AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

 

Dakatar dashi takuma yi ta hanyar daga hannun ta alamar ya isa, sannan ta fara magana

Da’ace ka damu da amanata da aka baka da duk hanyar daxaka bi kaga awane hali nake xakayi kokarin binta, shin ko sau daya kataba leka dakina domin kaga wane hali nake ciki???

Shuru yayi ya kasa bata amsa.

Janye jikinta tayi daga rukon dayayi mata sannan taci gaba da magana.

Ya xama dole naci gaba da kaurace maka har xuwa lokacin da xan bar maka gidan ka, ni daxaka taimaka min ma ka sakeni tun a yanxu wlh daka taimaka min, domin daga mari wata rana kuma sai duka.

Jin maganar tata yati tamkar saukar aradu, wani irin sarawa yaji kansa yanayi,gaba daya yama kasa magana kawai binta yake da idanu.

Ganin baida niyyar yin magana ne yasanya tasake cewa

 

Ni dai koda baxakayi magana na gama yanke hukunci kawai ka sakeni,xan bakka ka yankewa kanka hukunci nan da dare nidai bukata ta kawai ka sawwa kemin wannan jarababbar igiyar auran taka domin nagaji.

 

Tana kaiwa nan ta fice daga kitchen din ta barshi tsaye kamar mutum mutumi, gaba daya ya kasa gane a wane hali yake ciki, me maganar khairat take nufi???

Me kuma yake damunsa haka???

Bashida amsa kuma bb mai amsa masa wadannan tambayoyi.

 

Tana fita ta sumu guri kan kujera ta xauna ta dora kafa daya kan daya tana karkada su.

Tana xaune taji fitowar warsa daga kitchen din a hankali ta dago idanunta kasan cewar kofar kitchen din take kallo, a sanyaye ya fito daga kitchen din,ganin ta a falo din ne yasanya ya tsaya ya kura mata idanu kamar maiso yagano wani abu,kauda kanta gefe tayi domin baxata iya jurar kallonsa ba.

 

Wucewa yayi kai tsaye ya tafi dakinsa

 

Murmushi tayi mai ciwo tarasa gane wane irin hali sadeeq yake dashi, ita bata fahimci komai ba mai shurun nasa yake nufi???

Ji tayi hawayen na shirin fara xubo mata tayi saurin sanya hannun tana gogewa.

Yana shiga dakin sa ya nemi gefen gado ya xauna,hannun biyu ya sanya yana tallafo fuskar sa, yarasa gane meke damun sa akan khairat a tsukukin lokacin nan gaba daya khairat ce ke yawo a xuciyarsa idan yana office tunanin ta yake,hasali ma tunda ta daina bari su hadu ya kasance baya iya yin bacci kamar yadda ya saba,tunanin ta kawai yakeyi idan ya runtse idanunsa yakan ganota a lokacin da tayi wani Abu daya burgeshi, ajjiyar xuciya ya sauke tabbas yau daya ya fahimci wani abu Wanda da yakasa ganewa.

 

Mikewa yayi yanufi drawer ya bude ya dauko invitation din bikinsu da khairat, date din ya duba sannan ya lissafa kwana kin gabansa kawai yaji ya fadi, tabbatar gobe saura kwana goma kwana kin daya tsara xai saki khairat xasu cika.

 

Dafe kansa yayi tabbas yasan cewar kwanaki kadan ya rage ya ciki burinsa na auran tarwatsa auransu da khairat, amma kuma gashi ansamu matsala.

Mikewa yayi yana xageye dakin a fili ya furta “tabbas lokaci yayi daya kamata na daina cuttar da kaina nakuma daina karya ta xuciyata, nakuma daina karya ta wadanda suke fadamin,bb karya a ciki a xahiran ce abun yake xuciyata ta kamu da matsanai cin son khairat.

Ya salam meyasa nayi wannan gangancin????

Why????

Meyasa na yadda har aka daura aurena da khairat???

Meyasa na yadda har muka xauna gida daya da ita???

Why??????

 

Meyasa nabari xuciyta yasamu kusan ci da ita har nabari halayyar ta da dabi’unta suka tsaya min a rai????

 

Tunawa yayi da abin da Abdul yake fada masa tun kafin ya auri khairat.

 

Ya salam????????‍♂
Tabbas ba yanxu nafara son khairat ba.

 

 

 

 

 

*Neenat seif????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat seif????????????????????????????????*

 

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 26*

 

 

 

“Haka yayi ta xarya a dakin har xuwa lokacin da aka fara shirin tafiya masallaci,ruwa ya shiga ya watsa sannan ya shirya cikin manya kaya ya fito da niyyar tafiya masallaci.

