AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

” haba khairat meyasa kike fadin wannan maganar?? “Sanin kanki kine idan na sake ki a yanxu xan iya samun matsala daga mahaifa na, ” kinfi kowa sanin bana ‘kaunar wannan xaman da muke da ke basai wani ya fada miki ba ni banta’ba cewa ina sonki ba iyayan mu ne suka hada wannan aure batare da jin ta bakina ba shin ina sonki ko akasin haka.

‘Karashe maganar yayi yana nazarin ta domin ya fahimci awane mizani zata sanya maganar tashi

Sai a lokacin ta d’ago idanunta ta kalleshi ji tayi xuciyarta na wani irin bugawa wani ‘bacin rai taji na maganar tashi, da xata maida mai da ba’kar magana ne amma saita fasa bataso ya fahimci har yanxu tana sonshi hasalima ko ‘kwarzane bai ragu a zuciyar ta ba indai na soyayyar sadeeq ne kullum karuwa yake.

Murmushi yayi saboda ko bata bashi amsa ba ya fahimci abinda yakeso ya sani, “bakice komai ba kawai kin ‘kura min idanu, kauda kanta tayi sannan ta ce ” shikenan naji ai 11days kamar gobe ne.

“Haka ne Allah ya kaimu”

“Ameen”

“Idan babu damuwa ki sako mayafinki xamuje anguwa”

“Uhm kaje ban xuwa nidai”

“Haba kanwa kar muyi haka dake yi hkr ki tashi mu tafi kinji”

Tunawa tayi ko gidan su zai kaita da sauri ta mike ta shiga daki ta sauya kaya ta fito ta sameshi inda ta barshi.

“Yaya nagama shiryawa da fara’arta tayi maganar, kallon ta yayi saita bashi tausayi saboda ya fahimci tayi tunanin gidansu xai kaita shiyasa ta saki ranta harda fara’ar ta.

” toh muje ”

Tare suka jera har xuwa wajan motors din suka shiga mai gadi ya bud’e musu gate suka fice daga gidan…

 

 

*Neenat seif????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????

AURAN WATA DAYA

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat seif (Peenah pinkly)????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 27*

 

Suna fita ya mi’ki titi suka fara tafiya, ganin ba hanya gidansu ya dauka bane ya sanya khairat ta d’ago idanunta tana kallonsa, yana sane da kallon sa da takeyi amma ya’ki ya waiga ya nuna baisan ma tanayi.

“Yaya ina xamuje???”

“Uhm ‘kya bari muje ai sai idanun ki su gane miki”

“Amma ai ya kamata……”

“Kin san dai baxan sai dake ba,ko kuma na kaiki inda bai dace ba” ya katseta da fadin haka.

Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake magana ba har xuwa lokacin da taga yayi parking motar a wani kata faren store.

Bude motar yayi ya fito sannan ya xagayo ya bude mata kofa yana fad’in “fito muje”

“Uhm kawai kaje ni xan jiraka anan”

Kasa yayo da kansa dai dai face d’inta yace “haba kanwata kayan abinci fa kawai zamu siyo naga bamuda komai kuma kinsan ni bansan list din abinda mukeda bukata”

“Nifa banida bu……”

Yatsansa daya ya d’ora kan lips dinta sannan yafa magana kasa kasa “haba khairat ‘kinsan banason musu dan Allah kiyi hkr ki fito muje kinji plsssss”

Dariya yaso ya bata ganin yadda ya marairai ce, “shikenan muje”

Tare suka shiga store din suka d’iba duk wani abu dasuke bukata, suka biya kud’in aka kawo musu kayan aka zuba a but din motar sannan suka shuga suka d’au titi.

Ji tayi kamar tace masa ya kaita gida tunda dare beyiba lokacin suna store akayi sallar ishsha’i, ganin hankali sa ba’a kanta yake ba ya sanya itama ta shareshe ta d’auko wayar ta kunna data ta fara karatun novel batare da tasake dago idonta ta kalli hanyar da suke d’auka ba.

Suna isa yayi parking motar a kofar gate din gidan sannan ya d’ago ya kalleta har lokacin hankalin ta yanakan wayar ta.

“Uhm munxo ki tashi ki shiga ciki, ni zanje na dawo amma ba dad’ew zanyi ba”

Rufe wayar tayi sannan tace “toh shikenan saika dawo” ta bude motar ta fito.

Sai a lokacin ta kula da inda suke, wani farin ciki taji ya ziyarce ta, da sauri ta juyo ta kalleshi lokacin da yake bude motar yana fitowa.

