AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Xagaye dakin kawai yakeyi xuciyarsa nayi masa maganar tace keyi masa yawo a kwakwalwa. “Ko auransa nace xanyi bakada yadda xakayi”. A fili ya furta ina Sam hakama baxata faruba,dafe kansa yayi dayaji yana Sara wa ya salam wai mena aikata ne???

Miye hurumina a cikin maganar nan tasune???

Meyasa na damu da kalaman datayi masa ne???

Tunawa yayi da Marin da yayi mata sai a lokacin ya kula da sautin Ku kanta dayakejj har cikin dakin nasa, jiyayi baya son kukan nata gaba daya sautin dagula masa lissafi yake yanajin wani ari a xuciyarsa amma baxai iya xuwa ya lallasheta ba.

Ya Allah wannan duk laifi nene khairat bakida laifi ni nasan da haka amma bansan meya tunxurani na aikata hakan ba.sautin kukan tane kawai yake damunsa toshe kunnansa yayi sbd xuciyarsa baxata juraba da sauri ya dauki key din motar sa ya bude kofar ya fito.

Har yanxu tana nan inda ya barta tana kuka,kasa kallonta yayi da sauri ya wuce ta ya fice daga gidan.

Sake fashe wa tayi da wani kukan, tana bukatar Wanda xai rarrasheta amma kuma baxata iya kiran Momcy ba to waxata kira???

Maryam mana

Xuciyarta tabata amsa, daukar wayar tayi ta soma kiran maryam.

Ringing daya ta amsa wayar hadi da sallama.

Tana kuka ta amsa sallamar

Da sauri maryam tace sis meya faru lpy najiki haka???

Saida tayi mai isar ta sannan tabata lbrn abinda ya faru takuma fashewa da kuka tana cewa maryam harda mari fah.

Murmushi maryam tayi tace haba besty meyasa wani lokacin kike kai hankalin ki nesa ne???

Ai mu yanxu abin nema ne ya samu.

Tsaida kukan tayi cikin mamaki tace kamar Yaya???

Uhm baki ganeba kenan, kinsan meyasa sadeeq ya aikata abin fa yayi miki yanxu????

Mexaisa yayi min haka kuwa banda tsanata dayayi dakuma xallar xalunci kawai, ta bata amsa tana dada tuna lokacin da ya mareta.

Murmushi maryam tayi tace nop ba haka bane.

Wannan Abu da sadeeq yayi yana nufin kishii.

Kishi kuma????

Eh mana

Maryam karki manta fa sai kana son Abu sannan kake kishin sa,shi kuma sadeeq baya sona.

Da kenan, maryam ta bata amsa

 

Uhm kin dai fada kawai sis amma bawani sona da yake.

Baxaki ganeba khairat amma kici gaba da hkr muna gab da samun nasara.

Shikenan sis xanyi kokarin yin hakan

Yawwa dear

Nan dai maryam ta dada rarrashin ta harta warware sannan sukayi sallama,

Tashj tayi tashiga daki sbd bataso yadawo ya sameta tayi niyyar saiya gane kuransa tunda har ya iya sanya hannu ya mareta..

 

 

 

 

*Neenat seif????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat seif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

2 eyes sukayi dashi,yana tsaye a bakin kofa ya jingina fa bango hannayen sa xube cikin aljihun sa,sanye yake da kana nan kaya ya xuba mata idanu.

Kasa tayi da idanunta ta kalli rigar dake jikinta iya gwaiwa ko hannun arxiki bata dashi, shima kallota yayi har kasa kamar yadda yaga tayi murmushi kawai yayi sannan ya tako a hankali ya karaso gab da ita.

Sun kai tsayin mintuna a haka amma ya kasa magana shin hakuri xai bata koko tambayar ta xaiyi dalilin dayasa take boye masa bataso su hadu???

Ganin bashi da niyyar yimata magana ne ya sanya ta tsame hannunta daga abin da takeyi ta rabeshi xata wuce

Tana xuwa gab dashi ya mika hannun sa ya xagayo kugun ta dashi sannan ya jawota ta dawo daf dashi ta yadda tana iya jiyo numfashin sa shima yanajin nata.

Da sauri ta dago ido tana kallonsa, shima kura mata idanu yayi har sai da ta dauke nata idanun,a hankali ya soma magana.

Uhm khairat ko gaisuwa babu???

Bsta bashi amsaba sai kallon mamakin datake binsa dashi tunda take a rayuwar ta bata taba jin ya kira sunan taba sai dai yace mata yarinya,yanxu ne ma yake cemata kanwa.

