AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Toh wai meyasa na damu da yaganta a hakane???

Uhm tabbas nasan cewar hakan yana nufin kishi kenan.

Amma mexaisa nayi kishi akan khairat???

Xuciyarsa ce tabashi amsa da sbd khairat ta kasance kanwar ka dan haka dole kayi kishi akanta kamar yadda kakeyi akan Aisha.

A xuciyarsa ya furta tabbas hakane, karasawa yayi kusa da ita yana kallonta.

Dauke kai tayi kamar bata ganshi ba, mika hannu yayi ya amsa wayar datake hannunta bata hana shiba ta mika masa amma still bata kalleshi ba, kanwa ya akayi ne???

Bata bashi amsa ba sai juyowa datayi ta kalleshi, murmushi yayi yace na gane laifina, amma kiyi hkr na tsaya mun taho da Abdul ne shiyasa…….. Sallamar Abdul ce ta katseshi da fara’a khairat ta amsa, karasowa yayi yana fadin amarya bakya laifi.

Murmushi tayi tace kona kashe dan masu gida

Kallonta sadeeq yayi yace ai ko kaxar masu gida kika kashe sai an hukuntaki bare kuma dan masu gida

Uhm dadin tama ko kaxar babu bare kuma Dan.

 

Naji nidai kawai yanxu yunwa nakeji ki tashi ki hada mana abinci.

Ai tunda naji ka dade nabawa almajiri abincin ka.

Dry Abdul yayi yace ammafa kin kyauta kuma kin burgeni yaseen, harara sadeeq ya jefeshi da ita sannan ya mike yace pls kanwa dan Allah ki tashi ki hada mana.

Ai dama gashi can sai na gama sai dai na xuba muku kawai

Karasawa sukayi ta xuba musu sannan ta xuba nata ta dawo kan kujera ta xauna ta soma ci.

 

Suna kammalawa ta kwashe kayan ta gyara wajan sannan tadawo falon ta samesu xaune suna fira,kallon sadeeq tayi tace yaya barina koma daki akwai abinda xanyi.

Toh shikenan ya furta yana sauya channel a TV

Abdul ne yayi saurin cewa haba sadeeq yaxa kayi min haka kuma???

Me nayi kuma bagaka gatanan ba ko sokake na xauna nayi mata bayani???

Uhm a’a

Kallon khairat yayi yana Sosa keya yace dama wajan ki naxo nayi wannan bawan magana amma naga rainamin hankali kawai xeyi.

Guri ta nema ta xauna tana cewa Allah yasa ba laifi nayi ba.

A’a babu abinda kikayi, dama akan maryam ne xanyi miki magana,tun kafin bikin Ku naji maryam ta burge ni harga Allah ina sonta nayi niyyar fada mata shiyasa na amsa number dinta lokacin bikin Ku amma kuma inna kirata saina kasa fada mata,bawai ina tsoron fada mata bane. Kawai ina tunanin amsar da xata bani bansani ba ko tanada Wanda takeso shiyasa na kasa fada mata,na damu da yawa shiyasa nace barina yimiki magana sbd nasan ke kadai ce xaki bani kwarin guiwa akan maganar nan.

Ajjiyar xuciya tayi sannan ta juya ta kalli sadeeq taga kwata kwata bama tasu yakeba wayar shi kawai yake dannawa,juyawa tayi ta kalli Abdul sannan tafara magana.

Banda abunka Yaya Abdul ai bakada matsala kawai ka sameta kayi mata magana batun kotana da Wanda takesoma bai tasoba sbd kaima kasan ba’ayi mata miji ba dan haka kaima xuwa xakayi ka jarraba sa’arka kuma nasan tabbas xaka dace sbd kanada tsari da xubin hallittar da bb wata mace da xata kika kaima kasan hakan.

Sai a lokacin sadeeq ya dago ya watsa mata wani mugun kallo akayi sa’a kuwa itama ta kalleshi kawai ta dauke kanta.

Kai amma fa naji dadin maganar ki insha Allah xanyi mata magana.

Har suka gama sadeeq baisa baki a. maganar ba suna kammalawa ta mike ta koma daki.

Saida sukayi sallah la’asar sannan sadeeq ya tafi maida Abdul gida sbd a motar sadeeq din sukaxo,sunatafe a hanya Abdul natayi masa magana amma yaki kulashi kadan kadan yake bashi amsa,haka kawai yakejin wani mugun bacin rai wai agaban sai khairat xata xauna tana wani yabon Abdul harda cewa wai kowace mace kenan harda ita???

