AURAN WATA DAYA

Kusan 20mins suna zaune a haka baiji ta motsaba kuma batayi magana ba, juyo da fuskar ta yayi ya kalla, mamaki ne ya rufeshi ganin bacci take karkad’a kai yayi a fili ya furta.
” sarakin bacci kenan, wai ita wannan bata gajiya da bacci??”
Ji yayi bazai iya tashinta ba, don haka ya jingina da kujera, ya gyara mata ‘kwanciyar a jikinsa yana binta da kallo wani mugun soyayyar ta yakeji tana ‘kara ratsa kowane sassa na jikinsa,kasa d’auke idanunsa yayi daga face d’in ta, a hankali ya fara lissafa ‘kwana kin da suka rage musu, wata fad’uwar gaba yaji ta ziyarce shi da sauri ya kara rungume ta yanajin wani irin abu a ransa ji yake kamar inya saketa shikenan sun rabu a haka har bacci ya kwashe shi. (Allah sarki har yabani tausayi????)
*****************************
Momy na zaune a falo Aisha ta fito sanye cikin wani dakakken less tasha ‘kwalliya da alama unguwa zataje.
Momy ce ta kalleta tace “wow autana kinyi ‘kyau fa”
Murmushin Aisha tayi tace “kai amma naji dad’in yabonki Momy” bata jira ta kuma magana ba tace
“Mom barina tafi kinga rana tanayi kuma karfe 3:00 zan shiga lecture”
“Oh daga can zaki wuce makaran tar??”
“Eh bakiga na d’auka jaka ba”
“Haka ne, toh Allah ya kiyaye hanya, ki gaida khairat d’in,shikuma kice masa har yau aikin bai barshi yazo ganin mu ba kenan”
“Toh Momy duk zan isar musu”
Kud’i Momy ta bata sannan ta tafi.
*****************************
Sai wajan 12:00 khairat ta farka a hankali ta bude idanunta hadi da salati….bata karasa salatin ya ma’kale a bakinta, binsa tayi da idanu har sai da ta gasgata tabbas a jikin Sadeeq ta gama sharar baccin ta,a hankali ta tuna dalilin daya sanyata bacci, murmushi tayi ta sake kallo Sadeeq wanda yaketa sharar baccin sa, a hankali ta shiga zame hannun sa daga jikinta daya zagayeta, ji tayi ya sake matse ta da sauri ta dago idanunta ta kalleshi, a hankali ya bud’e idanunsa cikin nata, da sauri tayi kasa da kanta dan wani abu ta hango cikin idanun nasa, kanta a ‘kasa tace
“Kayi hakuri Yaya na tasheka kana baccin ka”
“Uhm dama ai ke kika sani baccin”
“Ni dai babu ruwana”
“Toh wayasa ki yin bacci a jikina bayan kinsan baxan iya tashinki ba??”
Cike da shagwab’a tace ” toh ai nima kai kasanya na ‘kware har baccin ya tafi da ni”
“Toh dama……..”
Sallamar Aisha ce ta katsesu, da sauri khairat ta juyo jin muryar Aisha ai tana ganin itace da sauri ta mike daga jikinsa ta ruga ta rungume Aisha tana fad’in
“Sis koki fad’amin zakixo”
“Sorry dear nima ban tashi da shirin zuwa bane kawai na shirya na taho ne”
Tare suka: karaso falon, shiko Sadeeq saboda haushi mi’kewa yayi ya wuce sama abinsa dan Aisha ta bata masa rai yau d’aya daya d’an samu kusanci da madarar ruhinsa???? tazo ta bata masa bajat.
Su Aisha kuwa binsa sukayi da idanu, Aisha ce ta juyo tace “wannan ko haushi yaji na katse muku jin dad’in Ku?”
Kauda maganar khairat tayi “yasu Momy da dady?”
Aisha ta kula khairat katse maganar tayi don haka ita ta basar sukaci gaba da firar su.
Suna kitchen suna girki Sadeeq ya sakko,sun gaisa da Aisha ta fad’a masa sa’kon Momy, cemata yayi ta fad’a mata yau zaizo,suna gama magana ya tafi masallaci.
Sai wajan 2:30 khairat ta rako Aisha zata tafi, lokacin Sadeeq ya shigo. Tambayar ta yayi tun yanzu zata tafi?
“Eh Yaya zan wuce school ne inada lecture karfe 3:00″
Duba time yayi yaga lokacin ya kusa dan haka yace muje na kaiki”
Sallama sukayi da khairat suka shiga mota suka fice daga gidan…
*Neenat seif (Peenah pinkly)????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA D’AYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*written by neenat seif (Peenah pinkly)????????????????????????????????*
????GORGEOUS WRITERS FORUM????