 

Ganin taki magana ne ya sanya yace toh ni barina gaishe ki.

Ina kwana???

 

Kunyar gai suwar tashi taji da sauri tace ina kwana Yaya???

Uhm sai dana roka???

Nanma still bb amsa.

 

Sai sukur sukur take xata xame jikinta daga nashi,ganin hakane ya sanya ya dada jawota harta hade da jikinsa.

Sai da yayo kasa da Kansa dai dai wuyanta sannan ya soma magana.

 

Nasan da cewar ban kyauta miki ba akan abinda na aikata miki,duk da nima bansan meyasa na aikata hakan ba, amma…..

 

Dakatar dashi tayi ta hanya sanya dan yatsanta akan labbansa sannan ta fara magana.

 

Ni banyi fushi akan abin da kayi min ba dan haka bana bukatar wani bayani naka ko kuma bada hakuri,uhm nama dade da sanin baxaka iya bani hakuri koda kuwa abinda ya faru yafi wannan.

 

Kallonta yayi yana naxarin ta sannan yace

Idan ba fushi kike dani ba mai yasa kika kaurace min??? yau kwana 4 kenan ban saki a cikin idanuwa na ba,bayan kinsan amanar ki aka bani idan wani Abu ya sameki ni xa’a bincika kuma bayan hakama………

 

Dakatar dashi takuma yi ta hanyar daga hannun ta alamar ya isa, sannan ta fara magana

Da’ace ka damu da amanata da aka baka da duk hanyar daxaka bi kaga awane hali nake xakayi kokarin binta, shin ko sau daya kataba leka dakina domin kaga wane hali nake ciki???

Shuru yayi ya kasa bata amsa.

Janye jikinta tayi daga rukon dayayi mata sannan taci gaba da magana.

Ya xama dole naci gaba da kaurace maka har xuwa lokacin da xan bar maka gidan ka, ni daxaka taimaka min ma ka sakeni tun a yanxu wlh daka taimaka min, domin daga mari wata rana kuma sai duka.

Jin maganar tata yati tamkar saukar aradu, wani irin sarawa yaji kansa yanayi,gaba daya yama kasa magana kawai binta yake da idanu.

Ganin baida niyyar yin magana ne yasanya tasake cewa

 

Ni dai koda baxakayi magana na gama yanke hukunci kawai ka sakeni,xan bakka ka yankewa kanka hukunci nan da dare nidai bukata ta kawai ka sawwa kemin wannan jarababbar igiyar auran taka domin nagaji.

 

Tana kaiwa nan ta fice daga kitchen din ta barshi tsaye kamar mutum mutumi, gaba daya ya kasa gane a wane hali yake ciki, me maganar khairat take nufi???

Me kuma yake damunsa haka???

Bashida amsa kuma bb mai amsa masa wadannan tambayoyi.

 

Tana fita ta sumu guri kan kujera ta xauna ta dora kafa daya kan daya tana karkada su.

Tana xaune taji fitowar warsa daga kitchen din a hankali ta dago idanunta kasan cewar kofar kitchen din take kallo, a sanyaye ya fito daga kitchen din,ganin ta a falo din ne yasanya ya tsaya ya kura mata idanu kamar maiso yagano wani abu,kauda kanta gefe tayi domin baxata iya jurar kallonsa ba.

 

Wucewa yayi kai tsaye ya tafi dakinsa

 

Murmushi tayi mai ciwo tarasa gane wane irin hali sadeeq yake dashi, ita bata fahimci komai ba mai shurun nasa yake nufi???

Ji tayi hawayen na shirin fara xubo mata tayi saurin sanya hannun tana gogewa.

Yana shiga dakin sa ya nemi gefen gado ya xauna,hannun biyu ya sanya yana tallafo fuskar sa, yarasa gane meke damun sa akan khairat a tsukukin lokacin nan gaba daya khairat ce ke yawo a xuciyarsa idan yana office tunanin ta yake,hasali ma tunda ta daina bari su hadu ya kasance baya iya yin bacci kamar yadda ya saba,tunanin ta kawai yakeyi idan ya runtse idanunsa yakan ganota a lokacin da tayi wani Abu daya burgeshi, ajjiyar xuciya ya sauke tabbas yau daya ya fahimci wani abu Wanda da yakasa ganewa.

 

Mikewa yayi yanufi drawer ya bude ya dauko invitation din bikinsu da khairat, date din ya duba sannan ya lissafa kwana kin gabansa kawai yaji ya fadi, tabbatar gobe saura kwana goma kwana kin daya tsara xai saki khairat xasu cika.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button