AURAN WATA DAYA

Gabansa ne ya fadi tunawa dayayi kwanaki kad’an ya rage wata daya ya cika,wata xufa yaji ta fara karyo masa, bai sani ba ko khairat xata matsa masa akan ya saketa haka xalika bai saniba ko xata iya hakuri kawai suci gaba da xamansu tunda dama aure sukayi wanda kowa ya shaida shi su biyune kawai suka san da maganar daga baya zai saketa sai kuma Abdul.
Jingina Kansa yayi jikin kujerar yana ayyana abubuwa da dama a xuciyarsa….
*Neenat seif (Peenah pinkly)????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat seif????????????????????????????????*
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
*Page 28*
Tunda ya jingina kansa a jikin motar yaji wani irin yanayi yana shigarsa, gaba daya komai nashi ya sauya a hankali ya dago Kansa, dai dai lokacin khairat dake bacci ta bude idanunta a hankali da sauri ta mi’ke tana fad’in “yaya ashe mun iso gida amma baka tashenj ba”
“Uhm” kawai yace mata ya bude motar ya fito,itama fitowa tayi,sannan ya rufe motar suka wace cikin gidan.
Kai tsaye khairat ta wuce d’akinta bata jira komai ba ta cire kayanta ta sanya na bacci, sai data kashe wayar ta sannan ta kwanta, da sauri ta mike tunawa da tayi da abincin da ta tahowa sadeeq dashi.
A falon ta sameshi ya kwata akan kujera Kansa yana kallon sama, da mamaki ta karasa kusa dashi tana fad’in “Yaya lafiya naga baka shiga d’aki ba?? Kuma naga kamar kanada damuwa”
Jiyowa yayi ya kalleta da sauri ya d’auke Kansa yace “Uhm babu komai khairat”
Har cikin xuciyarta bata yarda ba amma saita share maganar tace “Yaya na manta da abincin ka fa a mota wanda na taho dashi daga gida”
“Na koshi”
“Haba Yaya kar muyi haka da kai nasan bakaci abinci ba gashi dare yayi yanxu banaso ka ‘kwana a haka”
Bai sake cemata komai ba ya tashi ya fita, ita kuwa guri ta samu ta xauna tanajin wani iri a xuciyarta game da yadda taga damuwa ‘baro2 a fuskar sadeeq.
Bai jima da fita ba ya dawo hannu sa ri’ke da kular abincin,tashi tayi ta amsa kulan ta ajje sannan ta nufi kitchen, bin bayan ta yayi yana kallon ta da ace tasan meyake damunsa da bata fito da kayan bacci a jikinta ba.
Hannun ta d’auke da plet ta fito ta ajje gaban sa ta zuba abinci tace “Yaya gashi”
Sakkowa yayi daga kan kujerar ya xauna a kan carpet d’in dake falon ya fara cin abincin, kasa tashi khairat tayi lafiya qalau suka taho daga can gida amma yanxu gaba daya ya sauya batasan meyake damunsa ba kuma batajin zai iya fad’a mata, ita kuma baxata juri ganin sa a haka ba har cikin xuciyarta takejin babu dad’i na ganinsa haka.
Kwata2 baici abinci da yawa ba ya miko mata yace ya koshi, kar’ba tayi ta hada da kular ta kai kitchen, sannan ta dawo falon,yana xaune inda yaci abincin ya dora Kansa jikin kujerar idanunsa a lumshe, karaso wa tayi gab dashi ta zauna a hankali ta furta “Yaya”
Bai amsa ba sai bude idanunsa kawai yayi, “dan Allah ka fad’amin meyake damunka jikina yana bani kamar ni nayi maka wani abu na laifi”
“Uhm babu abinda kikayi min banajin dadi ne kawai shiyasa, ya kamata ma kije ki kwanta 12:15 fa yanxu” ya nuna mata agogon dake manne a bangon falon.
“Allah ya baka lpy”
Tana fad’a ta mike ta shige d’aki ba tare da ta sake kallon sa ba.
Yajima zaune a wajan ba tare da ya koma d’akiba, sai da yaji wani irin sanyi na shigar sa alamun zazza’bi neman kamashi sannan ya tashi ya tafi daki.
Washe gari saida khairat taci baccin ta sannan ta fito falon wajan karfe 10:00 kasan cewar yau weekend.
