AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Tana xuwa gab dashi ya mika hannun sa ya xagayo kugun ta dashi sannan ya jawota ta dawo daf dashi ta yadda tana iya jiyo numfashin sa shima yanajin nata.

Da sauri ta dago ido tana kallonsa, shima kura mata idanu yayi har sai da ta dauke nata idanun,a hankali ya soma magana.

Uhm khairat ko gaisuwa babu???

Bsta bashi amsaba sai kallon mamakin datake binsa dashi tunda take a rayuwar ta bata taba jin ya kira sunan taba sai dai yace mata yarinya,yanxu ne ma yake cemata kanwa.

Ganin taki magana ne ya sanya yace toh ni barina gaishe ki.

Ina kwana???

Kunyar gai suwar tashi taji da sauri tace ina kwana Yaya???

Uhm sai dana roka???

Nanma still bb amsa.

Sai sukur sukur take xata xame jikinta daga nashi,ganin hakane ya sanya ya dada jawota harta hade da jikinsa.

Sai da yayo kasa da Kansa dai dai wuyanta sannan ya soma magana.

Nasan da cewar ban kyauta miki ba akan abinda na aikata miki,duk da nima bansan meyasa na aikata hakan ba, amma…..

Dakatar dashi tayi ta hanya sanya dan yatsanta akan labbansa sannan ta fara magana.

Ni banyi fushi akan abin da kayi min ba dan haka bana bukatar wani bayani naka ko kuma bada hakuri,uhm nama dade da sanin baxaka iya bani hakuri koda kuwa abinda ya faru yafi wannan.

Kallonta yayi yana naxarin ta sannan yace

Idan ba fushi kike dani ba mai yasa kika kaurace min??? yau kwana 4 kenan ban saki a cikin idanuwa na ba,bayan kinsan amanar ki aka bani idan wani Abu ya sameki ni xa’a bincika kuma bayan hakama………

Dakatar dashi takuma yi ta hanyar daga hannun ta alamar ya isa, sannan ta fara magana

Da’ace ka damu da amanata da aka baka da duk hanyar daxaka bi kaga awane hali nake xakayi kokarin binta, shin ko sau daya kataba leka dakina domin kaga wane hali nake ciki???

Shuru yayi ya kasa bata amsa.

Janye jikinta tayi daga rukon dayayi mata sannan taci gaba da magana.

Ya xama dole naci gaba da kaurace maka har xuwa lokacin da xan bar maka gidan ka, ni daxaka taimaka min ma ka sakeni tun a yanxu wlh daka taimaka min, domin daga mari wata rana kuma sai duka.

Jin maganar tata yati tamkar saukar aradu, wani irin sarawa yaji kansa yanayi,gaba daya yama kasa magana kawai binta yake da idanu.

Ganin baida niyyar yin magana ne yasanya tasake cewa

Ni dai koda baxakayi magana na gama yanke hukunci kawai ka sakeni,xan bakka ka yankewa kanka hukunci nan da dare nidai bukata ta kawai ka sawwa kemin wannan jarababbar igiyar auran taka domin nagaji.

Tana kaiwa nan ta fice daga kitchen din ta barshi tsaye kamar mutum mutumi, gaba daya ya kasa gane a wane hali yake ciki, me maganar khairat take nufi???

Me kuma yake damunsa haka???

Bashida amsa kuma bb mai amsa masa wadannan tambayoyi.

Tana fita ta sumu guri kan kujera ta xauna ta dora kafa daya kan daya tana karkada su.

Tana xaune taji fitowar warsa daga kitchen din a hankali ta dago idanunta kasan cewar kofar kitchen din take kallo, a sanyaye ya fito daga kitchen din,ganin ta a falo din ne yasanya ya tsaya ya kura mata idanu kamar maiso yagano wani abu,kauda kanta gefe tayi domin baxata iya jurar kallonsa ba.

Wucewa yayi kai tsaye ya tafi dakinsa

Murmushi tayi mai ciwo tarasa gane wane irin hali sadeeq yake dashi, ita bata fahimci komai ba mai shurun nasa yake nufi???

Ji tayi hawayen na shirin fara xubo mata tayi saurin sanya hannun tana gogewa.

