AURAN WATA DAYA

*Kuyi hkr da jina dakukayi shuru jiya banida lpy ne, yanxuma da kyar na iya yin wannan sbd haka xaku iya jina shuru amma insha Allah innaji da dauki xan yi kokarin yimuku typing, ina godiya da irin kaunarku gareni????????*
*Neenat saif????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat seif????????????????????????????????*
*Dedicated to my lovely fan (AURAN WATA DAYA fans group) (AUNTY MAMIE’S novel fans group) (DAN KISHIYATA fans group) (AURAN SIRRI fans group) da shauran groups wadanda ban lissafo ba ina yinku irin totally dinnan????????????*
_masoya ina godiya da addu’arku gareni???????? bansan da wane irin kalami xanyi godiya garekuba shiyasa na sadaukar da wannan page gareku baki daya????_
*Page 21*
Tunda sadeeq ya fita gidan kaitsaye ya wuce wajan Abdul, tunda yaje Abdul ya dameshi akan maganar maryam har abun ya isheshi domin shi yace bb ruwansa da maganar gashi ga maryam dinnan amma shi ya barshi yaji da damuwarsa, ganin bashida niyyar kyaleshi ne ya sanya ya kwanta ya rintse idanunsa har baccin dole ya kwasheshi.
Sai da Abdul yaji ana kiran sallar axahar sannan ya tasheshi sukayi sallah, suna idarwa sadeeq yayi masa sallama ya wuce gida.
Yana isa gidan ya iske khairat harta tashi gidan sai kamshi yake da alama har tayi girki, waigawa yayi ya kalli dining yaga kulolin abincin a kimtse falon sai kamshi yake xubawa ta gyara shi tsaf murmushi yayi a fili ya furta yarinyar nan badai tsabta………motsinta dayaji ne ya sanyashi kasa karashe maganar sa ya juya yana kallonta tana sakkowa daga steps din.
Sanye take da farin wondo jins sai orange din t-shirt ta sanya farin dan kwali a kanta kitsonta ya sakko gadon bayanta, da murmushinta ta karaso kusa dashi tana bata rai kamar tayi kuka tace uhm sannu da xuwa yaya.
A hankali ya iya furta “yawwa” sbd tsabar tafiya da hankalinsa da tayi a hankali ya yayi kasa da idanunsa yana mata kallon up & down sannan ya tsaida idanunsa akan face dinta dayaga ta bata rai tana kallonsa, haka kawai saiyaji bb dadi sbd yafiso yaga face dinta dauke da murmushi.
Ganin yayi mata shuru batare da yafurta mata komai ba sai wani kallonta kawai yake baima damu da ganin sauyin daya gani a fuskarta,kawai saitaji ranta ya baci kwalla na shirin xubo mata da sauri ta juya xata bar wajan, jitayi ya riko hannun ta ta baya tsayawa tayi cak batare data juyo ta kalleshi ba, kusan 2mns suna tsaye a haka batare daya cemata kala ba,wani mugun haushi ya bata ta fixgi hannunta daga nashi amma taji ya riketa gam, tsayawa tayi tana jin faduwar gaba juyowa tayi tana kallonsa kawai, riko daya hannunta yayi yajata har xuwa wajan kujera sannan ya tsugunna gabanta har lokacin hannunsa na rike da nata,ita kuwa kallon sa kawai take da mamaki domin taji mexai cemata sai kissima abubuwa take a xuciyar ta….
Amma fa kanwa kinyi matukar kyau kamar bakeba
Kalam da suka tsaidata daga lissafe lissafen da takeyi a xuciyarta kenan waige waige tashiga yi ko xataga wanda yayi maganar duk da tana kallonsa lokacin da yayi maganar, ganin yanayi mata murmushi ne ya sanya ta kauda kanta gefe batare da tace mai kala ba.
Hannu ya sanya ya juyo da fuskarta yace uhm wannan fushin kuma na mene tunda na shigo ko murmushi bakiyiba meya faru ne???
Tsuke dan karamin bakinta tayi kamar baxatayi magana ba sannan tace ba kai bane ba
Murmushi ya sake yi yace toh a fadamin me nayi saina bada hkr
Uhm tun daxufa ina bacci ka lallaba ka fita ka barni ni kadai bayan kasan yau weekend ne Bb inda ake xuwa.