????G.W.F.????
*Home of gorgeous, intelligent, and expert writers, we are the best among in the rest.*
Https://www.Facebook.com
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_
*Page 31*
Suna fita ta koma cikin gidan, har akayi la’asar Sadeeq bai dawo ba har wajan ‘karfe biyar, khairat kuwa ta cika fam,bawai saboda bai dawo bane taji haushi ba saboda ta ajje masa abincin ya barshi tun rana har zuwa yanzu, ‘kwafa tayi a xuciyar ta ta ayyana komai hucewar abincin haka zaici, dan ma yaci sa’a a kula yake.
Sai da tayi sallar magrib sannan ya shigo, lokacin tana falon tana chart, da sallama ya shigo falon, ko kallon sa batayi ba ta amsa.
Binta kawai yayi da idanu ya samu guri ya zauna, sun jima a haka batare da tace masa komai ba, sai da ya gaji sannan yace
“Ina abinci na??”
“Yana falon kasa a dining”
Kamar yace ta d’auko ta kawo masa nan amma saiya fasa ya tashi ya nufi falon can ‘kasa.
Yana kammalawa yaji ana kiran salla dan haka ya fice ya tafi masallaci.
Khairat naji ankira sallah ta tashi ta tafi d’akin ta tanayin sallah ta sanya kayan bacci, wani mugun bacci takeji saboda yau bata samu yin baccin rana sosai ba.
Shirin ‘kwanciya take ta tuna Sadeeq bai d’auki maganin sa ba, sarai tasan halinsa sai ya’ki shan maganin musamman da yaga yau jikin nashi yayi normal har yawo ya samu damar fita.
Fitowa tayi taga baya falon sama, sakkowa tayi kasan nanma bayanan, ‘kofar falon ta duba taga an rufe ta ciki, nan ta tabbatar ya dawo yana d’akin sa, komawa saman tayi kai tsaye ta nufi d’akin sa ta tura kofar had’i da sallama.
Zaune ta sameshi bakin gado yana danna laptop, tsayawa tayi tana kallon sa da alama baiji sallamar da tayi ba,sake mai maitawa.
Amsawa yayi sannan ya d’ago ya kalleta, ‘kura mata idanu yayi harta ‘karaso inda yake, har lokacin kallon ta yake, iska ta hura masa tace “ya dai Yaya sauya maka nayi ne??”
Wayan cewa yayi yay murmushi yace “nop ina mamakin yadda kika sakko cikin sau’ki ne”
Bata rai tayi tace “au na manta ma fushi nake dakai barina koma” tana fad’a ta juya.
Hannun ta ya ri’ko tsayawa tayi tana murmushi amma bata juyoba.
Mi’kewa yayi ya tako zuwa gab da ita ta yadda har sunajin numfashin juna, runtse idanun ta tayi tanajin wani irin abu yana shigarta tun daga kanta har zuwa yatsun ‘kafafunta.
Ganin ta runtse idanun ta ne yabashi damar ‘kare mata kallo tun daga fuska har zuwa jikin ta, murmushi yayi yana yaba yadda kayan bacci sukayi masifar yimata ‘kyau, wani irin shaukin soyayyar ta yakeji yana shiga kowace kafa da jini yake gudana a cikin jikin sa, ‘kurawa face d’in ta idanun sa yayi, a hankali ta soma bu’de idanunta, tas ta bud’esu cikin nashi, murmushi yayi mata, batasan lokacin da itama ta mayar masa ba.
Gaba d’aya ya manta da komai ‘kwa’kwalwar shi ta tsaya cak Khairat kawai yake gani, bai san lokacin da yasanya hannayen sa biyu ya rungume ta jikinsa ba tsam ya riketa yana shafa bayan ta.
Hawaye farin ciki Khairat taji suna bin kuncinta hannu ta sanya ta goge, wani dad’i taji ya ziyarci ruhin ta tabbas zuwa yanzu tafara gasgata maganar maryam, babu wasa tabbas Sadeeq yafara sonta,murmushin mugunta tayi lokacin data tuna wahalar da tasha akan Sadeeq da irin hawayen da tazubar ta dalilin sa.
Zamewa tayi daga jikin sa, sake ri’kota yayi,gani kamar ba’a hayyacin sa yake bane ya sanya da sauri tace ” yaya zan koma d’akina ne fah”
Sai a lokacin komai ya fara dawo masa dai dai, sakinta yayi ya koma bakin gadon ya zauna, harta juya zata tafi ta tuna da abinda ya kawota d’akinsa, dawo wa tayi ta nufi inda yake ajje maganin ta d’auko sannan ta had’o da ruwa, ajje wa tayi a ‘kasa tace “uhm dama nazo na tuna maka shan maganin ka ne”