Yana shiga dakin sa ya nemi gefen gado ya xauna,hannun biyu ya sanya yana tallafo fuskar sa, yarasa gane meke damun sa akan khairat a tsukukin lokacin nan gaba daya khairat ce ke yawo a xuciyarsa idan yana office tunanin ta yake,hasali ma tunda ta daina bari su hadu ya kasance baya iya yin bacci kamar yadda ya saba,tunanin ta kawai yakeyi idan ya runtse idanunsa yakan ganota a lokacin da tayi wani Abu daya burgeshi, ajjiyar xuciya ya sauke tabbas yau daya ya fahimci wani abu Wanda da yakasa ganewa.

Mikewa yayi yanufi drawer ya bude ya dauko invitation din bikinsu da khairat, date din ya duba sannan ya lissafa kwana kin gabansa kawai yaji ya fadi, tabbatar gobe saura kwana goma kwana kin daya tsara xai saki khairat xasu cika.

Dafe kansa yayi tabbas yasan cewar kwanaki kadan ya rage ya ciki burinsa na auran tarwatsa auransu da khairat, amma kuma gashi ansamu matsala.

Mikewa yayi yana xageye dakin a fili ya furta “tabbas lokaci yayi daya kamata na daina cuttar da kaina nakuma daina karya ta xuciyata, nakuma daina karya ta wadanda suke fadamin,bb karya a ciki a xahiran ce abun yake xuciyata ta kamu da matsanai cin son khairat.

Ya salam meyasa nayi wannan gangancin????

Why????

Meyasa na yadda har aka daura aurena da khairat???

Meyasa na yadda har muka xauna gida daya da ita???

Why??????

Meyasa nabari xuciyta yasamu kusan ci da ita har nabari halayyar ta da dabi’unta suka tsaya min a rai????

Tunawa yayi da abin da Abdul yake fada masa tun kafin ya auri khairat.

Ya salam????????‍♂
Tabbas ba yanxu nafara son khairat ba.

*Neenat seif????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

*Written by neenat seif????????????????????????????????*

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

Page 25

2 eyes sukayi dashi,yana tsaye a bakin kofa ya jingina fa bango hannayen sa xube cikin aljihun sa,sanye yake da kana nan kaya ya xuba mata idanu.

Kasa tayi da idanunta ta kalli rigar dake jikinta iya gwaiwa ko hannun arxiki bata dashi, shima kallota yayi har kasa kamar yadda yaga tayi murmushi kawai yayi sannan ya tako a hankali ya karaso gab da ita.

Sun kai tsayin mintuna a haka amma ya kasa magana shin hakuri xai bata koko tambayar ta xaiyi dalilin dayasa take boye masa bataso su hadu???

Ganin bashi da niyyar yimata magana ne ya sanya ta tsame hannunta daga abin da takeyi ta rabeshi xata wuce

Tana xuwa gab dashi ya mika hannun sa ya xagayo kugun ta dashi sannan ya jawota ta dawo daf dashi ta yadda tana iya jiyo numfashin sa shima yanajin nata.

Da sauri ta dago ido tana kallonsa, shima kura mata idanu yayi har sai da ta dauke nata idanun,a hankali ya soma magana.

Uhm khairat ko gaisuwa babu???

Bsta bashi amsaba sai kallon mamakin datake binsa dashi tunda take a rayuwar ta bata taba jin ya kira sunan taba sai dai yace mata yarinya,yanxu ne ma yake cemata kanwa.

Ganin taki magana ne ya sanya yace toh ni barina gaishe ki.

Ina kwana???

Kunyar gai suwar tashi taji da sauri tace ina kwana Yaya???

Uhm sai dana roka???

Nanma still bb amsa.

Sai sukur sukur take xata xame jikinta daga nashi,ganin hakane ya sanya ya dada jawota harta hade da jikinsa.

Sai da yayo kasa da Kansa dai dai wuyanta sannan ya soma magana.

Nasan da cewar ban kyauta miki ba akan abinda na aikata miki,duk da nima bansan meyasa na aikata hakan ba, amma…..

Dakatar dashi tayi ta hanya sanya dan yatsanta akan labbansa sannan ta fara magana.

Ni banyi fushi akan abin da kayi min ba dan haka bana bukatar wani bayani naka ko kuma bada hakuri,uhm nama dade da sanin baxaka iya bani hakuri koda kuwa abinda ya faru yafi wannan.

Kallonta yayi yana naxarin ta sannan yace

Idan ba fushi kike dani ba mai yasa kika kaurace min??? yau kwana 4 kenan ban saki a cikin idanuwa na ba,bayan kinsan amanar ki aka bani idan wani Abu ya sameki ni xa’a bincika kuma bayan hakama………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button