AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Da mamaki khairat ta kalleta xatayi magana……..maryam ta katseta ainace xanyin miki bayani karki damu tashi muje gida kawai.

Mikewa sukayi suka kintasa suka fito.

Bb abinda khairat ke tunani axuciyarta tana wa kanta tambayoyi

Shin me maryam xatayi ne?

Kuma tacemin bb matsala kamar yaya?

A haka ta manta da maganar domin tasan wacece kawar tata…..

 

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:25 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 3*

 

 

*Wace ce khairat da sadeeq?*

Asalin mahaifin sadeeq da khairat yan uwane na jini mahaifin sadeeq shine babba wato alh mukthar mahaifin khairat shine mai binsa sunansa alh kabeer su uku mahaifansu suka haifa akwai mace wacce ke bin mahaifin khairat amma Allah yayi mata rasuwa sakamakon hatsari dasukayi tareda mahaifan nasu sai su biyu suka rage.

Mahaifin sadeeq shahararran dan kasuwane a garin kano, itama mahaifiyar sa haifafiyar garin kano ce hjy xainab sadeeq shine dansu na fari sai kanwarsa dake binsa mai suna Aisha shekara shida ke tsakaninsu da sadeeq daga kanta Allah bai kuma basu haihuwa ba har xuwa wannan lokacin.

Mahaifiyar khairat haifafiyar garin gombe ce sun hadu da alh kabeer ne a garin gombe sakamakon daurin auren wani abokinsa dasuka je a gombe har Allah ya Nufa taxama matarsa.

”Ya”yansu uku ta farko itace khadeeja wato (khairat) sunan mahaifiyar su alh kabeer sai mai binta sageer saikuma autar su rahama, khairat shekarunsu daya da Aisha kwana goma tabawa Aisha, rabin rayuwar ta agidansu sadeeq takeyinsa tareda Aisha tun sadeeq yana gida khairat ke mutuwar sonsa har xuwa sonda yatafi India karatu a lokacin yana karantar medicine babba matsalar shine ko dariya sadeeq baya yiwa khairat ko fira sukeyi inta shigo gidan tashi yake ya fita har hajiyarsu ta fahimta, tayi kokarin yimasa fada amma ya nuna mata shi rainine bayaso shiyasa kawai baya sakarmata fuska da haka hajiya ta hkr ta kyaleshi.

Lokacin da sadeeq xai tafi India khairat tayi kuka kamar ranta xai fita amma har xuwa lokacin bb wanda tafadawa damuwarta sai kawarta da suka hadu a school wato maryam tana yawan bata lbrn yaya sadeeq da irin abubuwan dayake mata kullum maryam na bata shawarar tayi hkr komai mai wucewane.

Lokacin da sadeeq ya kammala karatunsa yadawo gida har ya fara aiki ne mahaifinsa ke sanar masa sun riga da sun yanke shawarar hada auransa da khairat yayi niyyar musawa amma mahaifinsa ya nuna masa umarni yabashi ba shawarar sa yake nema ba.

Ta bangaran khairat kuwa da mahaifanta suka sanar mata jitayi kamar taxuba ruwa a kasa tasha duk da alokacin bata kammala karatun taba amma hakan bai dameta ba domin tafi bukatar xama da masoyinta akan karatun.

Abinda yafi daga mata hankali shine yadda yaya sadeeq ke wulakanta ta agaban kowaye bb ruwansa da komai a gaban mahaifansu ne kawai yake nuna mata kulawa, haka kurum xai kirata a waya yayi mata baraxana da cewar intayi kuskuran bari aka aura masa ita saitayi data Sanin abinda tabari akayi, inta fadawa maryam takan bata shawarar ta rabu dashi tunda ai ba ita ta sanya iyayensu hada auranba, kuma intayi kus kuran nuna bataso iyayensu xasuga itace ta bijire musu shikuma yabi umarninsu dan haka kawai ta kyaleshi.

Ana hakane yaxo mata da wannan magana ta auran wata daya kawai xasuyi sbd yabi duk wata hanya data dace yabi yaga bb nasara shiyasa kawai ya yanke wannan hukunci domin yariga da ya shirya abinda xaiyi kafin wata dayan.

