AURAN WATA DAYA

A falo ya sameta tayi tagumi,gaba d’aya ta manta da wani batun yunwar data soma ji d’azu,tun tana gida idan taga wani bashi da lafiya nan danan hankalin ta zai tashi ta kasa samun sukuni bare kuma yanxu da shashin xuciyarta ne babu lafiya????
Zama yayi kusa da ita da sauri tace “haba yaya in wani abu kakeso kayimin magana mana kana sane baka da lpy fah”
Murmushin yayi saboda yaji dad’in maganar ta ko babu komai ta nuna damuwar ta a kansa, “kar ki damu dama zazza’bin ne ya hanani fitowa amma yanxu dana sha magani na watsa ruwa naji yad’an sauka”
“Toh Allah ya kara baka lafiya”
“Ameen”
Kallon taya yayi sannan yace “tashi ki shirya zaki rakani anguwa”
Sakin baki tayi tana kallon sa
“Yes anguwa zaki rakani”
“Hmmm kaida bakada lpy”
“Na sani tashi ki shirya”
“Toh amma fa kasan banyi wanka ba”
“Karki wani damu zan jiraki”
“Toh shikenan”
Bata dad’e sosai ba ta fito ta gama shiryawa tsaf,fita sukayi kai tsaye suka nufi wata motar bata jiya ba saboda ko kayan da suka siyo basu ‘kwashe ba.
Ma zaunin driver ya bude yana yimata nuni da tazo ta shiga, no’kewa tayi,da sauri ya bata face yace “bafa wasa nake miki ba”
Bata musa masa ba tazo ta shige shi kuma ya zauna a mazaunin mai zaman banza ta tada motar suka fice daga gidan.
Shiya nuna mata hanyar da zasubi har xuwa wani kata faren chemist tana parking d’in motar ya fita ya shiga wajan, mintuna kad’an ya fito ya gama siyo magun gunan da yake da bu’kata,motar ya shiga yace taja su tafi.
“Gida zamuje?”
“A’a”
Bata sake magana ba taja motar suka tafi,wanna karon ma shiya nuna mata hanyar da zatabi har suka isa wani gidan abinci sannan yace ta tsaya, jiyowa tayi tace “me zamuyi a gidan abinci kuma?”
“Saboda kinajin yunwa”
“Nina fad’a maka haka?”
“A’a amma kinsan ina sane da cewar bakiyi break fast ba kuma gashi yanxu karfe d’aya saura”
“Hakane amma ka barshi idan munje gida saina girka”
“Karki damu barina siya mana kawai” yana gama fad’a ya bude motar ya fita,yana fara tafiya taga ya tsaya ya dafe kansa, da sauri ta bud’e motar ta xagayo ta rikeshi tana fad’in “maiya faru yaya badai ciwon kan bane??”
Ganin baxai bata amsa bane yasanya ta taimaka masa ya koma cikin motar sannan itama ta shiga zata tada motar.
Da sauri ya ri’ke hannun ta ya ciro kud’i a aljihun sa ya mika mata “jeki siyo mana abincin”
Zatayi magana ya dakatar da ita, kar’ba tayi ta fice daga motar tashiga gurin abincin,takeaway 3 tayo sannan ta fito ta suka tafi.
Tun daga bakin gate ta ciro takeaway d’aya ta bawa baba mai gadi, suna shiga falo ta nufi kitchen ta dauko musu plet tazo ta ajje, kaya sadeeq yakeso ya sauya amma kuma bayajin zai iya taka steps d’in saboda haka ya fad’awa khairat, tashi tayi taje dakin sa ta dauki mas kaya marasa nauyi ta kawo masa sannan ta shige kitchen domin yasamu damar sakawa.
Saida ta tabbatar zuwa lokacin ya sanya sannan ta fito,samun shi tayi harya gama sakawa yana jiranta,’karasawa tayi ta zuba musu abincin suka ci,bai wani ci abincin da yawa ba yasha magani.
******************************
Yau Abdul ya tashi da niyyar zuwa gidansu maryam, don haka tun magariba ya shiraya yana yin sallar ishsha’i ya shiga motar sa sai gidan su maryam.
Yana zuwa gidan ya kirata ya shaida mata, kanin ta ta turo yayi masa ido zuwa d’akin ba’ki, saida ta gama shiryawa sannan ta nufi d’akin ba’kin, da sallama d’auke a bakinta ta shiga d’akin cike da nutsuwa.
Amsa mata yayi sannan ta samu d’aya daga cikin kujerun ta zauna ta gaishe da shi ya amsa,kusan 5mns babu wanda ya kuma magana a cikin su, xuwa can Abdul ya nisa yace. “Da farko dai basai nayi miki bayani akan waye ni ba kin sanin kinsan iyayena da kuma duk wani abu daya kamata ki sani a kaina.