Ohh wannan ne laifina???
Kai kawai ta daga masa
Toh kanwa yi hkr wani ixuri ne ya fitar dani kuma naga kina kina bacci ne kinsan Bb kyau tashin mutum yana bacci musamman ma keda kike kanwata banason naga na katse miki jin dadinki.
Uhm kamar gaske nidai nasan wani abun kake bukata kake wani lallabani saikace kwai
A xuciyarta tayi wannan furici
A fili kuwa murmushi tayi tace toh shikenan ya wuce muje muci abinci, tashi sukayi gaba daya suka nufi dining din inka gansu gwanin sha’awa(nima saida na kyasa amma narasa dalilin dayasa sadeeq bayason khairat ☹☹ amma muje xuwa????)
Xaune suke a falon Dady yana cin abincin shida rahama sageer kuwa yana dakinai ,dady ne ya kalli Momcy yace amina (sunan mahaifiyar khairat kenan) daxu mun hadu da Yaya(mahaifin sadeeq kenan) yake sanarmin su sadeeq sunxo jiya.
Ayya mantawa nayi alhaji sbd jiya saida nayi bacci ka dawo, ai har nan gidan sukaxo amma basu samekaba.
Ayya amma banji dadin hakaba,amma dai bb wata matsala a tsakaninsu dai koh????
Washe baki Momcy tayi tace yadda dai nagansu jiya Bb wata matsala tsakaninsu baka gansuba gwanin sha’awa sai dai kawai mucigaba dayimusu addu’a.
Masha Allah ai haka akeso Allah yabasu xaman lpy ya dauwwamar musu fa farin ciki axaman auransu.
Ameen ameen Momcy ta fada yayin datake daukar rahama data fara gyangyadi ta wuce daki da ita.
*Neenat seif????????*
[12/19, 1:25 PM] 0mmr Farouk: ????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat????????????????????????????????*
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
_Aunty Mamie’s ina tayaki murnar sauke littafin????????????????????????USTAZIYA KO YAR DUNI YA????????♀????????♀????????♀ Allah yasa sakon dakikeso ki fada kar akansa ya isa ga wadanda akeso su fahimta, Allah yasa al’umma su amfana da abinda kika rubuta???????? munan muna jiran sabon novel mai xuwa????????????_
*Page 22*
Washe gari misalin 2:00pm khairat xaune a falo tana jiran dawowar sadeeq daya fita xuwa gidan su abdul tun 12 ya fita amma har yanxu shuru, gashi ta gama abinci amma har yanxu bai dawoba, bata damu da dadewar saba, sbd ita dama ba wuriminta bane kawai tana yimasa abinda ya kamata ace dole idan lokacin rabuwarsu yayi shima yaji bb dadi a tattre dashi, amma tariga da ta fahimci sadeeq yadan sauya a kwanaki 2 nan duk da haka baxata taba sawa ranta cewar sadeeq yafara sonta ba sbd batasan wane irin abu yakeda niyyar fadawa iyayan su ba idan lokacin rabuwarsu yayi tafi bawa xuciyarta cewar hakan yana daya daga cikin shirnsa ne kawai.
Tunda suka yi parking motar su sadeeq ya fito da sauri yana shirin shiga gidan, Abdul ne yace ya dai naga kanata sauri haka???
Jiyowa yayi yace akwai abinda nakeso xan dubane amsa mukullinnan ka rufe motar, amsar mukullin Abdul yayi shi kuma ya shige gidan.
Da sallah ya shiga gidan tana xaune a daya daga cikin kujerun fake parlour din ta amsa masa tana kallonsa ganin yadda ya kura mata idanu.
Ajjiyar xuciya ya sauke ganin ta dayayi sanye da atamfa riga da xani a jikinta,tunda taxo gidan bai taba ganin ta da xaniba sai siket ko riga da wando ko doguwar Riga, murmushin jin dadi yayi sbd tunda suka taho da Abdul yake jin faduwar gaba, haka kurum yaji bayaso suxo su shigo shida Abdul su tadda khairat da irin shigar da take ta kanan kaya shiyasa yake ta sauri domin yariga Abdul shigowa ya sanyata ta suturta jikinta sai kuma yayi sa’ar samunta da shigarda baiyi tsammaniba.