 

*a takaice kenan*

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:26 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 4*

 

*ciganan labarin*

 

Khairat da maryam suna isa gida suka iske momcy a parlour harta tashi daga bacci tana waya da dady akan kayan furniture daya tura akawowa khairat daga Dubai.

Sallama sukayi khairat taje ta xauna a kasa kusa momcy ta dora kanta kan cinyarta tana fadin momcy wlh duk nagaji.

Katse wayar momcy tayi tana shafa kanta tana fadin ” kedai khairat raguwace me kikayi da har xaisa ki gaji?

Momcy da kaina nayi driving fah ta fada kamar mai shirin kuka.

Maryam ce ta katsesu tana gaishe da momcy amsawa tayi cikin sakin fuska tana fadin

Ai dama tunda naji khairat shuru nasan gidanku ta biya domin nasan inda na aiketa ya isa ace ta dawo.

Momcy kema kinsan in bataje ta kwasoni ba baxataji dadi ba ta fada tana dry.

Sallamar su sageer da rahama ne suka katsesu sun dawo daga school, rahama ta taho da gudu xata fada jikin momcy khairat tayi saurin kaucewa karta fado kanta tana fadin

”Kekuma haka akeyi kawai ki wani kwaso aguje kina shirin buge mutane ta fada ta galla mata harara

Maryam ce tace

Haba khairat ai kema kinsan wajantane tunda itace auta ba kema.

Fada matadai momcy tace tana kollon autar tata data fara digar da kwalla tace.

Sorry autata waya tabamin ke ne?

Khairat bata jira amsarsuba ta miki taja hannun khairat suka wuce dakinta.

Suna shiga toilet suka nufa sukayi alwala sukayi sallah.

Suna idar wa khairat tajawo wayart tana fadin barina kira Aisha yau kwana biyu kenan bataxoba kuma bata kirani ba.

Uhm wata kila kin mata laifine maryam ta fada tana kokarin cire hijab dinda tayi sallah.

Ringing 2 Aisha ta amsa wayar khairat cike da shagawaba take fadin haba sis dama xaki iya 2 days batareda kinji lpy ta ko kin ganniba?

Kwafa Aisha tayi tace

”Eh mana tunda gashi kema tunda akasa bikinku da yaya kika daina xuwa wajena ko wajan hajiya ma bakya xuwa.

Haba sis kema kinsan haka kurum baxanki xuwaba wlh kunyar hajiya nakeji.

Daga maryam har Aisha dry sukayi Aisha tace

”Chab khairat yau kece kike kunyar hajiya,?

Eh mana wlh banaso mu hada ido da ita dan Allah kiyi hkr gobe kixo kinji

Toh Allah ya kaimu wai ina maryam ne mun kwana 2 bamuyi waya da ita ba?

Wlh gatanan tana jinki khairat ta fada tana mikawa maryam wayar.

Suna gama wayar suka xauna suka fara tsara yadda komai nasu xai wakana batareda ansamu matsala ba, sai wajan karfe 5:00 khairat ta raka maryam gida.

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:26 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 5*

 

 

Shirye shirye biki ake ta kowana bangare inda ta kama yau ne xa’ayi kamu, tun ranar da sadeeq yaxo ya sanarwa khairat cewa auran wata daya ne xai kasance a tsakanin su bata sake sashi a idonta ba duk abunda suke bukata maryam ce mai kiransa a waya ta sanar mai, amma ko sau daya bai taba tako kafarsa yaxoba sai dai ya turo musu abokinsa Abdul yakawo musu sakon, bai ragesu da komai ba duk abunda sukace suna bukata toh saiya aiko musu fiye da yadda suka bukata.

Khairat kuwa kullum cikin xullumi take gashi wani mugu mugun son sadeeq ne ke kara ninkuwa a cikin xuciyarta kullum cikin sallah da addu’oi take babu kakkautawa gawata muguwar rama datayi kowa yaganta saiyayi maganar ramar tata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button