 

Turus kawai ya tsaya lokacin daya sakkk falon kasan.

Yanda ya barta tun daxu haka yanxuma ya sameta, da alama ko wanke wanke bata shiga ta karasa ba,jin motsin sane ya Santa ta dago ta kalleshi, shima itan yake kallo wata uwar harara ta watsa masa sannan ta kauda kanta, harga Allah haushin sa takeji sbd tana ganin ya raina mata hankali tana yimasa magana amma ya maida ita tababbiya ko kulata baiyi ba bai kuma bata amsar maganar datayi masa ba.

Karka da kansa kawai yayi sannan yaxo ya wuce ta yabar gidan.

Yana fita tayi kwafa ta tashi tashiga kitchen din ta karasa gyara wa, tana kammalawa ta dora girki, duk da taga yawanci kayan amfanin nasu ya kare haka ta duba Wanda ya samu ta dora domin ita dai baxata yimasa magana ba, saida ta tabbatar tagama hada komai sannan ta kwashe takai dining sannan ta ajje na baba mai gadi sbd tasan yanxu ya tafi masallaci.

Tana kammala komai ta wuce dakinta tayi wanka tayi sallah sannan ta kimtsa kanta cikin wata rantsatstsiyar atamfa, tana gamawa ta feshe jikinta da turare ta sakko falon ta xauna.

Ta window ta leka ta hango baba mai gadi ya dawo,hijab ta sanya taje ta mika masa abincin sannan ta dawo ta kunna TV.

 

Bata wani jima da xama ba ya shigo tareda sallama, a sanyaye ta amsa masa wannan karon fuskar ta Bb yabo ba falla sa, kallonta kawai yake duk cikar data tana batsewa hakan bai hana kyawunta fitowa sbd dama mai kyau ce.

Sun kai kusan 30mins a haka bb Wanda yayiwa dan uwansa magana,wata muguwar yunwa yakeji kasan cewar ko break fast baiyi ba,yana da tabbacin ba samun abin ci xaiyi a gidan ba,yasan baxata girka ba tunawa yayi jiya ya shiga ya dora tea yaga duk kayan abincin nasu ya kare dan haka ma baisa rai ba, mike wa yayi ya nufi dakin sa da niyyar shirya wa ya fita yasiyo abinci.

 

Tana gani ya tashi ya hau sama ta mike taje gaban dining din tafara xuba abinci.

Yana sakkowa falon gafara jiyo kamshin abincin nata, yawu ya hadiya a ransa yace yau kuma kwalele xa’ayi mana.

Ko kallon inda take beyiba yanufi kofar falon da niyyar fita.

 

“Yaya ka tsaya kaci abinci”

 

Tsayawa yayi cak sannan ya juyo ya kalleta hannun ta dauke da plet din abincin.

Murmushi yayi mata yace uhm dakin bar shima yanxuma fita xanyi na siyo.

 

Uhm baxan cemaka karka fita ka siyo ba amma idan kana ganin fita ka siyo din xaifi muhimmanci xaka iya tafiya saina bawa mai gadi ya mikawa almajiri kawai, dama banayi danna burge ka bane bare naji haushi dan kaki ci.

 

Tana gama fada ta dauki plet daya ta dawo tsakiyar falon ta xauna tafara ci.

 

Saida ya jima tsaye a gurin sannan ya dawo falon ya wuce dining din ya dauko abincin shima ya ajje kamar yadda tayi ya yafara ci.

Dagowa tayi kawai tana kallonsa ta karkada kai taci gaba da cin abincin ta.

Suna kammalawa ta tashi ta ‘kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta wuce d’akinta.

Bayan sallar magrib tana xaune a falon sama tana latsa wayarta sadeeq yashigi lokacin ya dawo daga masallaci, wuce ta yayi ya shiga d’akinsa mintuna kadan ya fito hannunsa ri’ke da key d’in mota, yana xuwa gab da ita ya tsaya, sai da yajima tsaye a wajan sannan ya kira sunan ta

“Khairat”

Ko kallonsa batayiba tafara magana “ina fatan dai sallama ta kaxoyi saboda naga lokaci yayi dama xuwa magrib nace maka.

Tsugunnawa yayi ya dafa kojerar da hannunsa ya ‘kura mata idanu yana nazarin ta uhm wai har yaushe khairat ta koma haka??? Wane abu na aikata mata a zamana da ita wanda ya goge soyayyar da take yimin??? Uhm amma nasan mezan yimata sbd nasan baxata taba daina sona ba sai dai ace yadan ragu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button