Suna isa ya sauke Abdul batare da yashiga gidan ba yajuya motarsa yanufi gidan yana tunanin abin da xaiwa khairat….

 

 

 

*Neenat seif????????*
[12/19, 1:25 PM] 0mmr Farouk: ????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat seif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my sis Ameena ina tayaki murnanar kara sheka Allah ya albarkaci rayuwar ki wannan page nakine na mallaka miki shi kiyi yadda kikeso dashi Allah ya kawo lokacin auranki muje niger musha biki????????????????????????????????*

*Page 23*

 

 

Allah Allah yake yaga ya isa gidan, yana karasawa yayiwa baba mai gadi horn da sauri ya karaso ya bude masa gate yana masa sannu da xuwa,ko bi takansa beyiba ya wuce yayi parking motar ya fito ya rufe yanufi cikin gidan.

Be sameta a palon kasa ba shiyasa yanufi saman.

Tana xaune kan kujera ta gama waya da maryam tana bata labarin yadda sukayi da Abdul kenan ta ajje wayar taji motsin tahowarsa bata ko motsa daga inda takeba bareta dago taga ta inda xai bullo.

Ganinsa kawai tayi a saman kanta yana wani cika yana batsewa, mikewa tayi daga kwanciyar datayi ta xauna tana kallonsa, ganin bashida niyyar yin magana ne ya sanya tace lpy kuwa naganka a haka???

Au ke bakisan abinda kikayi ba kenan har kike tmbyt meya faru???

Jin maganar tayi wani iri tunda ita dai tasan Bb abinda tayi,yatsuna fuska tayi tace nidai a iya sanina bb abinda nayi ????????‍♀

Gani yayi tama raina mai hankali yaji ransa yakuma baci,kasa yayi da kansa yadda yana iya jiyo numfashin ta itama tana jin nasa, gabanta taji yana faduwa amma ta dake.

A kausashe ya soma maga, “wato sbd kinga ina miki wasa 2 days shiyasa kika rainani,tsabar iskan ci a gabana xaki xauna kina yabon wani kato sbd kin maidani sauna koh???

 

Sai a lokacin ta gane laifin nata,murmushi tayi a xuciyarta tace ” tabbas yau anxo wajan da alama ka shaka yanxu xan kuma shaka maka.

 

Kawai dan nafadi gsky shine xakaxo kana huci wai nayi maka laifi ni ai banga aibu a abinda nayiba.

Kallonta kawai yayi yace “oh rashin kunyar taki xaki Nuna min kenan, toh wlh xan gar gadeki duk ranar da kika sake aikata maka mancin irin wannan wlh ranar xakisan koni waye.

Wai kai akan Abdul kaxo kake yimin wannan abun???

Kallon mamaki yabita dashi a harxuke yace waye shi Abdul din a wajanki???

Wai ko kin manta cewar ni mijinki ne kike nuna damuwar ki akan wani harda yabonsa kuma a gabana ku kunyar idanuna bakiji ba(chab su oh oh sai yau aka tuna da igiyar aure????)

Wata uwar harara ta hurga masa sannan tace aure kai kasan shi kuma nayi din ko kamanta matayin da muke dakai ne acikin gidan nan???

Kuma indai akan abin da na fada ne sai dai kayi abinda kaga xaka iya ko auransa nace xanyi bakada yadda xakayi sbd ai ba haramun bane tundai kai dakake dan uwana baka dauki auran mu da muhimman ciba sai yanxu xakaxo kana gayamin wata magana kuma wlh yanxu na……..

 

Bata karasaba taji saukar wani gigi taccen mari a kuncinta,hannu ta sanya ta dafe wajan tana kuka ta dago jajayen idanunta tana kallonsa.

Juyowa yayi da niyyar sake magana amma ya fasa ya karkada kai kawai ya wuce dakinsa ya rufe kofa.

Saka kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta dafe kanta tana wani irin kuka mai tsuma xuciya, taresa gane metakiji gameda abinda sadeeq yayi mata ita abin yana bata mamaki sannan yana bata haushi da takaici,me tayi masa da xai daga hannu harya kwada mata mari,kawai daga magana ita da tana xaune dashi ne kawai na wucin gadi kafin wa’adinta ya ciki,gsky baxata iya juraba tunda gashi yanxu abin ya sauya harda duka wai ita sadeeq ya mara abinda yafi tsaya mata a rai kenan wani kukan tasake fashewa dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button