“Wow amma Yaya naji dadi wlh kamar kasan yadda nake kewar Momcy da dady”

“Kara sowa yayi inda take tsaye ya fuskan ceta kana yasoma magana.

“Kamar yadda nayi tsammani zakiyi farin ciki matukar na kawoki gidan danku gashi kuwa kinyi duk da baki wani jima da ganin su ba, nasan da cewar na bata miki kuma bansan wane abu zanyi miki Wanda zaisa ki rage jin zafin abinda nayi miki ba,shiyasa na kawoki gidan Ku a lokacin bai kamata ace na dauki hannu harna mareki ba,ko babu komai ke amana ce a wajena,na 2 kuma kina jin haushin nayi miki ba dai2 ba amma na gaxa baki hkr, bawai ha’kuri ne bazan iya baki ba, kamar yadda kika fada min d’azu ba,kawai bansan wace Kalmar zan furta miki ba ne”

Ta ‘kosa ta shiga gidan shiyasa tace “karka damu yaya ai ya wuce”

“Shikenan amma dan Allah inki shiga ciki kar…..

” nasan abinda zaka fada,in dai nice karka damu babu Wanda zan fadawa wani abu”

Murmushi yayi ganin harta fahimci abinda zai fad’a mata “toh ki shiga saina dawo zan shigo”

Bata bashi amsaba ta juya tanufi gidan shi kuma ya bud’e motar ta shiga ya tafi.

Da sallama ta shuga falon babu kowa aciki sai kayan kallo da suke aiki a falon,dakin Momcy ta nufa, tana gab da shiga saiga dady ya fito shida rahama. Rahama na ganin ta ta saki hannu Dady da gudu ta taho ta rungume khairat.

“Aunty dama zakizo amma Momcy bata fadamin ba??”

“Ai ban fada mata zanxo ba shiyasa bata fada miki ba”

Dady ne ya karaso yana murmushi
“mamana kece a gidan???

” Dady ina wuni???”

“Lpy qalau, ina sadeeq din yabar ki ke daya da daren nan haka??”

“Ah ai tare muke dashi ya d’an je wani wajene yanxu zai dawo”

“Owk”

Sm”shiga kiyi mata magana nasan batasan da zuwanki ba”

“Toh Dady” ta fada ta fara tafiya,rahama ce ta bita da gudu, Dady ne ya juyo yana fadin “yanxu sbd kinga yar uwarki shiyasa kika fasa tayani kallon news d’in??”

“Uhm nidai Dady na fasa”

“Toh ai shikenan” ya fad’a yana tafiya, khairat na dariya ta shiga dakin Momcy.

A d’akin suka sameta tana gyara kayan da aka kawo mata daga wajan guga.

Momcy taji dadin ganin khairat sosai, nan ta tayata suka gyara kayan, sannan suka dawo falon,lokacin khairat ke tambayar ina sageer, Momcy ta sanar mata yana gidansu sadeeq, tashi tayi sbd batayi salla ba,tana idarwa Momcy ta xubo mata abinci taci, nan suka zauna firar yaushe gamo tunda wancan zuwan basu jima ba,shidai dady tashi yayi yabasu guri.

Kwata2 khairat bata bari Momcy ta fahimci komai tsakanin ta da sadeeq ba.

Sai wajan 10:00 sadeeq ya dawo, sun gaisa da Momcy da Dady a gurguje sbd dare yayi, sadeeq ne ya fara tafiya sannan khairat harta fita ta dawo tacewa Momcy ta xuba mata abinci a kula saboda tasan sadeeq baici abinci ba.

Tunda suka dau hanya khairat takejin wani mugun bacci,ganin idanunta sai lumshewa suke ya sanya ta kwantar da kujerarta ta kwanta bata jimaba bacci ya kwasheta.

Suna isa gida yayi parking motar ya jiyo xai yimata magana, tsayawa kawai yayi yana kallon ta shidai yaga lokacin da ta kwantar da kujerar ta amma baisan bacci tayiba,yayi tunanin ko xaman kujerar ne beyi mata dad’iba ta gyara.

Rasa yadda zaiyi ya tashe ta yayi kawai ya tsaya ya ‘kura mata idanu,wani irin kyau yaga tayi masa a hankali ya sauke wata ajjiyar xuciya ya maida idanunsa kan lips dinta,yanason sanya light pink din lipstick shi kuma hakan ba karamin tafiya yake dashiba, ji yake kamar yayi kissing lips din nata amma baxai iya,sai a yanxu ya dada tabbatar wa da Kansan yayi nisa akan son khairat shiyasa komai nata yake burgeshi, tun yana kasar waje yake ganin mata Kala2 amma bai taba ganin macen da komai tayi kyau yake mata ba kamar khairat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button