Kitchen taso ta shiga ta had’a musu breakfast amma saita tuna basu shigo da kayan da suka siyo ba, don haka saita fara gyara gidan kafin sadeeq ya fito su kwaso kayan sai tayi girkin.
Harta gama shuru babu alamar sadeeq zama tayi a falon sama tana jiran sa kusan 1hrs tana zaune amma shuru, gashi ta fara jin yunwa,yanke shawarar xuwa ta tasoshi tayi domin ta gaji.
Kai tsaye ta bud’e kofar ta shiga kwance yake a tsakiyar gado ya lullu’ba da wani katon bargo.
Mamaki abin ya bata saboda ita dai tasan ba sanyi ake yiba,karasa wa tayi ta janye bargon a ‘kudundune ta ganshi fuskar sa tayi fayau da ita,da sauri ta furta ” yaya bakada lpy ne??”
Bai bata amsa ba sai bud’e idanunsa yayi ya sake rufesu, da sauri ta zauna bakin gadon ta sanya hannun ta dafa goshin sa da sauri ta d’auke hannun ta jin zafi dau a goshin.
Da sauri ta sanya hannu ta d’agoshi tana fad’in ka tashi mu tafi hospital bakaji yanda jikinka yayi zafi sosai ba.
A hankali ya janye hannun ta daga jikinsa ya jingina da filo sannan yace ” ba sai munje hospital ba barina kira wani doctor daga hospital d’inmu saiya dubani.
“Toh” kawai tace masa, wayar dake kusa dashi ya dauka ya nemo number da yake nema sannan ya kara a kunnen sa.
Sai da suka gama gaisawa sannan yace heesham inaso kazo gida ka duba ni ne tun jiya banida lpy.
“Owk bani 30mns ganinan zuwa,
” owk” kawai yace ya kashe wayar sa.
Sun dad’e a zaune batare da ya kuma cemata komai ba sannan itama bata tashiba.
Can wayar sa ta fara ruri yana dagawa yace “owk” ya kashe wayar kana ya kalli khairat kayan bacci ne a jikinta bata sauya kaya ba, “kije ki dauki hijab ki sanya saiki shigo da doctor heesham banajin zan iya sauka ‘kasa”
Bata bashi amsa ba ta fita, zuwa can sai gasu tare da doctor heesham, suna shigowa ko zama bata yiba ta fice daga d’akin ta koma falo.
Sai da heesham ya gama duba sadeeq sannan yace “doctor sadeeq basai na fada maka abin da yake damunka ba, abin mamaki kai da kake yiwa mutane fad’a akan su daina sanya damuwa a zuciyarsu saboda sanin illar da hakan ke haifar wa amma sai gashi kai da kanka kana neman illata kanka ta hanyar sanya wa kanka damuwa”
Ajjiyar zuciya sadeeq ya sauke sannan yace ” tabbas maganar ka haka take amma inaso ka sanani malami ne zakaga yana fad’akar wa akan wani abu Wanda shi kanshi yana aikata wa, just kawai inaso ka fahimci ita damuwa tana zuwa ma d’an adam ne bashi yake kiran ta da Kansa ba.”
“Hakane amma dan Allah ka kiyaye, nasan kasan mugun gunan da kake bukata sbd haka zaka iya turawa a siyo maka saboda babu a hospital d’in mu bare nasa a kawo maka amma kafin lokacin ka nemi maganin da zai saukar maka da zazzabin nan tukkunna.
” shikenan heesham na gode sosai ”
“Babu damuwa”
Doctor heesham na fita ta shigo tana fad’in “sannu yaya ko kana da bu’katar wani abu??”
“tea kawai zaki hado min amma kar kisamin madara”
“Owk barina je na hado maka”
Mintuna kadan ta kammala sai kwai data soya masa ta kawo masa, yana kammalawa yace ta mi’ko masa wani karamin box, karasawa wajan tayi ta d’auko ta kawo masa,yana budewa taga Ashe magunguna ne aciki, ruwa yasa ta miko masa yasha sannan yace ta hada masa ruwan wanka.
*Neenat seif (Peenah pinkly)????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat seif????????????????????????????????*
*Dedicated to ASHANTY(CAKUS) FATEEMA BUKAR KHDEEJA YALLILO MAMAN KHALEEFA SUNNA SAK tare da dukkan fans na AURAN WATA D’AYA ana tare????????*
*Page 29*
Ruwan da ya watsa a jikinsa ne ya sanya yad’an ji ‘kwari, shiryawa yayi cikin wani d’anye boyel ya fito.