” ko ban fad’a miki ba nasan kinsan abinda yakawo wajanki ina fatan wani bai rigani”
Murmushi tayi saboda ita maganar ma dariya taso ta bata.
“Bayan haka ni a yanzu banida wani buri daya wuce ace kin amince dani sannan ki soni kamar yadda nake sonki,maryam na jima ina sonki sanar mikine kawai banyi ba sai yanzu saboda kar naci gaba da yin sake wani yazo ya kwace min ke,amma idan bakiyi na’am dani ba karki boyemin ki sanar dani.
Murmushin tayi sannan tace ” sanin kanka ne duk macen da tace bata sonka ta fad’a ne saboda tasan dama baxata sameka ba,baka da makusa ka hadu duk wani abu da mace take bukatar namiji ya kasan ce dashi nasaba, ilimi, kyau, uwa uba kanada aikin yi,saboda haka babu abinda zance sai dai Allah ya tabbatar mana da alkairi.
“Ameen ameen” ya fad’a yana mai jin dad’in kalaman ta, nan dai suka sha firarsu ta masoya sannan Abdul ya tashi ya tafi, maryam na shiga gida ta sanarwa hajiya yadda sukayi, hajiya taji dad’i sosai a ranta sannan tayi musu addu’a.
*Neenat seif (Peenah pinkly)????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA DAYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat seif????????????????????????????????*b
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
*Page 30*
Tun daga wannan lokacin soyayya ta d’in ke tsakanin Abdul da Maryam soyayyar su sukesha basuda wata matsala.
*****************************
Kulawa sosai Khairat ke bawa Sadeeq saboda wani irin mugun ciwon kai dayake zuwa masa lokaci zuwa lokaci,wani mugu mugun tausayin sa da ‘kaunar sa takeji a ranta, tayi tayi dashi akan a fad’awa su Momy da dad amma fur yaki.
Ya riga da yasan abin da ke samasa wanna ciwon kan,yawan tunanin da yakeyi ne ya sanya kansa yake sarawa a duk lokacin da ya matsawa kansa da tunani ga wani zafi da xuciyarsa ke yimasa, gashi doctor amma bayason shan magani ko a hospital idan time na shan maganin marasa lpy yayi zaije ya basu amma idan zasusha juyawa yakeyi baya ‘kaunar ya kalla.
Khairat ce zaune a falo tana jere kayan break fast d’in su s kan Capet saboda yanzu Sadeeq baison zaman dining, sai da ta gama kammala komai sannan ta shiga d’akinsa zata kirawo shi.
A bakin mirro ta sameshi yana feshe jikinsa da turare da alama wanka ya fito yake shiryawa,’karasawa tayi kusa dashi ta gaishe shi ya amsa, ta kalleshi tace
“Amma ko kayimin magana nazo na had’a maka ruwan wanka shine ka hada da kanka bayan kasan baka da lpy”
“Karki damu naji sau’ki yau jikin nawa garau nake jinsa”
“Uhm kai dai kace bakaso na samu lada”
“Ladan me zaki samu?”
“Ladan had’awa mijina ruwan wanka mana, ko ka manta duk abinda mace tayiwa mijin ta lada take samu matu’kar yaji dad’insa?”
Jiyowa yayi yana kallonta, da sauri tace
“Sorry Yaya wasafa nake maka yayana xance nace miji”
Juyawa yayi batare da ya sake kallonta ba, ita kuwa ‘kwafa tayi dama tana sane tayi mai haka.
“Dama na kammala break fast ne nace barina yimaka magana”
“Owk muje toh tunda na kammala”
Tare suka fito suka zauna ta zuba musu abincin, bayan sun kammala ta ‘kwashe kayan ta d’ebo masa mugun gunan sa, tana kawo masa yafara yatsuna face ya amsa, da d’ai d’ai yake ‘bare su yana runtse idanunsa ya a watsa wa a bakinsa kamar zaiyi amai.
Khairat dake gefe abin yabata dariya, a kuwa tayita ‘kya’kyata abarta, kallonta kawai ya tsaya yanayi dariyar tayi mata kyau gwanin sha’awa, ko ‘kifta ido bayayi, tari ta fara yi alamun ‘kwarewa,ya dauka kawai just irin tarinnan ne kawai amma sai yaga abin ya’ki tsayawa harta fara hawaye,a rud’e ya d’auki ruwan daya sha maganin ya janyo ta jikinsa ya bata ruwan kad’an tasha har lokacin tarin takeyi hannu ya sanya ya shiga bubbuga bayanta a hankali, sannu a hankali tarin yaringa lafawa har lokacin tana rungeme a jikinsa.