dan gadon data sababa,jingina jikinta tayi a jikin kujerar dasuke xaune,tun tana gyan gyadi har tasoma bacci domin haka kurum taji batason kwanciyar domin wani lokacin har gajiya take da kwanci amma kuma bacci baya isarta wayarta ace bataci abinci ba.

Sadeeq ne ya dago da sauri jin khairat ta jingina da kafadar sa,kallonta yayi da mamaki axuciyarsa yace wannan yarinyar wai bacci tayi??? Uhm wata kilama ba bacci takeba wani sabon salon iskancin ne,a hankali yayo kasa da kansa ya tsaya yana kallon idanunta dake alumshe tsawon mintuna yaga ko motsawa basayi, murmushi yayi yace Ashe dai baccin take inda ba bacci takeba nasan xuwa yanxu dole ta motsa idonta,juyawa yayi yacigaba da latsa wayarsa da tun daxu abinda yake kenan,

Jimawa kadan yaji ta gangaro ta dawo da kanta xuwa cinyarsa ma’ana tayi filo da cinyar sa,ajje wayar yayi ya juyo yana kallonta baya ganin fuskarta sbd ta juya kanta ne tana kallon gefe,shuru yayi a xuciyarsa yana fadin wannan yarinyar tana Neman ta takuramin wlh,juyi tayi a hankali tado tana kallon dai dai fuskar shi yayinda dan kwalin ta ya xame,tsayawa yayi yana kallon bakin gashinta sidik Wanda yasha xara xaran kitso, baisan lokacin da yasanya hannu yana shafa kanta a hankali, dawo da idanunsa yayi dai dai fuskar ta yana kallonta yaji gabansa ya fadi a hankali ya runtse idanunsa sannan ya bude su akan fuskar khairat, ya ilahi wai meyasan idan na kalli yarinyar nan nake jin fadukyawunta ??? axuciyarsa yayiwa kansa wannan tambayar, ta daya bangaren xuciyarsa tabashi amsa da xata iya kasan cewa sbd kyawunta ne????????‍♂

A hankali ya sake kallon face dinta har lokacin hannunsa yana kanta ya kasa daukewa,gani yayi Kamar murmushi take masa a fili ya furta gsky bantaba ganin yarinyar da take matukar kyau idan tana bacci ba jiyayi kamar karta farka kawai yayita kallon fuskar ta haka kawai yaji kallon nata yana sanyashi nishadi.

A hankali ya tsurawa dan karamin lips din ta idanu mika hannu yayi yana xagaye lips din nata da hannunsa, itakuwa khairat baccinta take cikeda kwanciyar hankali batasan abinda ke wakanaba.

Jiyayi yanayin jikinsa yafara sauyawa,hankalinsa yayi mugun tashi tabbas inyaci gaba da xama a haka xa’a samu matsala,dan karamin tsaki yaja a hankali ya xame khairat daga jikinsa ya kwantar da ita kan kujera ya dauki key din motarsa ya fice daga gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button